ALHERI DANKONE ( 1 )
NA UMMI A'ISHA
ALHERI DANKO NE
PART 1
1⃣
Na UMMI A'ISHA
JAN KUNNE- duk wanda ya canza min
wannan labarin ko ya canja sunan taurarin ciki,
ko yayi min editing ALLAH YA ISA BAN YAFE
BA.
Tafe yake yana cire safar hannun dake
hannunsa yana cillar da ita akan tile din dake
malale aharabar runfar asibitin, leburorin
wurinne suke biyeda shi suna tsince duk abinda
ya yar awurin shikuwa sai faman yatsina fuska
yake yi sai kace yaune ranar farko wadda yafara
karbar haihuwa kokuma yafara
operation,ahankali yake tafiya sai kace marar
jini ajiki yana sanye da light blue colour din t
shirt mai dogon hannu da black din jeans idonsa
sanye cikin farin gilashi amma da alama gilashin
nasa na gayune bana kara karfin ido bane, duk
inda ya ratsa babu abinda kakeji sai weldon sir!
Shi kuwa gogan baya magana sai daga hannu
domin magana tana mutukar bashi wahala
saboda yangarsa da jan ajinsa gashi da iyayi
kamar mace amma hakan yana mutukar kara
masa kyau kuma da alama iyayi nature dinshine,
ayanda na hango fuskarsa zan iya kiyasta
shekarunsa bazasu haura 27 ba aduniya,fari ne
dogo siriri lange lange kana ganinsa zaka gane
baya aikin wahala kuma hutu ya zauna ajikinsa,
cikeda yanga ya karasa office dinsa wanda yake
jere a rukunin ofisoshin manya likitoci
( consultants) wani office yabude yashiga
wanda asaman kofar aka manna wani dan
katako aka rubuta DR TAFIDA ajiki da manyan
harrufa, ahankali yashiga cikin office din wanda
yayi tsananin tsaruwa kamar ofishin shugaban
kasa, kan wata doguwar kujera baka yaje
yakwanta yamike yatasa kansa da hannun
kujerar yafara cire (neck tied) din wuyan rigarsa
yacire gilashin fuskar sa yalumshe manyan
idanuwansa wanda suke zagaye da bakaken
gashi masu mutukar baki sai da yadan huta
sannan ya mike a hankali tamkar mace ya isa
kan teburinsa yadanna wata kararrawa aguje
wasu fadawa guda uku sanye cikin jajayen kaya
suka shigo, suna shigowa suka fara zabga kirari,
Allah ya taimaki mai girma tafida, dan sarki
jikan sarki kuma sarkin gobe da yardar Allah,
Allah yakara maka nisan kwana!
[6:56PM, 11/11/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣
Na UMMI A'ISHA
Hannu yadaga musu take sukayi shiru saboda
sun gane nufinsa kuma dama can shi baya son
yawan magana duk maganarshi atakaice yake
yinta itama sai takama mutuka amma in
bakamawa tayi ba sai dai yayi umarni da
hannunsa, kallonsu yayi yanuna musu kan table
dinsa tuni suka zabura suka fara harhada
takardun dake kan table dinsa gamida dibar
wasu files manya, laptop dinsa da brief case
dinsa suna gama harhadawa sukayi waje
yayinda shi kuma dr tafida ya sake mikewa a
kujerar da yake kai sai da ya shafe sama da
minti 20 ahaka sannan yatashi yahau kan
kujerarsa ta aiki yajawo drawer dinsa yaciro
tabar wiwi (ganye) yadauki ashana ya kyasta
yafara busa hayaki, wani dan madaidaicin glass
cup ya ajiye musamman akan table dinsa inda
yake tara tokar tabar da yakesha kuma da
alama yana sha akai akai domin har kofin
yakusa cika da tokar tabar, zukar tabar wiwin
yaci gaba dayi har ta kare sannan ya kishingida
ajikin kujerarsa nanma yashafe fiyeda minti
goma sannan yatashi ya dauki phones dinshi da
gilashinsa yafita daga office din yana fita
fadawansa suka zabura suka nufi motarsa
dasauri suka bude masa gidan baya yashiga
yazauna suka rufe kofar motar suka runtuma
tasu yayinda daya daga cikinsu yashiga
mazaunin direba ya zauna yatashi motar ya
harba suka bar harabar cikin asibitin.
[7:33PM, 11/11/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
3⃣
Na UMMI A'ISHA
Fita sukayi daga harabar asibitin mutane
sai kallon motocin nasu sukeyi gamida daga
musu hannu amma dan mulkin yana daga
kishingide acikin kujerar baya hannunsa rikeda
jaridar daily trust yana karantawa da haka har
suka isa kofar fada inda anan gidansu dr tafida
yake, wani makeken gida nagani gaba dashi
kuma filine babba tuni digarawan dake zaune
abakin kofar gidan suka mimmike tsaye saboda
ganin motar tafida,kan motocin suka kutsa cikin
babban gidan wanda yasha zane iri iri da adon
kala kala irin na sarakai nidai ummi Aisha tun
daga nan nagane cewar gidan sarki nashigo
domin gaba daya tsarin gidan namasu sarauta
ne, cikeda iyayi da takama hadida kasaita dr
tafida yafito daga cikin motar yatasamma cikin
gidan wanda akalla sai da aka wuce zauruka
sunfi 5 sannan yakarasa wani babban fili mai
dauke da part part akalla zasu kai guda 5 kansa
tsaye yawuce wani sashe mai mutukar kyau
wanda yasha ado da kwalliya, budewa kofar
falon yayi yashiga nan nahango wani dattijon
mutum wanda akalla shekarunsa zasu kai 65
yana kishingide akan kilisan dake malale acikin
falon wanda yawansu zai iya kaiwa guda biyar
kala kala gashi jikin bangon dakin yasha zane na
sarauta, gefensa tumtum ne wanda yajingina
ajiki ga kayan marmari nan agefe dangin itatuwa
kamar su inibi, tufa, ayaba, kankana, gwanda,
zaitun, ruman, da sauran kayan itatuwa cike
cikin wani dan madaidaicin kwando wanda aka
tanada musamman dan adana kayan marmari,
cikeda alamun gajiya yayi sallama ahankali
yashiga wannan al'adarsa ce duk lokacin daya
dawo daga office sai yaje ya gaida mahaifinsa
da mahaifiyarsa,washe fuska dattijon yayi ya
amsa sallamar da Wa'alaikas salam wa
rahmatullahi wabrakatu, barka da zuwa ibrahim
cikin jin dadi yakarasa inda mahaifin nasa yake
yazube akasa yafara kwasar gaisuwa,barka da
hutawa mai martaba dafatan mun sameku lfy,
ya akaji da jama'a? Cikin jin dadi yace
alhamdulillah ibrahim dafatan ka dawo lfy? Lfy
lau yafada yana murmushi gamida mikewa yana
fadin nabarka lfy ranka yadade, Allah yakara
nisan kwana, Allah yaja zamani.
4⃣
Yana fitowa ya gangara izuwa wani sashen
nagaba wanda tun daga nesa nafara hango bayi
da kuyangu sai faman kaiwa da komowa suke,
wasu suna aikace aikacen gida wasu kuma suna
ta faman shige da fice tunda tafida yadoso su
suka fara zubewa suna dibar gaisuwa barka da
dawowa mai girma tafida, takawa lfy dan sarki
jikan sarki, tafiya sannu sannu kwana nesa
sarkin gobe, hannunsa kawai yake cira musu
amma ko kala yakasa furtawa sai dai da alama
sun san halin tafidan domin hakan bai hanasu
cigaba da gaishe shi ba, ko kallo basu isheshi
ba balle ya amsa gaisuwarsu wannan dalilin ne
yasa mutane da dama suke kiransa da mai
girman kai wasu kuma suce yanada iyayi da
wulakanci to koma dai menene da alama iyayin
nature dinsa ne
[8:36PM, 11/11/2015] Ummi A'isha: Tamkar
wani mai ciwon kafa yaci gaba da tafiya har ya
cimma sashen mahaifiyarsa hajiya Kilishi
wadda yake tangamemen gaske yana shiga
kasaitaccen falon nata wanda yasha adon kayan
alatu yafara cin karo da bayinta wasu sunata
aikin gyaran falon wasu sunata wawwatsa wani
abu mai mutukar kamshi kamar turaren wuta
suna ganinsa suka durkusa barka da shigowa
mai girma tafida! Kai kawai ya gyada yawuce
cikin dakin inno kamar yadda yake kiran
mahaifiyar tashi, akan wata katuwar darduma ya
hangota tana zaune ta jingina bayanta da
babban filo kafafuwanta kuma ta dorasu kan
tumtum wata baiwa sai aikin mammatsa mata
kafafun take, da sallamarsa yashiga yana shiga
wannan baiwar ta zabura barka da zuwa
yallabai, bai bata amsaba tatashi tafice, agefen
gadon mahaifiyar tashi ya zauna wani irin
gadone nakarfe mai runfa fentinsa kalar ruwan
hoda yasha lallausar katifa da shinfidu na
alfarma ga kamshi mai dadi dayake tashi daga
cikin dakin, barka da hutawa inno yafada yana
wani lallausan murmushi, yawwa barka da zuwa
tafida tafada tana murmushin itama, kallo daya
zakayi mata kagane cewa mahaifiyarshi ce
domin babu ta inda ya barta akama, kamarsu
daya dashi kuma da alama tana jidashi sosai,
macece mai fara'ar gaske kuma bata tsufa ba
dan shekarunta bazasu wuce 45 amma bazaka
taba gane hakan ba saboda jikinta bai nuna ba
ko kusa, cikeda kulawa tace zakaci abinci ne
yanzu? Kai ya girgiza tamkar wani karamin yaro
yace a'a inno sai anjima yanzu bacci nakeji, to
atashi lfy tafada tana murmushi,murmushi
yakuma yi yakwanta akan gadon mahaifiyar
tashi yaja filo yatasa kansa dandanan bacci yayi
gaba dashi, tashi inno tayi takoma falo tazauna
gudun kada azo adameshi yana bacci.
5⃣
Karfe 3:40 yatashi daga baccin da yakeyi
yafito idonsa duk yayi kalar masu bacci afalo ya
taradda inno tana salla dan haka bai tsayaba
yawuceta yafita daga lungunta yanufi nashi yana
shiga yafada toilet ya hada ruwan zafi yayi
wanka yafito yasaka farar t. Shirt mai gajeren
hannu yasa wando jeans baki yafesa turaren
FOGG yafito yanufi masallaci lokacin dayaje har
anshiga salla, yana idarwa ya fito ya wuce ma
'ajiyar dawakai yasamu an shirya masa dokinsa
anyi masa shimfida an gyarashi domin fita kilisa
bai bata lokaci ba yahau suma fadawansa
wanda suka hada da sarkin fada, sarkin mota, da
maja sirdi suka hahhau nasu suka fito daga
gidan ahankali suke tafiya tacikin garin har suka
fita suka shiga dokar daji, dama idan da sabo
sun saba dan kusan kullum sai tafida yafita
kilisa, kilisa tana daya daga cikin abubuwan da
suke burgeshi a harkar sarauta, tafiya kawai
suke suna shakar iskar dake ratsa dajin sannan
suka billa tawata hanyar domin komawa gida
alokacin mangariba takusa yi har ta kawo jiki,
suna zuwa gida ana kiran salla, akasalance
tafida yasauka daga kan kosasshen dokinsa yayi
alwala yashiga masallaci ana idar da salla yafito
adaidai lokacin wata hadaddiyar mota tashigo
baka kirar croutoure mai tsananin kyau ajiki an
rubuta TAFIDA 1 kallon motar yayi yai tsaki
yawuce gaba, agabansa aka yi packing din
motar aka fito wani saurayine wanda zai kaishi
atsaye kuma ashekaruma bazai fishiba yafito
daga cikin motar yana dariya Allah yaja zamanin
tafida, batare da tafidan yayi masa magana ba
yawuce yafara tafiya shikuma yabishi abaya har
suka karasa sashen tafidan suka shiga, afalo
suka zauna cikin muryar iyayi tafida yace wai
kai faisal meyasa bakada mutunci ne? Motar
tawa kadauka katafi yawon iskanci? Dariya yayi
wanda aka kira da suna faisal yace haba
abokina kaima iskancin nan kana dan tafabawa,
fuska tafida ya yamutsa, ni bana wani iskanci
kaine dan iska, ok naji ni dan iskane saboda ina
neman mata kai kuma dan ganye? Filon kusa
dashi tafida yadauka yajefeshi kai dan iska ne
idan ni dan ganye ne ai dasauki tunda har yanzu
ni saurayine cikakken saurayi kuma, dariya
abokin nasa yayi dakyau virgin boy, amma dai
abi ahankali banda ganganci,shiru tafida yayi bai
kara magana ba domin shi baya doguwar
magana idan kajishi yayi magana mai tsawo to
da mahaifinsa ne ko mahaifiyarshi ko kuma
abokinsa faisal.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [7:23PM,
11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE !
6⃣
Na UMMI A'ISHA
Tashi tafida yayi ya shiga daki yahaye gado
yakwanta minti kadan faisal yabiyoshi cikin
dakin abokina ya zaka kwanta bayan ba
mugama magana ba? Kai malam bana son
surutu, eh nasani ai shiyasa nake son na sanar
dakai cewa na dauki wadannan kudin naka nayi
sadaka dasu, tsaki tafida yayi mtwww to ina
fata ba iskanci kaje kayi da kudina ba?
Murmushi faisal yasake yi wai kai finka laifi
nayi? Kaima fa mai laifi ne, kana shan ganye
over ni kuma ina neman mata jifa jifa ba koda
yaushe ba, murmushi tafida yayi yatashi zaune,
to ai ni matan ne ma tsoronsu nake, gaba daya
ban san ta inda zanbi ba yanzu haka idan ka
ajiye min mace wlh ban san yadda zanyi da
itaba, wata irin dariya faisal yayi hahahaha!
Ammafa kacika dan rainin wayo, ta ina kake
karbar haihuwa? Kaida ka karanci mata kasan
yadda suke, karfa ka manta kai likitan matane
su kake gani kake dubawa akoda yaushe, dan
malalacin murmushi tafida yasaki to sai aka
fada maka kuma nasan hanyar? Karya kake
kasani mana, dariya tafida yayi kai dan iska ne,
wlh duk ranar da mai martaba yasan kana
neman mata sai ya tube rawanin da ya daura
maka,cikin dariya shima faisal din yace kamar
yadda kaima mai martaba zai tube rawanin daya
daura maka ba duk ranar da yagane kai mugun
dan ganye ne, murmushi tafida yayi ra'ayina
shine nasamu cikakkiyar budurwa kamar yadda
nake cikakken saurayi, taba baki faisal yayi eh
munji kai saurayine amma ai dan ganyene,
dariya tafida yayi duk da haka dai nafika,ni
yanzu ma ka kyaleni wlh yunwa nakeji sai da
inno tace naci abinci dazu nace bacci zanyi
amma bari nayi mata waya akawo mana,
wayarshi ya dauka kirar yota phone yakira inno
yace akawo masa abinci shida faisal ba awani
jimaba sai ga kuyangi guda 2 sun shigo
hannuwansu dauke da tirarrika na silba manya
manya anan suka ajiye suka fita, suna fita faisal
ya fara bubbude kwanukan abincin, abinci ne
kala kala na gargajiya saukowa tafida yayi suna
ci suna hira har suka gama, suna gamawa suka
tafi masallaci sukayi salla suka shigo gida afalo
faisal yazauna yafara waya da yanmatansa shi
kuma tafida yawuce daki yafada kan gado
yajanyo tabar wiwi yafara zuka.
7⃣
Washe gari dasafe dr tafida yashirya tsaf
cikin shirinsa nafita office bakin wando yasa da
bakar t.shirt mai dogon hannu yadora jar jacket
asama yasa bakin takalmi cover shoe
[7:38PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: Yafesa
turaren fogg yafito lokacin faisal yanata bacci
kasancewar shi a ministry for local government
yake aiki baya fita dawuri shikuwa tafida 7:30
yasaba fita office, yana fitowa sarkin fada da
sarkin mota sukazo suka zube suka fara zabga
kirari barka da fitowa mazajen fama hadiri sa
gabanka inda kakeso, murucin kan dutsi baka
fitoba sai da ka shirya, atafe dakyau, atsaye
dakyau amma azaune kafi dadin kallo dan
ahmadu jikan sani gyara kintsi giwa kinfi karfin
waiwaye, kura ko kin mutu kinfi karfin kare, wani
kaya sai amale wane jaki, cikeda takama yace
barkanku da safiya yawuce cikin gida yanufi
dakin inno mahaifiyarshi alokacin har ta harhada
masa kayan karyawarshi tsaf ta zuba acikin
akushi mai kyau tana jiran shigowarsa, yana
shiga yazube agabanta tana kushingide
hannunta rikeda carbi tana ja sukuma bayinta
har sun fara aikace aikacen da suka saba yi,
barka da asuba inno yafada idonsa akasa, barka
da tashi tafida, kafito lfy? Lfy lau inno, to Allah
yabada sa'a, Allah ya tsareka, Allah yadawo
dakai lfy, amin inno nabarki lfy, tashi yayi yafita
yanufi sashen mai martaba lokacin shima yana
zaune afalonsa yana karatun alqur'ani mai
girma, cikin girmamawa tafida yadurkusa barka
da asuba ranka yadade, cikin murmushi yace
yawwa ibrahim har anfito? To Allah yatsare
Allah yabada sa'a, amin mai martaba yafada
yatashi yafita inda aka adana motarsa yanufa
aka bude masa gidan baya yashiga yazauna
cikeda nuna isa yake daddana wayar hannunsa
fadawa sai kawo gaisuwa suke yi amma yakasa
amsawa,asibitin Rasheed shekoni specialist
hospital suka dosa inda tafida yake aiki.
[7:48PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
8⃣
Na UMMI A'ISHA
Suna zuwa kamar kullum yafito yashiga office
dinsa wanda yake jere ajerin gwanon ofisoshin
kwararru na asibitin, yana zama wata nurse
tashigo tana sanye da fararen kaya,morning sir!
Morning ya amsa mata idonsa yana kan laptop
dinshi yana daddannawa, sir akwai patient
wanda jiya kayiwa operation tofa har yanzu bata
farfado ba, cikeda damuwa ya tashi domin shi
yana tausayin mata duk lokacin dayaga mace
acikin halin rashin lafiya sai yaji kamar zaiyi
kuka, maternity yanufa wannan nurse din tana
biye dashi abaya ita dai wannan likitan yana
burgeta domin yasan aikinsa matsalarsa kawai
yanada girman kai ga nuna isa kamar shine
sarkin ko dan sarauta ne? Yahadu sosai ga kudi
da sarauta ga ilmi ga uwa uba kyau, yana shiga
maternity yafara bin patient din daya bayan daya
yana dubasu har yagama yakoma office dinsa
alokacin yafara ganin marassa lfy wadanda suka
zo ganin likita kuma gaba dayansu matane
domin shi mata kawai yake dubawa baya duba
maza sai wurin 11 yagama ganin marassa lfy
yayi breakfast yatashi yashiga round.
[8:16PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
9⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana dawowa daga round yanemi wuri a office
dinsa yazauna lokaci lokaci fadawansa suna
lekowa domin ganin lafiyarsa, sai misalin karfe 5
yatashi lokacin yafito daga theatre cikin gari
suka shiga akan hanyarsu ta tafiyane suka ratsa
tawani dan kauye anan yaga wata makekiyar
gona wadda akalla zata kai kilo mita 5 anyi
shukar shinkafa aciki, shukar tayi kyau sosai
sarkin mota ya yiwa magana cewa ya tsaya
cikin sauri ya taka birki yaja ya tsaya yabude
kofa yafito suma fadawan firfitowa sukayi suka
tsattsaya, gonar ya zubawa ido ta kayatar dashi
hakika wannan zatayi daidai da wurin da yake
nema domin gina business suit dinshi hadida
gidan shakatawarsa motar ya koma yashiga ya
zauna, fadawansa suka shisshiga suka nufi gida
tun da suka shiga yasan cewa mai martaba yau
yana fada dan hakan fadan yashiga wacce ta
kayatu sosai, mai martaba yana zaune akan
wata karagar mulkinsa ta alfarma wadda tasha
ado da zinare, gefe daga hannunsa nadama
wazirine da galadima ga chiroma, kusa dashi
kuma hakimin cikin garine, daga hannun hagu
kuma wani dan dattijone zaune wanda
shekarunsa zasu kai na mai martaba kusa dashi
kuma san turakine wato faisal aminin tafida,
cikin sallama tafida yazauna yayi gaisuwa
yatashi yashige cikin gida yawuce dakin inno
yau bai wani jimaba yafito yashiga dakinsa yayi
wanka yafito cikin bakar riga da bakin wando,
yanufi lambu wanda yake girke acikin gidan,
wurin yasha shukoki na kayan marmari ga wata
korama daga tsakiya tana gudana can gefe
wasu kujerune hadaddu aka ajiye saboda
hutawa kan kujerar yaje yazauna amma ko minti
5 bai yiba yatashi yafita yanufi dakinsa yashiga
yakunna tv yakamo tashar kwallo yafara ganin
wasan arsenal da man u, wasan yafara kayatar
dashi faisal yashigo remote ya dauka yakashe tv
din domin yasan yanzu zasuyi fada saboda
faisal dan arsenal ne shi kuma tafida dan man u
ne gashi ancisu har 2-0 yasan idan faisal yagani
yau zai sha tsiya, kusa dashi faisal yazauna.
[8:32PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Kusa dashi faisal ya zauna yafara dariya ko
kallonsa tafida bai yiba yadauke kansa shikuwa
faisal sai dariya yakeyi, haushi tafida yafara ji
yace ya isheka haka,dariya faisal yayitayi sai da
yayi mai isar shi sannan yace kasan me nake
yiwa dariya? Jiya jiyan nan kagama yimun
bayanin kaifa bakasan hanyar da zakabi ba
awurin mace idanma aka ajiye maka mace
bakasan yadda zaka bida itaba to sai gashi
yanzu za abaka mace nan da sati 2,kaga ashe
kenan ka kusa kasamo hanyar ko? Wani kallo
tafida ya watsa masa ni zanyi aure amma ba
yanzu ba sai nan da 3years dariya faisal
yakumayi kasan Allah? Kai angone kakusa ganin
hanya, wai kai waya fada maka aure zanyi ne?
Uhm abokina bazaka yarda da abinda nake fada
maka ba sai kaji kira daga wurin mai martaba
sannan zaka gasgata ni, tsaki tafida yayi insha
Allahu kai zai yiwa aure amma baniba,ni daba
dan iska ba wa zaiyi min aure yanzu? Kai da
kasan mata kake nemansu ai kai yadace ayiwa
aure, dariya faisal yayi kasan Allah? Wlh kakusa
zama ango kai barima kaji dazu daka zo
kasamemu da mai martaba wlh maganar
aurenka akeyi kuma nan da sati biyu za ayi,
cikeda mamaki tafida ya kalleshi wai dagaske
kake yi? Wlh Allah dagaske nake tafida wlh aure
mai martaba zaiyi maka dazu akanka mukayi
meeting da yamman nan kuma wani abin
burgewar ma zaka samu virgin girl kamar yadda
kake virgin boy, zumbur tafida yamike ni za
ayiwa aure yanzu? Wanne laifin nayiwa mai
martaba da zai hukantani ta wannan hanyar? Wa
zai aura min? Yaya kamanninta suke? Girgiza
kai faisal yayi wlh ban saniba abokina, to nima
dai ummi Aisha ban saniba sai muci gaba da
bibiyar tafida, masu karatu muje zuwa kubiyo
Aisha.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [8:53PM,
11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Kallon faisal tafida yayi ai kuwa wlh bazai taba
yiyuwa ba nikadai ne da agidan? Akan me za ayi
min wani aure yanzu kai ba gaka nan ba haba
da Allah wlh bana so babu wanda zai rabani da
gidan nan yanzu, kuma wlh duk yarinyar da tayi
kuskure ta aureni sai ta raina kanta, dariya
faisal yayi wadda takara kular da tafida kaga
bani zaka fadawa ba kamata yayi kaje gurin mai
martaba kayi masa wannan bayanin amma nidai
ina tayaka murna sai dai shawarata agareka
itace kasan mai martaba baya yin magana 2
daga yayi magana to yagamata so be careful
kar kaje kajawa kanka, kaga mitumin nan
nadazu daka samemu afada dashi? Shine
mahaifin yarinyar wlh kayi dacen suruki cikeda
bakin ciki tafida yace malam banfa tambayeka
ba dan haka kayi min shiru banza kawai dariya
faisal yaci gaba dayi ganin haka yasa tafida
ficewa daga dakin yatasamma lungun inno
wadda yake da dan tazara daga sashensa, yana
shiga yatarar da bata cikin dakin sai kuyanginta
suna gyara dakin kusan ko wanne lokaci dakin
nata cikin gyaransa ake, shiyasa koda yaushe
yake cikin tsafta tamkar dakin sabuwar amarya,
suna ganinsa sukayi waje suka bar aikin da
sukeyi, gadon inno ya dale yakwanta idan
dasabo kowa agidan yasaba ganinsa akan gadon
inno koda wanne lokaci yagadama zai zo yahaye
yasha baccinsa akai kamar wani yaron goye.
[9:36PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Rufe idanuwansa yayi amma yasan ba bacci zai
iya yi ba maganganun faisal ne kawai suke
dawo masa jiya jiyan nan kagama fadamin idan
an baka mace baka san yadda zakayi da itaba
sai gashi nan da sati 2 zaka zama ango an baka
mata, zunbur ya tashi zaune jin abin yake kamar
a mafarki aurefa? Daidai lokacin inno tashigo
taganshi zaune akan gadonta, tafida ashe kana
nan? Nima daga wurin mai martaba nake yakira
ni yabani wani sako wurinka ras! Gabansa yafadi
wato maganar faisal ta tabbata kenan ai kuwa
tunda yake da mai martaba bai taba yimasa
musu ba amma awannan karon dai zai yi, domin
bai kamata ayi masa haka ba, abinda yafi
cancanta shine abarshi ya zabi matarsa da
kansa tunda sauran yayyensa ba haka akayi
musu ba, maganar inno ce ta dawo dashi cikin
hankalinsa mahaifinka yace nasanar dakai zai
daura maka aure nan da sati 2 da wata yarinya
yar gidan abokinsa amma ayadda naji yafada
yarinyar ma ba lafiyayyiya bace, cikeda damuwa
yace inno kuma ni za aurawa marar lfy? Haba
inno yanzu mace ma an daina yimata auren dole
balle namiji kuma naga sauran duk ba haka aka
yimusu ba agaskiya nidai afasa maganar auren
nan idan bahaka ba wlh za aji kunya, cikeda
tashin hankali inno tace haba tafida mai
martaba kake fadawa haka? Mahaifin naka zaka
kunyata a idon duniya? To bari kaji wannan
sakon naka yafi karfina sai dai yanzu katashi da
kanka kaje ka sanar dashi bazakabi zabin da
yayi maka ba, amma kasani mahaifinka ba yayin
magana 2 magana daya yakeyi kuma aduk inda
yasaka doka a garin nan ana bi balle agidansa
dan haka ina baka shawara da kayiwa
mahaifinka biyayya kar kajawo abinda zaiyi fushi
dakai, shiru tafida yayi ransa duk yagama
jagulewa wannan wanne irin abu ne? Shidai wlh
wannan auren bada shiba, kallon inno yayi to
inno abawa faisal mana amma sai ace ni za
abawa? Wlh bana so ni babu auren da zanyi ban
shirya yin aure yanzu ba kafin inno tayi magana
jakadiya tashigo gafara dai ranki yadade barka
da hutawa ayi min izini nashigo, kya iya shigowa
jakadiya inno tafada tana kokarin kishingida.
[10:49PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Shigowar jakadiya ne yasa tafida dago dara
daran idanuwansa yafara kallon jakadiya cikin
girmamawa jakadiya ta durkusa ranki yadade
barka da hutawa, Allah ya kareki uwar dakina
sarki ya aikoni, kallonta ta maida kan tafida mai
girma tafida sako daga mai martaba sarkin
adalci sarki nakwarai yace kaje yana son
ganinka cikeda damuwa batare da tafida yabata
amsa ba yatashi yafita izuwa lungun sarki gaba
daya jinsa yake kamar a mafarki, yana isa dakin
sarki yaja yatsaya abakin kofa sakamakon ganin
maga kofa dayayi toge akofar, cikin girmamawa
maga kofa yafada dakin sarki yayiwa sarki
bayanin zuwan tafida, yashigo sarki yafada
atakaice, dasauri maga kofa yadawo yayiwa
tafida iso suka karasa dakin sarki sannan maga
kofa yafita yabasu wuri sunkuyar dakai tafida
yayi Allah yaja zamaninka yanzu na samu
kiranka daga wurin jakadiya,eh nine naturata
takira min kai, ranka yadade na amsa kira,
ibrahim! Mahaifin nasa yakira sunansa na'am,
Allah yaja zamaninka, Allah yasa kafi haka
tafida yafada kansa yana duke akasa, dalilin
kiran da nayi maka shine kayi hakuri da abinda
zakaji daga gareni, wato ibrahim aure zanyi
maka nan damako biyu, ina fata zakayi dukkan
wasu shirye shiryen dasuka dace nan da sati
biyun, sannan ina so kayi hakuri da ita matar da
zan aura maka domin ba lafiyayya bace kuma ga
hotonta idan kana da bukatar gani, kansa akasa
yace ya mai martaba ayi min adalci kuma
asausauta min dan Allah afasa auren nan domin
banida shirin tunkarar aure ahalin yanzu, kai!
Wata tsawa mai martaba yadaka masa wadda ni
kaina ummi Aisha sai da narazana, bafa
shawararka nake nema ba umarnine nake baka,
yanzu kai ibrahim har kayi girman da zan fada
maka magana kayi min musu? Tuba nake ranka
yadade, natuba mai zamani, ayi min afuwa
hakika nayi kuskure amma ayafe min, cikin fada
sarki yace to aure babu fashi zan daura shi
inyaso aranar dana daura kana iya warwareshi
ta hanyar sakin matar, ai kuwa zan sakenta
tafida yafada acikin ransa.
[8:17AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Tabbas ko wacece sai narabu da ita danme
za ayi min auren dole bayan ga faisal nan shi ba
ayi masa ba, kuma naga komai mai martaba zai
yi tare yake yi mana nida faisal sai a wannan ne
za a banbanta mu? Fadan mai martaba ne ya
dawo da shi cikin hayyacinsa, sanin kankane ni
ba karamin mutum bane bare jama'ata su
rainani, bana alqawari in saba sannan bana yin
magana biyu dan haka dolenka ka amincewa
umarnina domin ba kaine ka haifeni ba nine na
haifeka idan hukuncin dana yanke maka yayi
maka tsauri to ka mutu kabar duniyar inyaso sai
ka huta da auren da zanyi maka, tuba nake
ranka yadade, ayi min aikin gafara, tashi kabani
wuri mutumin banza mutumin wofi, Allah ya huci
zuciyarka ya mai martaba cikin hanzari tafida
yatashi yafita gaba daya idanuwansa sun kada
sunyi jajawur kamar gauta, ransa in yayi dubu
yagama baci, dakin inno ya koma acan yaci karo
da momcy bai iya yi mata magana ba yashiga
dakin inno yazauna akusa da kafafunta, inno wai
dan Allah laifin me nayi muku ne haka kuka
tsaneni? Murmushi tayi irin nasu na manya haba
tafida na, da daya tamkar da dubu, wlh tafida
idan na rantse maka cewa dani da mai martaba
munfi sonka fiyeda kowa acikin yayanmu ba
zanyi kaffara ba, ni da mahaifinka duk cikin
yayanmu munfi nuna maka so da kauna ba wai
dan kasancewar ka dan auta ba a'a soyayyar
daga Allah take haka nan Allah ya sanya mana
sonka fiyeda sauran yan uwanka sannan nasan
mahaifinka bazai taba cutar dakai ba, saboda
idan kashiga damuwa sai yafika damuwar, dan
Allah tafida ka kwantar da hankalinka kayiwa
mahaifinka biyayya kaji? Shi wannan mutumin
da zai baka yar tasa mutumin sarki ne tun suna
yara, yayiwa sarki alherai da dayawa wadanda
bazasu lissafu ba to kaga kuwa shi ALHERI
DANKO NE! Baya faduwa kasa banza sannan
kuma dadi musanye ne, abinda nakeso dakai
kawai shine kayi biyayya, cikin kunar rai tafida
yace amma inno ga ba faisal nan ba why not shi
baza abashi ba? Sai ni za abawa danni aka
tsana? Kai rufe min baki marar kunya inno
tafada cikin fada dan kaga inata shawo kanka
ina lallaminka da kalamai masu dadi shiyasa
zaka fada min maganar banza? Anki abawa
faisal din kai aka yi niyyar bawa in yaso aranar
da aka daura auren ka saketa ko kuma idan
ankaita gidan naka ka kasheta kaji? Fitsararren
kawai in banda tsabar rashin kunya har sarki
yabada umarni katsaya kana ja in ja da
umarninsa? To sai gareka karka fasa, tashi
maza kafice min daga daki kuma kar nasake
ganin kafarka acikin dakina, da sauri tafida
yatashi yafita bayi da kuyangu sai mamaki suke
domin inno bata taba yiwa tafida irin wannan
fadan ba kowa agidan yasan tafida shine dan
lelen inno da mai martaba.
[8:41AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣5⃣
Na A'ISHA (UMMI)
Tafiya yake ahankali duk da cewa dama haka
yasaba tafiya amma tafiyar yau tasha banbam
data kullum lungun momcy mahaifiyar abokinsa
faisal kuma dan uwansa najini yanufa yana
shiga jakadiya tayi masa iso yakarasa dakin
momcy tana zaune akan gado wata baiwa tana
yimata firfita da muhucin kaba gefenta kuma
wata baiwar ce take yi mata labarun ban dariya
ko sallama bai iyayiba yashiga take bayin suka
bar abinda sukeyi suka tashi suka fita, akan
daddumar dake malale acikin dakin ya zauna
yadukar da kai barka da hutawa ranki yadade,
barka kadai tafida,cikin damuwa yace momcy ko
kin samu labarin abinda zai faru dani? Cikin
bacin rai tace nasamu tafida dazun nan jakadiya
tazo min da labarin kuma inaji banyi kasa
agwiwa ba natashi natafi wurin mai martaba
domin jin sahihancin labarin anan ya tabbatar
min da gaskiyar lamarin sai dai nayi takaici da
ba abar min kai kazabi matarka da kanka ba
kamar yadda aka yiwa sauran yan uwanka sai
amma kirana gareka shine kar kayi jayayya da
umarnin sarki domin hakan zai iya janyo maka
fushin mai martaba akanka sanin kanka ne kuma
fushin Allah yana daga cikin fushi na iyaye
wannan hadisine ingantacce saga bakin
annabinmu annabin rahma, kayi hakuri kayi
biyayya idanuwansa jawur ya dago yadubi
momcy dama momcy duk wanda kaji anbawa
hakuri ai cutarsa akayi cikin damuwa tace babu
komai tafida ni kaina narasa dalilin sarki
nayimaka wannan irin aure acikin gaggawa
amma babu komai kayi biyayya kawai ni naso
ace ma wannan shashan dan uwan naka faisal
za ayiwa auren, babu komai momcy nagode,
tashi yayi yafita yanufi sashensu shida faisal
yana shiga yasamu faisal kwance afalo cikin
kujera cikeda damuwa yanemi wuri ya zauna
faisal yana kallon fuskarsa yasan ya amsa kiran
mai martaba tashi zaune yayi yadafa kafadar
tafida abokina ya akayi? Kamar tafida zai yi
kuka yace faisal wlh bana son auren nan bana
so bana so, cikin damuwa faisal yace wlh tafida
dazun nan lokacin da akeyin maganar tun
alokacin nafara rokon sarki akan yayi hakuri
nasan bazaka so auren nan ba amma yaya
chiroma da baba galadima suka hayayyako min
da fada wai nida kai mun raina kowa afada
bama bin umarnin mai martaba saboda mu yan
gata ne nida kai ne kawai sarki zai bawa umarni
mu tsaya muna jayayya dashi ganin sun dauki
zafi yasa nataso nabaro wurin amma dan Allah
kar kadamu kanka, lallashin tafida faisal yayi
tayi da kalamai masu sanyaya zuciya tareda
nuna masa illar rashin bin umarnin iyaye.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:21AM,
11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Shidai tafida yau rauni yafi gaban ciwo kallon
faisal yayi kasan Allah? Ana daura auren nan sai
nasaketa kowacece cikin sauri faisal yakatse shi
kar kasoma yin haka abokina domin zaka aikata
babban kuskure kar kazo kayi abinda mai
martaba zaiyi fushi dakai, tashi tafida yayi
yashige daki yabar faisal afalo cikeda damuwa
domin damuwar tafida ta faisal ce.
