Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Thursday, June 21, 2018

Ko kun san adadin Yara da aka ketawa haddi a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu


Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya
bayyana mun samu rahoton cewa, akwai
kimanin adadin yara 500 da aka ketawa
haddi a sansanan gudun hijira cikin
watanni hudu da suka shude.

Jakadiyar Najeriya a Majalisar Dinkin
Duniya, Ms Comfort Lamptey, ita ta
bayyana hakan a ranar Alhamis din da
ta gabata da cewar akwai yara 500 da
aka ci zarafin su cikin sansanan gudun
hijira dake fadin kasar nan tsakanin
watan Janairu da Afrilu.

Take cewa ana keta haddin yaran ne
cikin kowace rana a sansanan na 'yan
gudun hijira.

Lamptey tayi wannan karin haske ne
yayin bikin tunawa da ranar Yaran
Afirka da hukumar kare hakkin dan
Adam ta Najeriya ta gudanar a babban
birnin kasar nan na Abuja.

Jakadiyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ms
Comfort Lamptey
NAIJ.com ta fahimci cewa, hukumar ta
NHRC (National Human Rights
Commission) ta gudanar da wannan
bikin taro mai taken "kada a bar
kowane yaro a baya domin ci gaban
nahiyyar Afirka"
Jakadiyar ta Najeriya ta bayyana
bukatar gwamnatin ta kara kaimi wajen
tabbatar da bayar da kariya ga hakkin
yara a kasar nan.

Take cewa, akwai tsare-tsare da dama
da za a bujoro da su domin wayar da
kai da kuma kira ga al'umma dangane
da kare hakkin yara da kuma rage
auren wuri da ake yiwa yara a kasar
nan.

A nasa bangaren, Babban Sakataren
hukumar NHRC, Tony Ojukwu, ya nemi
shugaban kasa Muhammadu Buhari
akan ya gaggauta rattaba hannu kan
sabuwar doka ta kare hakkin yara a
kasar nan.


Ya ce, wa'adin shugaban kasa ya zama
wajibi ne don kare hakkin yara da
nakasa, yara da aka yi hijira da
waɗanda aka yi wa masu cin zarafin
yau da kullum.
Yake cewa akwai bukatar amincewar
shugaban kasa akan wannan doka
domin bayar da kariya ga hakkin yara
da ake ciwa zarafi da keta ma su haddi
a kowace rana.

Ya kuma roki gwamnatin jihohi akan su
karbi wannan doka hannu biyu-biyu
domin dabbaka ta cikin dokoki na
jihohin su.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad