Idan Ba'a Kiyaye Ba
Kannywood Zata Iya Shiga
Tsaka Mai Wuya -
Zaharadden Sani
A hira da PREMIUM TIMES ta yi da fitaccen
dan wasan fina-finan Hausa kuma Furodusa
a farfajiyar Kannywood, Zaharadden Sani, ya
bayyana mana yadda farfajiyar ke a sannu-
sannu neman ta fada halin kaka ni kayi
saboda masifar ‘yan fashi teku’ wato ‘Piracy
Zaharadden ya koka kan yadda waddan
dabi’a na ‘yan fashin teku ke neman ya
dukusar da farfajiyar fina-finan Hausa.
Ina so in gaya maka cewa tabbas idan fa
ba’a yi wani abu akai ba toh ko Allah ya
kiyaye zamu fada cikin tsaka mai wuya.
Yanzu abin ya baci sai kaje kasuwa kaga
babu sabbin fina-finai.
Ko kuwa kaga an
dade da fidda fim a Sinima amma shiru ba
ka gan shi a CD ba.
Toh babban dalilin kuwa
shine maganan wadannan muggan Mutane.
Basu da mutunci ko kadan.
Da zarar an saki
fim sai su je su buga shi iya yadda suke so
su fara sai da shi naira 50 zuwa naira 100 a
fim din da Furodusa ya kashe miliyoyin
naira.
Wani abin takaici ma shine har ta waya ana
tura fim kan naira 20 naira 50.
Saboda Allah
da me wannan yayi kama?
Sai kaga yanzu Ka kashe makudan kudi
wajen shirya fim amma uwar kudin ma ta
fito babu ballantana a ce wai har an samu
riba.
Yanzu haka kawai ba za ka fidda kudi ka
kashe wa fim ba bayan kasan baza ka sami
riba ba.
Biyan jarumai ma ya zama sai a a
hankali, Ko sai kayi kaffa- kaffa tukuna in ba
haka ba kuwa ka kira wa kan ka ruwa. Kana
gani kiri-kiri wani na kwankwadan romon
wahalar ka saboda bala’in irin wadannan
mutane.
Zaharadden ya kara da cewa ita kanta
Sinima da suke nuna fim din abin dai sai a
ahankali, domin ba kowa bane zai iya fidda
kamar naira 1000 zuwa sama ya shiga kallon
fim daya.
Kaga shi Sinima yana da kyau sai dai masu
kallon fina-finan mu da yawa ba za su iya
biyan irin wannan kudi ba na shiga kallo abin
sai kaga dakyar ko tanan ma ake fita.
Abu daya da zai taimaka wa wannan
farfajiya sannan ya ceto mu daga
gangarawar da muke yi, shine fa a samu a
giggina gidajen kallo masu saukin kudi da
mai sai da ruwa, dan achaba, mai keke
Napep zai iya shiga ya kalla da dan naira
100n sa. Kaga hakan zai taimaka wajen
samun isar da fina-finan mu duk inda muka
so ya isa kuma ba za a fadi ba.
Amma tabbas idan ba haka muka yi ba toh
fa kaico abin sai du’ai fa. Ba za ka iya sakin
fim a CD ba kai kuma ga dukiyar a make a
cikin fim din.
A karshe Zaharadden ya bayyana cewa mafi
yawan su sun fara karkata zuwa yi wa
tashoshin nuna finafinan ta satalat,inda
sukan siya fim din idan yana kyau sannan ya
cika sharuddan su su nuna a gidajen talabijin
din su.
Abin fa ya kai ga haka.
Dole ne fa sai gwamnati da masu hali sun sa
mana hannu wajen giggina irin kananan
wuraren kallon fina-finan a fadin kasar nan
idan dai ana so a sai nasara wadannan
miyagun mutane da sannan muma mu sami
riba a kan sana’ar mu.
No comments:
Post a Comment