***********************
Alhaji Ahmad Muhammad sani shine sarki na
uku ajerin sarakunan garin misau ta jihar bauchi,
garin misau babban gari ne sannan kuma babbar
masarauta ce mai girman gaske, sarkin misau
nayanzu shine sarki na uku yagaji sarautar ne
ahannun mahaifinsa alh Muhammad sani nabiyu,
alh Ahmad sani sarkin misau nayanzu yana da
matan aure 2 hajiya kilishi (inno) da hajiya
mabruka (momcy),hajiya Kilishi wadda akafi
sani da inno itace uwar gida sunyi auren saurayi
da budurwa ita da mai martaba lokacin baifi dan
shekara 23 ba alokacin aka nadashi sarkin garin
misau, Allah ya albarkacesu da yara guda 5
duka maza babban dan sarki shine chiroman
misau alh Muhammad sani sai mai bimasa
marafan misau alh adamu Ahmad sani sai
turakin misau alh jamil ahmad sani sai barwan
misau alh Mahmud ahmad sani sai kai gaman
misau alh mannir ahmad sani daga nan sai dan
autansu tafidan misau sannan hakimin disina alh
ibrahim ahmad sani, amaryar mai martaba
hajiya mabruka (momcy) yara biyu suka haifa
da mai martaba babbar yarsu itace hajiya
maryam (hajiya daso) sai kaninta alh faisal
ahmad sani san turakin misau hakimin dambam,
faisal da tafida tare suka taso adaki daya
kasancewar babu yan ubanci agidan kowa yana
kaunar dan uwansu bazaka taba iya banbance
tsakanin dan hajiya inno da dan hajiya momcy
ba saboda tsabar hadin kai, gaba daya yaran
inno adakin momcy suke tasowa yayinda itama
momcy ita ta aurar da hajiya daso kasancewar
bata da ya mace, shi kuwa faisal da tafida
kusan lokaci daya aka haifesu tsiransu kwana 5
ne atsakani shiyasa suka taso kamar wasu yan
biyu sannan suka zama abokan juna dukkaninsu
basuda wani aboki sai junansu tun suna yara
haka suke kiran junansu kuma wani abin
sha'awar shine bazaka taba jinsu sunyi fada ba
kullum cikin zolayar junansu suke, gashi suna
yar kama duk kuwa da cewar tafida yafi faisal
kyau domin shi mahaifiyarsa ya dauko ita kuma
bafulatana ce.
[10:03AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Tunda suka taso basa rabuwa tare suke yin
komai har suka zama samari shekarunsu daya
tsayinsu daya kuma ko amakaranta ajinsu daya,
tun lokacin da suka gama primary school suka
tafi america acan sukayi karatunsu gaba daya
suna gama degree suka jona masters dinsu,
zaman da sukayi akasar waje anan tafida ya
koyi shan ganye shikuma faisal yakoyi neman
mata amma daga nan baya wata dabi'a shima
tafida daga shan ganye baya komai mace kuwa
babu abinda yake hadashi da ita sai asibiti idan
bata da lafiya, tun akasar turai yan mata suke
nuna masa maitarsu afili daga turawan har
bakar fatar amma bai taba yadda ya kusanci
kowacce mace ba neman mata sai dan uwansa
faisal, suna kammala karatunsu suka dawo
Nigeria kowannensu yakama aiki shi tafida
kwararren likitane a fannin mata shikuma faisal
auditor ne a ministry for local government, basu
jima da fara aikiba akayi musu sarauta shi faisal
sarautar sa san turakin misau hakimin dambam
shikuma tafida sarautarsa tafidan misau hakimin
disina,tun asali shi tafaida bamai yawan
magana bane bashida surutu magana bata
dameshi ba wannan dalilin ne yasa ake yimasa
kallon mai girman kai yanmata dayawa kuma
suke masa kollon mai takama dakyau basusan
shi haka yakeba naturally.
***********************
Tafida yana shiga daki yakifa akan gado
zuciyarsa sai tukuki take tamkar zata fasa
kirjinsa tafito waje cikin damuwa faisal ya tashi
yabishi cikin dakin yaci gaba da bashi baki
amma tafida Ji yake kamar ya rushe da kuka,
tashi yayi ysdauko ganye yafara busawa
shikuma faisal ganin haka yasashi fara tsaki
dalla malam kafita waje kagama busa hayakinka
acan hararsa tafida yayi kana iya fita kai tunda
ba daureka nayi ba dan iska kawai, dariya faisal
yayi kaima ka kusa zama dan iskan ai tunda
kakusa sanin hanyar da baka sani ba, tsaki
tafida yayi yasake xukar tabar ya busar da
hayakin ai wannan hanyar ko zan santa ba
yanzu ba, kai dan iska ne sau nawa zaka santa?
Inji faisal murmushi tafida yayi kaine dan iska
amma ni banida hadi da kowacce mace,yanzu ai
zakayi hadin da ita faisal yafada yana dariya,
hira suka cigaba dayi har karfe dayan dare
sannan suka kwanta bacci amma shi tafida
bacci gagarar idonsa yayi shima faisal din baiyi
dayawa ba yatashi. Kamar yadda yasaba fita
yauma haka ya shirya ya dakin inno ya gaisheta
dakyar ta amsa fuskarta babu walwala, fitowa
yayi ya shiga dakin mai martaba shima hakan
take, dakin momcy ya shiga itace ta karbeshi da
fara'a ga kayan karyawa ta shirya masa sai data
kara yi masa nasiha sannan yatashi yatafi. Yana
zuwa asibitin su ya zauna jugum yana nazari
wai shi mai martaba zai yiwa auren dole, bayan
auren dolen ma marar lafiyace yarinyar, kai ai
auren nan bazai dadeba yafada yana bude
laptop dinsa.
[10:30AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Laptop dinsa yabude yashiga email dinsa anan
yaci karo da wani sako daga kungiyar litocin
mata ta duniya ta shirya musu wani course har
na tsawon wata 5 kuma har dashi aciki zasu
gudanar da course din ababban birnin kasar
India wato Mumbai dadi yadanji domin dama
garin yayi masa zafi da azamarsa yatashi yanufi
maternity domin duba halin da suke ciki. Tunda
yadawo daga office yakule adaki shi kadai
yafara cike ciken takardun tafiya course dinshi
anan faisal yazo yasameshi abokina dama kana
ciki, eh gani kaganni kuwa, akusa dashi faisal
yazauna me kakeyi? Wlh wani course zan tafi na
5 months, kai dazakayi aure wanne course kuma
zakatafi bayan ga babban course zaka samu
duka tafida yakaiwa faisal yace zan yimaka
rashin mutunci wlh, dariya faisal yayi duk
tsiyarka dai ana daura maka aure kazama
bazawari,waya fada maka? Wlh karya kake kaine
bazawari amma ni virgin ne dariya faisal yayi ai
mun kusa muga karshen virgin domin virgin zai
koma disvirgin dariya tafida yayi yace ka karaci
iskancinka kagama akwai ranar ramuko. Tuni
aka fara shirye shirye agidan mai martaba har
an hada kayan aure irin na al'ada dana zamani
ankai gidansu amarya kullum bushe bushe da
raye raye akeyi agarin mai girma tafida zai
angwance,ni ummi Aisha hannuna asama nace
Allah yaja zamanin mai girma tafida, tunda aka
fara shirin biki tafida baya shiga sabgar kowa
agidan tsakaninsa da kowa gaisuwa ce daga
angaisa shikenan dama can shi ba mai magana
ba da faisal kawai yanzu yake magana mai
tsawo shima faisal din dan bazai iya fushi dashi
bane saboda sun shaku sosai, amma ko inno da
mai martaba tsakaninsu gaisuwa ce yadda suke
fushi dashi shima haka yake fushi dasu, ana
igobe za afara gudanar da biki yafara shirye
shiryen tafiyarsa India domin nan da sati 2 zasu
fara gudanar da course din mai taken yaki da
cutar sankarar mama (cancer),shi dai faisal
shine yazama tamkar angon domin komai wanda
ango yakeyi shine yayi, shikuma tafida hakan ko
ajikinsa tashi yayi yaje wurin mai martaba yayi
masa maganar tafiyarsa India maimartaba bai
damuba yace babu matsala dama itama amaryar
taka karatu takeyi koda tana nanma nace babu
maganar tarewarta yanzu tunda bakaso duk
lokacin dakaso ta tare nan gaba, dukar da kai
tafida yayi yace godiya nake mai martaba Allah
yakara nisan kwana yatashi yafita.
[8:41PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
1⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana fita yayi kicibus da faisal kallon faisal
yayi yadauke kai domin yafuskanci faisal ya
zake akan auran nan, cikeda dariya faisal yaja
hannunsa mutumina ya akayi? Shiru yayi kamar
baijishi ba cikin zolaya faisal yace wai kai duk
dokin zaka samu hanyar ne ya hanaka magana?
Sai alokacin tafida yayi murmushi wlh kai
wannan yadama ni yanzu ba wannan ne
agabana ba, dariya faisal yayi zo muje abokina
kaji hannunsa yakama suka nufi cikin gida har
dakinsu suka zazzauna faisal ya dubeshi yace
dan Allah tafida ka tsaya ka nutsu ka rungumi
matarka shifa aure mukaddari ne, cikin jin
haushi tafida yace me zai hana kai ka rungumi
kaddarar ka aureta? Dariya faisal yayi ai ni ba
abani bane amma kai kaga da yake dan gatane
aure za ayi maka kasha sha'aninka tsaki tafida
yayi yajawo earphone dinsa yajona ajikin
wayarsa yafara shan sauti dariya faisal yayi
yace kadai kusa ka zama bazawari, jin shiru
tafida bai amsa ba yasashi gane cewa bai ji
abinda yace ba domin dayaji da sai ya bashi
kyakkyawar amsa domin babu abinda yatsana
irin yaji yakirashi da bazawari tashi faisal yayi
yafita yana dariya. Shirye shiryen biki ya
kankama yayinda shi kuma tafida yaketa shirye
shiryen barin kasar, ranar alhamis aka sanya
amarya a lalle faisal shine yake tsaye akan
komai kullum baya samun lokacin kansa daga
nan zai yi nan gidan mai martaba kuwa ya cika
yayi dam da al'umma garin in banda kade kade
da raye raye babu abinda akeyi domin sarki zai
aurar da dan autansa kuma dan gaban goshinsa
amma shi tafida in banda fushi babu abinda
yakeyi gaba daya yadaina walwala yazama
marar fara'a gashi kullum sai sunyi fada da
faisal, ranar juma'a aka fara niyyar daura auren
tafida amma kememe yaki kirshayawa.
[9:05PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣0⃣
Na A'ISHA (UMMI)
Babu yadda faisal bai yi da tafida ba kan ya
shirya su fita domin da misalin karfe 1:30 za
adaura auren amma yaki yarda yatashi ya shirya
tun faisal yana yimasa cikin lallami har yafara
fada shiru tafida yayi masa bai tanka masa ba,
ganin haka yasa faisal yakara tunzura ya hasala
yafita daga dakin, lokacin har su mai martaba
sun tafi inda za adaura suren, faisal shi kadai
yatafi yasha fararen kaya masu tsada yana
zuwa lokacin wurin yacika makil amma haka
yasamu ya kutsa ya isa wurin mai martaba sarki
yana ganinsa yafara tambayarsa ina tafida
cikeda damuwa yace ranka yadade bashida
lafiya ne bazai iya zuwa ba, cikin fushi mai
martaba yace yayi daidai kuma rashin zuwansa
bashine zai sani nafasa yimasa wannan auren
da nayi niyya ba, hakuri faisal yafara bawa sarki
tuba muke ya mai martaba ayi mana
uzuri,galadima ne ya matso yace ranka yadade
ni ina ganin afasa daura auren nan da tafida
abawa faisal, girgiza kai sarki yayi a'a galadima
banki ta takaba amma nidai da tafida zan daura
auren nan, nan aka fara daurin aure waliyyan
amarya sunzo aka daura auren tafida da
amaryarsa akan sadaki naira dubu dari, ana
gama daurin aure sarki yakira uban amarya gefe
yafara yimasa bayani kan cewar amarya ba
yanzu za akawota ba sai lokacin da yayi
magana gyada kai mahaifin amaryar yayi tareda
yiwa mai martaba godiya, ana kammalawa faisal
ya koma gida afalo ya taradda tafida kwance
yana danna wayarsa dariya faisal yafara yi
yamikawa tafida hannu assalamu alaikum mr
ango harara tafida ya cilla masa yayi tsaki wata
dariya faisal yayi mr ango asamo hanya lafiya
amma banda rashin imani dan wlh idan kayi
mata takarfi zaka iya kasheta, tashi zaune
tafida yayi wlh faisal kar ka kaini bango, ya
isheka, murmushi tafida yayi daga fadar
gaskiya? Allah yabaka hakuri gyara kayanka
baya zama sauke mu raba, murmushi tafida yayi
yau kam yazama amma kabari duk lokacin dana
nemi hanyar narasa zan nemi taimakonka, zama
faisal yayi bawani nan dama can kasan inda
take, wai kai sau nawa zan fada maka ne? Wlh
Allah ni ban san ta inda take ba kai nifa ko
haihuwa idan zan karba bana tsayawa naduba
kawai aikina nakeyi dariya Faisal yayi to
congratulations yanzu zaka gane ta inda take
sallamar jakadiya ce ta katse musu hirar tasu.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:27PM,
11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Har cikin falon jakadiya tashigo tarussuna
barkanku da hutawa samarin kwarai tafida ta
kalla ranka yadade mai martaba yana kira tana
gama fadin haka tajuya tana cewa afito lafiya,
tashi tafida yayi yafita shikuma faisal bai bishi
ba domin yasan fada zaisha awurin mai martaba
yana tsoron kar yaje ahada dashi, tafida yana
isa dakin mai martaba yasameshi shida inno da
momcy zazzaune gabansa wuri yasamu yazauna
gabansa yanata harbawa, cikin fada mai
martaba yafara magana ibrahim ka raina kowa
agidan nanko? Kanuna mana mu bamu isa dakai
ba kenan tunda har za muyi maka umarni amma
kasa kafa ka shure, saboda baka daukemu da
daraja ba shine zaka ki halattar daurin aurenka
ko? To ka kyauta kuma duk abinda kayi daidai
ne domin ahalin yanzu sai dai kanemi wani uban
amma baniba aure kuma nayi maka shi sai dai
zaka iya nunawa duniya rashin matsayina ta
hanyar sakin matar, nanfa inno itama tadauka
ya saketa mana shiyasani kuma mutumin banza
kawai kai in banda tsabar raini har ayi maka
umarni ka ki bi? Yaran yanzu bakuda kunya kota
sisin kobo muda aurenma basai an tare zakaga
matar ba,waye zai tsaya jin ra'ayin mutum,
hakuri momcy tafara basu hajiya inno ayi hakuri
dai, mai martaba dana yayi kuskure amma ayi
hakuri ayi masa gafara ayafe masa kar yashiga
cikin wani hali dan Allah aduba kokena, tashi
inno tayi tafita tanata fada shima mai martaba
tashi yayi yafice yatafi fada, kallonsa momcy
tayi tafida baka kyauta ba meyasa zakaki zuwa
wurin daurin auren? Cikin kasala yace momcy ni
auren ne bana so, 27 years nayi aure? Is too
early wlh,murmushi momcy tayi babu komai
yanzu abinda nakeso dakai anjima da daddare
kuzo kaida faisal kubawa sarki hakuri kaji? Naji
momcy, yawwa Allah yayi maka albarka, tashi
yayi shima yafita.
[9:47PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Da daddare faisal yasaka tafida agaba sukaje
wurin sarki suka bashi hakuri amma sai dakyar
suka samu ya sauko sa'arsu daya su yan
lelensa ne domin badan hakaba da zai dade
yana fushin bai huceba, daga nan sashen inno
suka shiga itama suka bata hakuri tsakanin da
da uwa sai Allah nan itama ta huce tace
tahakura suna dawowa dakinsu faisal yafara
bawa tafida shawara, abokina kafin katafi India
yakamata kaje kaga amaryarka kayi mata
sallama, tsaki tafida yayi naji zanje, yawwa
mutumina yakamata kaje. Abangaren gidansu
amarya kuwa koda mahaifinta yaje musu da
batun rashin tariya dawuri nan dangi suka fara
kace nace wasu kuma mamakine ya kamasu
wannan wanne irin aure ne kodan anga basuda
kudi shiyasa za araina musu wayo? Shidai uban
amarya baice komai ba kuma zancen da nake
yimuku har yau nidai ummi Aisha banga kalar
amaryar tafida ba balle na zayyano muku yanda
take, kasancewar sarki mutum ne mai adalci
yasa ya aikawa da gidansu amarya kayan abinci
kala kala yace arinka ciyar da amarya kuma duk
lokacin da yakare zai aiko wani sannan duk
wata bukata tata arinka sanar dashi hakan da
yayi ba Karamin dadi gidansu amaryar sukaji ba.
Tafida shirin tafiya yagamu domin yau saura
kwana 2 yabar kasar, wanka yayi ya shirya
yadau kwalliya cikin bakin danyen boyel yasa
bakar hula takalmin kafarsa ma baki yaafito sai
zuba kamshin turare yake take fadawansa suka
bude masa motarsa yashiga suka rufa masa
baya driver yaja sai disina, suna zuwa suka
zarce wani dan madaidaicin gida daga ganin
gidan gidan talakawa ne masu rufin asiri, cikeda
yatsina fuska tafida yafito daga motarsa yanufi
cikin gidan fadawansa suna take masa baya,
babu ko sallama yakutsa kai cikin gidan yana
rayawa aransa wai dan abin kunya nanne gidan
sirikansa kai Allah ya kiyaye, atsakar gida
yahango mahaifin matarsa da mahaifiyarta tana
hura wuta, kafarsa yasa yayi bol da wata buta ta
farin karfe atsakar gidan da alama butar mai
gidan ce, dayake gwanine wurin kwallo take
butar tawuce tasaman kan mai gidan taje tadaki
bango tadawo baya tafadi atsakar gidan ta
tankwashe yanda bazata moruba har abada.
[10:07PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikin tashin hankali mahaifiyar matarsa tafara
magana suwaye ku? Me kukazo yi anan gidan?
Cikin yayyatsina fuska tafida yadubi wannan
mitumin yace bawan Allah yadda kasa aka daura
min aure da yarka to tun wuri kaje kasa
awarwareshi domin bazan zauna da itaba kuma
bazan taba sonta ba, banda tsabar son zuciya
tayaya zaka dauki yarka ka kaiwa mai martaba
rallarta har alika min ita, to bana sonta kuma
sai nasaketa sai asannan suka gane ashe shine
mijin yarsu sirikinsu duk cikinsu babu wadda
yayi masa magana kawai tsayawa sukayi suna
kallonsa fadawansa kuwa sai fadi suke
hutawarka lafiya tafida wannan sako naka ya je
inda kakeso yaje, abi tafida a zauna lafiya tafida
buhun karangiya ko an zazzage dole sai ya
makale, gaba salamun baya salamun dan sarki
jikan sarki, gunbar dotse, icen kan kabari titi kafi
karfin a tsallakaka dole sai an waiga, takawarka
lafiya toron giwa dawisu da ado aka sanka,
ragayar dutse namijin fama, juyawa tafida yayi
yafita daga cikin gidan fadawansa suka rufa
masa baya kai tsaye fadarsa yawuce inda
wakilinsa yake, anan ya tambayi wakilin nasa
wacce gonace tafi kowacce girma agarin? Cikin
washewar baki wakili yace ranka yadade gonar
sirikinka malam faduluddeen gonarsa tafi
takowa girma cikin rashin damuwa tafida yace
ok to inaso nan da sati mai zuwa agyara min
domin zan turo masu aiki zasuyi min ginin gidan
shakatawata awurin, cikin mamaki wakili yace
yallabai sirikinka fa, ka iya bakinka wakili
fadawa suka fada lokaci daya, shiru wakili yayi
yace tuba nake yallabai tashi tafida yayi yana
bawa sarkin fada sallahun ginin da za azo ayi
masa, cikeda farin ciki yakoma gida domin
yasan abinda yayiwa mahaifan matarsa dole
zasuji haushi kuma kila zasu samu sarki suce
yasashi yasakar musu yarsu amma abin mamaki
shiru yaji ba wani batu alokacin har ansoma fara
yimasa ginin gidan da yabada umarni acikin
yanayin yashirya yanufi kasar india yana cikeda
haushin auren da yake kansa.
[10:45PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Lokacin da tafida ya tafi india ya samu damar
mantawa da auren dayake lankaye akansa sai
dai kusan kullum idan sunyi waya da faisal yana
yawan yimasa maganar amaryarsa dariya kawai
tafida yakeyi domin yanzu ya daina damuwa
idan faisal yana yimasa tsiya, cikin ikon Allah
yasamu yagudanar da course dinsa cikin
kwanciyar hankali da nasara wata 5 daidai yayi
yafara shiri ysdawo Nigeria. Ranar da yadawo
ranar fada ta cika makil da yan sannu da zuwa
faisal kuwa sai zolayarsa yakeyi amma
yashareshi har sai da suka koma daki sannan
yakalli faisal yace mekake cewa dazu? Dariya
faisal yayi abokina kayifa kyau sosai kayi fresh
kodai kabi hanyar ne? Tsaki tafida yayi kai wai
baka da wata magana sai kwaya daya? Ai ni
nafada maka ko zanbi hanyar da kake fada to
ba yanzu zan bitaba, dariya faisal yayi to malam
yakamata fa kasan inda dare yayi maka dan wlh
nakusa korarka daga dakin nan? Wazaka kora?
Kai zan kora tunda yanzu Kai magidancine so
sai kakoma wurin iyalinka, kamanta zurriyya ba
iyaliba tafida yafada tareda mikewa yafara cire
rigar jikinsa domin shiga wanka. Washe garin
ranar da tafida yadawo yakwanta yayi baccinsa
ranar bai je office ba sai wurin 11 sannan
yashirya cikin suit milk colour yasa milk colour
din takalmi yasha turare yafito dan zuwa
asibitinsu yana so yaje yakai report, agidan baya
yazauna acikin motarsa fadawansa suna tareda
shi har asibitin yana fitowa daga mota wasu
yanmata wanda zasu kai kimanin su 20 suna
sanye da unifoam suka fara kallonsa da alama
yan practical ne aka turosu asibitin duk cikinsu
babu wadda tafida bai tafi da imaninta ba nanfa
suka fara tattauna maganar a tsakaninsu. Sai da
tafida yayi hutun sati 2 sannan yafara zuwa
office aranar dayaje yana tsaye acikin office
dinsa yana daddanna wayarsa wata nurse
tashigo masa office akidime pls sir ka taimaka
mana munada patient wadda take neman
taimakon gaggawa kamar baijiba yayi har saida
ta sake maimaitawa sannan yace yaji yabi
bayanta har zuwa female ward can gadon
karshe takaishi tace gata sir wannan ce, gaban
gadon yakarasa wata yar budurwa yagani wanda
shekarunta zasu kai 23 aduniya tana sanye da
farar riga da bakin dark blue din wando daga
gani yar practical ce domin yaganta da unifoam
din yan lab science.
[11:12PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Kallon fuskar ta yayi kyakkyawa ce ta daukar
hankali shidai yana ganin mata masu kyau
amma baiga wadda ta kai wannan kyau ba duk
kuwa da cewa baka ce amma bakinta mai kyau
ne har wani shining take kallon nurse din yayi
me yasameta? Cikin inda inda tace let me go
and call her friend she's d one dat brought her
here, dasauri tafita Jim kadan sai gata dawata
budurwa itama tana sanye da uniform irin na
wadda take kwancen kallonta tafida yayi meya
sameta? Dr wlh kawai muna zaune mukaga
tafadi, sai alokacin yasa hannunsa yatabata
amma da bai taba koda hannunta ba ya salam!
Yafada saboda jin laushin fatar jikinta, nan
yafara jin wani yanayi ajikinsa daurewa yayi
yafara checking dinta anan yasamu yagano
matsalar tata yayi mata allurai har guda hudu
alokaci guda, kallo yabita dashi dama wannan ai
dole tasamu matsala saboda tahadu sosai
shiyasa takamu da ciwon mara mai tsanani
wanda bazata taba warkewa ba har sai tasadu
da namiji, fita yayi yakoma office dinsa sai 3
yashiga round yana shiga yan practical suka
fara gulmarsa wannan likitan duk asibitin nan
yafi kowa kyau, ai duk misau ma babu mai
kyanshi inji wata aciki, yana tafiya yana duba
patient har yazo gadon karshe inda yanmatan
nan suke, waje yace sufita yafara duba patient
dinshi wadda har ta wartsake kallonta yayi
doguwa ce baka tanada manyan idanuwa da
dogon hanci gata da dan tsukakken karamin
baki, gashin girarta mai yawane batada kiba
dayawa amma tana hips da cikar kirji sosai,
yanmata kin tashi? Ya tambayeta, biron
hannunsa ta karba da takarda tayi masa rubutu
kamar haka, bana jin abinda kafada ni bebiyace
kuma kurma ce, mika masa tayi yakarba ya
karanta cikeda mamaki ya rubuta mata, ayya
sannu, amma ko kin san ke kyakkyawa ce? Mika
mata yayi takarba tagani takaranta tayi masa
reply nagode amma Kayi hakuri ni matar wanice,
karba yayi yai murmushi nima mijin watane,
murmushi tayi wlh inada aure, bai gasgata ta ba
saboda yaga tana fama da matsalar ciwon mara
sperm yataru dayawa a mararta gashi har ya
haifar mata da ciwo shi kuma yasan da ace
tanada aure da hakan bazata faruba kallonta
yasakeyi waye zai mallaki wannan a matsayin
mata yatsaya yazuba mata ido yana kallonta?
