Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh ya yi gargadi - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Tuesday, June 19, 2018

Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh ya yi gargadi


Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya
bayyana gwamnatin tarayya ta bayar da
wani gargadi da jan kunne mai ban tsaro
dangane da amfani da shinkafa 'yar
Thailand inda ta ce ba bu abin da ta kunsa
face guba mai haifar da cutar daji.

Ministan noma da raya karkara na
Najeriya, Cif Audu Ogbeh, shine ya
bayar da wannan gargadin a ranar
Litinin din da ta gabata yayin ganawa
da wasu matasa a babban birnin kasar
nan inda ya bayyana cewa, mafi
akasarin mutane sun kulla soyayya da
shinkafa 'yar Thailand sakamakon
shaharar ta sai dai tabbas tana kunshe
da sunadarin guba.

Yake cewa, akwai sunadarin Arsenic da
yake yaduwa a cikin gonakin da aka
shafe shekaru da shekaru a na gudanar
da noman shinkafa wanda a sanadiyar
hakan ne yake kara habaka kuma shi
sunadarin Arsenic yana haifar da cutar
Daji watau Kansa.

NAIJ.com ta fahimci cewa, irin su jihar
Delta da wasu kasashe dake yankin
Kudu maso Gabashin nahiyyar Asia
akan samu ire-iren wannan habaka ta
sunadarin Arsenic a gonakin su
sakamakon yawaitar noman shinkafa
da ba bu kakkautawa.

Akwai Guba cikin Shikafa 'yar Thailand - Ogbeh
ya yi gargadi
Ya ci gaba da cewa, a kwana-kwanan
nan za a rufe iyakokin kasar nan na
dindindin domin dakile fasakaurin
shinkafa daga kasashen ketare da
sauran ababe masu dauke da sunadarin
guba zuwa cikin Najeriya.

Ministan ya kara da cewa, daya daga
cikin ababe masu rusa tattalin arzikin
Najeriya shine shigo da shinkafa daga
kasashen ketare wanda cikin 'yan
kwanaki kadan za a dakatar da hakan
domin kare lafiyar al'umma da kuma
tattali arzikin kasa.

Ogbeh ya kuma bayyana damuwar sa
dangane da yadda alakar dake tsakanin
Najeriya da wasu makotan kasashe na
nahiyyar Afirka ke janyo nakasun
tattalin arzikin kasa da ya sanya aka
yanke shawarar rufe iyakokin ta.
NAIJ.com ta fahimci cewa, cikin shekaru
biyu da suka gabata gwamnatin tarayya
ta sama babbar nasara wajen raguwar
shigo da shinkaffa da kaso 95 cikin 100
tare da ƙara adadin manoman shinkafa.

Ya kara da cewa, akwai jihohin da suka
yi hobbasa wajen noman shinkafa da
suka hadar da Anambra, Ebonyi, Kebbi,
Kano da kuma Jigawa.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad