2019: Sule Lamido ya jaddada cewar Buhari ya gaza ba zai iya mulkin ba, a wata ziyara da ya kaiwa Wadata - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Saturday, June 30, 2018

2019: Sule Lamido ya jaddada cewar Buhari ya gaza ba zai iya mulkin ba, a wata ziyara da ya kaiwa Wadata

- A yayin jawabinsa lokacin ziyarar ne
tsohon gwamnan yayi jirwaye mai kama da
wanka ga shugaban kasa Muhammadu
Buhari
Bayan Kwanaki 2 da ziyarar da tsohon
mataimakin shugaban kasa kuma mai
neman Jamiyyar PDP ta tsayar da shi
takarar shugabancin kasar nan wato
Alh. Atiku Abubakar.

Sai ga shi tsohon gwamnan Jihar Jigawa
wanda shi ma ya ke zawarcin kujerar
shugabancin kasar a dai tutar Jamiyyar
ta PDP ya kaiwa masu ruwa da tsaki
akan shugabancin Jamiyyar, inda ya
bayyana musu sha'awarsa ta neman
tsayawa takarar shugabancin kasar nan
a tutar Jamiyyar a zaben 2019.

2019: Sule Lamido ya jaddada cewar Buhari ya
gaza ba zai iya mulkin ba, a wata ziyara da ya
kaiwa Wadata
Sule Lamido wanda ya bayyana tare da
rakiyar Tsohuwar ministar harkokin
kasashen waje, Josephine Anenih da
wasu manyan ‘yan Jamiyyar PDP da
wasu masu take masa baya.

A jawabinsa yayin ziyarar Sule Lamido
ya bayyanawa shugabancin Jamiyyar
cewa shi jigo ne a siyasar kasar nan
wanda zai iya kai kasar nan tudun Mun
tsira, matukar ya kai ga nasarar zama
shugaban kasa.

Sannan kuma ya bukaci shugabancin
Jamiyyar da ya yi duk mai yiwuwa
wajen hada kai don ganin sun kai
dukkanin wani dantakarar jamiyyar
APC zata tsayar kasa a zaben 2019 da
ya ke tafe.

Da yake bayyana irin salon gwamanatin
shugaban kasa Muhammadu Buhari
kuwa, kira yayi ga ‘yan kasar nan da su
sani cewa dama tun asali shugaban kasa
Buhari yana da tarihi yin mulki cikin
rikice rikice, wanda wannan ne ya sa
yanzu ma rikici ke cigaba da faruwa a
sassan kasar nan.

Sannan ya shaida cewar babban
Burinsa shi ne dawowa da kasar nan
martabarta domin ‘yan kasar nan su
amfana da arzikin da Allah yayi mata.

Kana yayi kira ga dukkan wani mai
fatan ganin hakan da ya taho su hada
karfi waje guda domin kaiwa ga gaci.
A nasa bangaren kuwa shugaban
Jamiyyar PDP na kasa Prince Uche
Secondus, bayyana Sule Lamidon yayi a
matsayin jajirtaccen dan kishin kasa
wanda ya dauki halin 'yan mazan jiya
irinsu Sir Ahmadu Bello,

Chief Obafemi
Awolowo da Dr. Nnamdi Azikiwe.
Latsa wannan domin samun sabuwar
manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a
wayar ku ta hannu:

Daga. Hausa.naij.ng

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad