SIRRIN DAKE TATTARE DA CIN DANYEN TUMATIR GA MAI AZUMI - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Sunday, June 3, 2018

SIRRIN DAKE TATTARE DA CIN DANYEN TUMATIR GA MAI AZUMI

Wani dalibi a jami’ar Maiduguri mai suna
Jesse Tafida ya binciko wadansu hanyoyi da
za a iya amfani da danyen tumatir wajen
karfafa garkuwar jika da samar wa jiki lafiyar
da take bukata, da kuma amfanin da ke
gareshi a jikin dan Adam musamman yanzu
da musulmai ke azumin watan Ramadan.
Ya ce ya gano hakan ne bayan binciken da
ya gudanar akan sinadarorin da dayen
tumatir ke dauke da su da mutane da yawa
basu sani ba.
Tafida ya gano cewa tumatir na dauke da
sunadarin da ake kira ‘Antioxidants’ a
turance da ke kare mutum daga kamuwa
daga wasu cututtuka sannan kuma ana
samun sinadarin Vitamins A da B da kuma
Folic Acid a cikinsa.
Dalibin yace cin dayen tumatir na kare
mutum daga kamuwa da cutar daji, hawan
jini da kuma bugawar zuciya.
Ya ce wasu binciken sun nuna cewa idan
ana gauraya danyen tumatir a cikin abinci
musamman cikin wasu gaiyayyakin da ake ci
kamar zogale, rama da makamatansu yana
rage cutar siga.
Ya kuma ce za a iya cin dayen tumatir idan
cikin mutum ya murde ko kuma idan cikin
mutum na ciwo sannan yana kuma rage kiba
a jiki musamman ga wadanda suke bukatar
haka.
Tafida ya ce cin dayen tumatir na kara
karfin ido da kuma ya kare idon daga
kamuwa daga wasu cututtuka kamar yanar
ido, amosanin ido da makamatan su.
Daga karshe ya shawarci matan da suke
dauke da juna biyu da su yawaita cin dayen
tumatir lokacin da suke da ciki da kuma
bayan sun haihu domin yana taimakawa
wajen kare jariri daga kamuwa da cututtuka
da kuma taimaka masa

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad