Yadda ake goge sokon da a katura bisa kuskure a WhatsApp ko da yaje - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Saturday, June 16, 2018

Yadda ake goge sokon da a katura bisa kuskure a WhatsApp ko da yaje

Assalamu Alaikum yan uwa barkan mu da war
haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin
sabo shirin namu wanda yake zuwa muka kai
tsaye daga mujallar Duniyar Fasaha, Insha
Allahu yau zamu koyi yanda ake goge sakon da
ake tura bisa kuskure koda kuwa ya isa wajen
wanda aka tura wa.

A yan kwanakin da suka shude kamfanin
WhatsApp tayi nasaran fitar da wani hanya ta
yanda zai taimaka wa mutane wanda suke
amfani da dandalin sadarwan ta wajen share
sakon da suka tura bisa kuskure koda kuwa ya
isa wurin wanda ake so a tura wa. Shi wannan
hanyar da aka masa lakani da “Delete for
everyone” ma’ana “share wa kowa” yana aikine
a kowace waya mudin mayar tayi nasaran
daukan WhatsApp.

Zaka iya goge sakon da ka
tura bisa kuskure zuwa ga wani ko kuma a
group.

A gane wanna yana aikine kadai a
dandalin sada zumuta na whatsapp.
Yanda akeyi
Misali na tura sako zuwa ga wani abokina sai
dai ma’anar bata cika ba bisa yan wasu kuskure
da na tafka yayin saurin rubutu in har hakan ta
kasance da kai abunda zakayi/kiyi shine ka/ki
danna kan rubutun ka/ki tsaya ma’ana ka/ki
latsa kan rubutun da aka tura nayan wasu daki
kai.

Zai fito ma ka/ki da wasu zabi guda shiga
wanda suke bayyana a sama wajen suna ko
lambar mutum

Dan share sakon sai a latsa wannan mabullin
wanda yayi kama da akwatin zib da
shara”Delete button” wanda shine na hudu a
jiren ababen da suka bayyana.

Wasu lokutan
baya bayyana a wajen yakan canza mazauni in
har ba ka/ki gansa inda na ambata ba sai a
latsa wannan ma bullin na karshe wanda a jiki
dot guda uku za’a ga an rubuta “Delete” sai a
latsa kai.

Za’a ga an rubuta “Delete for me” ma’ana “goge
wa kaina” amfanin wannan mabullin shine in
harka ka/ki dannan kai sakon da ka tura ko aka
turo ma zai bace ma kai kadaine amma
mutumin da ya turo ko ka/ki tura masa zaigani
sai dai in har shima ya danna, sai na biyun
waton “Cancel” shi wannan mabullin amfanin sa
shine soke abunda ka zaba in dai ka latsa
wannan zai mayar da kai izuwa shafin baya ba
tare da yin wani aiki ba.

Sai na karshen wanda
shine manufar wannan darasin wato “Delete for
everone” shi wannan mabullin in har ka latsa sa
toh abunda ka tura zai bace ma’ana kai da ka
tura da wanda ka turawa gaba dayan ku bazaku
ga idaninsa ba ya tafi Kenan.
Dan takaiceciyar hanaya Kenan da za’a bi wajen
goge sakon da aka tura bisa kuskure a
whatsapp in ka/ki na da Karin bayani ko naiman
taimako zaka/ki iya rubutawa a akwatin da ke
kasa.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad