JINI NACE ITAH PART 1 - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Monday, June 4, 2018

JINI NACE ITAH PART 1

🌺🌺🌺
🍄🍄🍄
🌺🌺🌺
*JINI NACE ITAH*👈🏻
*🌺Na🌺*
🍄🍄🍄🍄
*ZAINAB NASEER SARKI*
🌺🌺🌺
*Zeenaseer*😘
🌺🌺🌺
*Littafi Na Daya*
*💋01*
............... "Sannu sannu insha Allah yanzu
zaki sauka lafiya Allah ya sake ki lafiya
sannu"
Wata Dattijuwa take fada,yayin da take
zaune kusa da me cikin da alama nakuda
take yi,hakan kuwa ba karamin wahala take
bah gashi har lokacin bata haihubah gashi
dare ne sosai dan Da alama kowa yayi bacci
dan ba'a jin motsin komai sai na wanan
mata me ciki da Dattijuwar dake zaune kusa
da ita.
Haka taita fama tsawan lokaci,har aka
kusan kiran sallar Asbah amma bata haihu
bah.

Mikewa dattijuwar tayi tare da kuma dauko
mata wani ,ruwa ko ince magani dake cikin
kwanan sha,kafin ta karasa garetah aka turo
kofar dakin cikin sauri,
Binshi tayi da kallo tare da fadin "Kabiru
ba'a samo likitan bah?"
"Wallahi Yaya ba'a samo bah, cewa sukayi
yayi tafiya tun shekaran jiya gashi inda aka
kwatantamin saina kai safiya ban karasa bah
tunda da nisa gababu abun hawa"
Binshi tayi da kallo tare da fadin "shekenan
mun mikama Allah lamarin mu Allah ya
sauketa lafiya dan tana jin jiki"
Shima Wanda aka kira da Kabiru wanda da
Alama shine mijin me nakudar, bin ta yayi da
kallo tana kwance sai wani irin abu take dan
tasha wahala tun 1am take nakuda gashi
yanzu 5 saura.

Ahankali ya fita daga cikin dakin tare da
zama wajan bakin kofa yana hawaye kamar
ya mashi ciwon matar tasa ya maidashi
kansa dan yana mutukar tausaya matah.
Bayan mintina da basu haura 10 bah yaji
kukan jariri.

Da sauri ya mike tare da shigewa dakin yana
bin ko ina da kallo cike da.murna hadi da
mamaki.
Jaririya ya gani rike hannun wanda aka kira
da Yaya yayi,dan ko tsabtaceta batayi bah
da alama lokacin ta fito duniyar.

Be damu da jinin dake jikin ta bah haka ya
mashe ta tare da rungumeta a kirjin sa yana
me yima Allah godiya Lokaci daya kuma ya
fashe da kuka tare da bin matar tashi dake
kwance idanuntah lumshe.

"Sannu Aisha Allah ubangiji ya biyaki da
gidan Aljanna ya baki abunda kike so duniya
da lahira ya baki lafiya ya kuma raya mana
yarinyar nan,na gode sosai nagode"
Aisha da idonta yake a lumshe itama
hawayan kebin gefan idanuntah wanda ta
rasa na menene.

"Toh kawota a gyara ta kaji ana kiran
sallah,jekayi sallah,kayima Allah godiya bara
na gyara su tare da dakin" Cewar Yaya dake
tsaye tana kallansa da murmushi a fuskar
tah.

Badan san ransa bah ya mika
yarinyar,cikinzani ta saka ta tare da mikawa
Aisha itah, " Amshi diyarki Indo Kiyi mata
addu'a taji fumin jikinki"
Hankali ta mike tare da amsar tah tana me
jin kunya kasancewar itace haihuwar fari
kuma abunka da fulani.

Binta tayi da kallo tare da kara tusata a jikin
tah.
Har Yaya ta gyara dakin Yarinyar na hannun
Uwar tah,
bayan ta gama tace "nasan Ruwan da
Kabiru ya dora Ya duhu, taso muje ayi
wanka ko kyaji kwarin jikin ki"
Ahankali ta kwanatr da yarinyar badan ranta
yana so bah,Mikewa tayi tare da cire katan
dake jikin tah, ita kuwa Yaya ta fita dan kai
ruwan ban daki.

Ahankali ta kaea matsawa wajan inda
yarinyar take kwance ta kara kallanrah tare
da sumbatar ta tana me jin tamkar ta shige
bayan da itah, Murmushi ta saki ganin yanda
idanta yake abu bude.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad