Zan sake tsayawa takarar gwamna - Mama Taraba - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Monday, June 4, 2018

Zan sake tsayawa takarar gwamna - Mama Taraba

Ministar harkokin mata ta Najeriya, Sanata
Aisha Alhassan ta sake bayyana aniyarta ta
sake tsayawa takarar gwamnan jihar
Taraba a zabe mai gabatowa na shekarar
2019
Zan sake tsayawa takarar gwamna - Mama
Taraba
Ministar harkokin mata ta Najeriya,
Sanata Aisha Alhassan ta sake bayyana
aniyarta ta sake tsayawa takarar
gwamnan jihar Taraba a zabe mai
gabatowa na shekarar 2019.

"Kowa yasan da sanin cewa nice na lashe
zaben gwamnan jihar nan a shekarar
2015, har babbar jam'iyyar adawa ma ta
PDP ta shaida cewar nice na lashe zaben,
saboda haka zan sake tsayawa takara a
zabe mai zuwa inda har Allah yasa ina
raye.


"Na san da cewa komai iko ne na Allah,
na san Allah ne bai nufe ni da zama
gwamnan jihar nan ba.

Na lashe zaben
2015, amma Allah bai so na hau kujerar
gwamnan ba. Zan cigaba da yarda da
nufin Allah da kuma cigaba da zama tare
da mutanen jihar Taraba, kuma na san
idan har Allah yaso zan lashe zaben
2019," inji ta.

Source:- Hausa.naija.ng

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad