A yau, Laraba, ne shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin
tawagar jiga-jigan jagororin darikar
Tijjaniya a fadar gwamnatin tarayya dake
Abuja.
A jawabin sa ga tawagar Tijjanawan
karkashin shugaban tan a duniya,
Sheikh Ahmed Tijjani Ibrahim Inyass,
shugaba Buhari ya shaida masu cewar
burin sa shine kawo cigaba ga kowanne
yanki na Najeriya ba tare da la’akari da
addini, kabila ko yanki ba.
Kazalika ya mika godiyar sa tare da
nuna jin dadi bisa yadda Shehunnan
darikar ke yi masa tare da Najeriya
addu’o’i.
Shugaba Buhari da Sheikh Inyass
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban
darikar Tijjaniya na duniya, Sheikh Inyass
A jawabin sa, Sheikh Inyass, ya
shaidawa shugaba Buhari cewar sun zo
Najeriya ne daga kasar Senegal domin
yin ta’aziyya ga iyalan shugaban
Tijjaniya na Najeriya, Khalifa Sheikh
Isyaka Rabi’u, da allah ya yiwa rasuwa
kwanakin baya.
Kazalika ya shaidawa shugaba Buhari
cewar, fiye da mutum miliyan 40
magoya bayan darikar Tijjaniya na
yiwa shugaba Buhari addu’ar samun
nasara a kokarin san a dora Najeriya a
kan turbar cigaba mai dorewa.
Kafin su bar fadar shugaban kasar,
Sheikh Inyass ya yiwa Najeriya addu’ar
samun zaman lafiya, cigaba da wadatar
lafiya ga dukkan ‘yan kasa bakidaya.
Shugaba Buhari da tawagar shugaban darikar
Tijjaniya
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban
darikar Tijjaniya na duniya.
Source:- Hausa.naija.ng
No comments:
Post a Comment