Kai karyane gaskiya budurwa ce cikakkiya
kuma.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [12:16PM,
11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Wani tsadadden murmushi tafida yayi mata yace
ok koma dai menene bari na rubuta miki
maganin dazai taimaka miki, wata yar takarda
yadauka ya fara rubutu yana gamawa ya mika
mata gashi Allah yabaki lfy, duk wadannan
maganganun da yakeyi bata jinshi murmushi
yayi mata kinyi min kinyi daidai da tsarina
hannunta tadaga tayi mai nuni ma'ana me yake
nufi, murmushi ya sakeyi wanda har sai da
fararen hakoransa suka bayyana kumatunsa na
dama ya lotsa kusan ko magana yakeyi sai
yadan lotsa kallonsa tayi taji gabanta yafadi
wannan likitan yanada kyau tafada acikin
zuciyarta astagfurullah tayi saurin tuba saboda
tunowa datayi itafa matar aure ce, fuskarsa ta
kalla lokacin da yake yin rubutu ajikin takarda
yadan dunkuyar da kansa yanayi yana lasar
lebenshi nakasa wanda suke jaja jaja duhu duhu
domin tabar wiwin da yakesha tahadu da jan
lebensa sai tabada wata irin kala mai kyau
kamar yana shafa jan baki gashi farinsa irin mai
dan jan nanne kura masa ido tayi kai wannan
saurayin yana yimata kama da Seth rollins dan
wrestling domin har tsayinsu ma zai zo daya
gashi manyan idanuwansa ma irin nasane sak,
dagowa yayi yana murmushi yamiko mata
takardar yayi mata wani kasalallen murmushi
yajuya yafara tafiya ita dai nurse tana tsaye
tana kallon ikon Allah domin tunda take acikin
asibitin nan bata taba ganin dr tafida yayi irin
haka da wata patient ba babu ruwansa da kowa
tsakaninsa da kowa gaisuwa ce amma sai gashi
yau har dasu bude hakora taf lallai wannan
tacika mai nasara.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana juyawa marar lafiyar tafara kallonsa
yahadu sosai ta kissima aranta sai da yafita
tabude takardar da yabata tafara karantawa
kamar haka Yake kyakkyawa agaskiya yau idona
ya yi duban da be taba yiba hakika banyi
kuskure ba idan nakiraki da suna tauraruwa
kigodewa mahaliccinki domin ya tsara halittarki
irin tsarin da har yau banga wadda takaiki ba,
ina sonki zuciyata takamu da kaunarki alokaci
guda,ina taredake aduk inda kike luv u! I. T.
Tana gama karanta wasikar kawayenta suka
shigo dukkaninsu kowacce tana sanye cikin
unifoam nanfa wata daga ciki tafara yimata
tambaya da hannu alamar meya ce mata
murmushi kawai tayi bata fargaba taji sun fizge
takardar hannunta karantawa sukayi take kuma
bakin ciki ya mamaye zuciyoyinsu domin
agaskiya wannan likitan bai dace da ita ba dasu
yadace mutum dayace bataji haushin hakanba
asalima murna tayi sukuwa sauran ji sukeyi
kamar su shaketa dan haushi. Dr tafida yana fita
daga female ward yanufi office dinsa zuciyarsa
cikeda tunanin yarinyar da yagani sai dai yana
jin tausayinta har cikin ransa domin abin
atausaya matane gata budurwa har budurwa
kyau iya kyau amma dayake Allah alhakimu ne
sai ya iyota kurma kuma bebiya, duk da haka
zuciyata tana sonki yanmata ni babu ruwana da
jinki ko maganarki ke kawai naji ina so, zama
yayi yafara kiran fadawansa minti kadan sai
gasu kayansa yace su hada masa zai tafi gida
babu bata lokaci suka harhada duk wasu
abubuwa nasa suka fita,tashi yayi yacire bakar
coat din jikinsa yabar iya tacikin wadda take
light green mai dogon hannu da neck tie baki da
green, ahannunsa yariko rigar idonsa yana sanye
cikin farin glass yana tafe yana daddanna
wayarsa.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Fadawansa na hango shi suka zabura suka zo
suka fara take masa baya suna tafe suna zabga
kirari, takawarka lafiya, alafiya dai tafidan alheri,
gaba salamun baya salamun namijin fama,
babban goro sai magogin karfe, karo da karo sai
rago, wani Kaya sai amale wane jaki, buhun
kaya kake mai daukarka sai wanda ya shirya,
kogi ba ayi maka katanga, kaga katangar sukari
kowa ya jingina sai ya lasa, sauka lafiya dan
ahamadu jikan sani, farin wata sha kallo, lafiya
dai mai dogon zamani, gaba salamun baya
salamun,shi dai tafida tafiya kawai yakeyi yana
yin waya da faisal amininsa kuma dan uwansa
har ya isa gun motarsa suka bude masa ya
shiga ya zauna, daliban nan duk akan idonsu
hakan tafaru har motar tafida tafita daga cikin
asibitin, daya daga cikinsu mai suna sakina
itace ta tabe baki wai kuga haduwar wannan
gayen amma yarasa wacce zai so sai waccan
kurmar,bebiya dukansu baki suka tabe wayaga
abinda rai keso inbanda haka me zaiyi da ita
kuma kunji ma dan gidan sarki ne ashe, daya
daga cikinsu ce ta katsesu haba sakina meye
amfanin haka? Ina ruwanku dasu, wannan abun
da kukeyi babu kyau hassada ce ita kuma
hassada Annabi yayi hani da ita domin akwai
wani ingantaccen hadisi da manzon Allah s.a.w
yake cewa iyyakum wal hasadu, fa innal hasadu
ta akulul hasanati kama ya akulul narul hadabe,
ma'ana nahaneku da hassada domin ita hassada
lallai tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda
wuta take cinye itatuwa ko kuma karare, dan
haka wannan abin da kukeyi wlh bashida amfani
ko kadan,soyayya ta Allah ce idan kukayi hakuri
kuma zaku samu rabonku, tana gama fadin haka
tabar wurin takoma cikin female ward, tsaki
sakina taja wannan damuwarki ce amma wlh
bazai yiyu ace mu masu baki da kunne yakimu
yaso kurma ba. Tafida jinsa yake kamar bashiba
har yaje gida,shidai bai taba soyayyaba asalima
ko budurwa bai taba yiba saboda shi miskili ne
nagaske kai kallon mata ma bai dameshi ba,
baya hulda da mata ko kadan amma yau yayi
gamo, gamo wanda za a iya cewa kyakkyawan
gamo.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
2⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikeda farin ciki ya isa gida sai wata walwala
yakeyi marar kan gado domin babu wadda ya
saba ganinshi cikin wannan yanayin su kansu
fadawansa mamaki sukeyi yadda yau yake cikin
nishadi da walwala, suna isa tangamemen
gidansu yafito daga cikin mota fadawan dasuke
tsaron kofar suka mimmike tsaye suka fara
gyara kintsi gaba salamun baya salamun barka
da shigowa tafidan zamani tafida ba akawo
maka wargi, takawarka lafiya dan toron giwa,
dan zaki kafi karfin rainon kura, ko kura ta mutu
tafi karfin kare yaja gawarta, namijin dawa kake
mai kayan alfarma, barka da shigowa zaki
dangin sikari, tsawo dangin rama, takawarka
lafiya gaba salamun baya salamun, cikeda jin
dadi tafida yadaga musu hannu kamar yadda
yasaba yanufi zauren dazai sadashi da lungun
mai martaba yana zuwa kansa tsaye yawuce
cikin dakin mai martaba yasameshi zaune yana
kallon labarai atashar CNN zubewa yayi yafara
diban gaisuwa, sannan yatashi yafita yanufi
wurin inno itama a falonta ya taradda ita tana
kishingide jikin tumtum ga bayi zagaye da ita
sunayi mata firfita ka kayan motsa baki a
gabanta shiga yayi yazauna a kan kujera bayinta
suka tashi suka fiffita anan ya zamo kasa ya
gaida ta yatashi yafita yau gaba daya jinsa yake
kamar wani sabon mutum dan tsabar nishadi,
yana isa dakinsu yashiga toilet yayi wanka
yafito yasaka kayan yan kwallo jar riga mai
number 1 ajikin rigar da wando dogo,adaki yayi
salla yana idarwa yafito yanufi wurin dawakansa
yasamu har an daura masa sirdi domin fita kilisa
shi kadai kawai ake jira baiyi wata wata ba ya
haye dokin shima sarkin fada yahau nasa da
alama yau su biyu zasu fita kilisar, tafe suke
ahankali kowannensu rikeda linzamin dokinsa
har suka isa wasu manyan gonaki, tafida ne yayi
yar magana ahankali kamar yadda yasaba, sarkin
fada wannan gonar idan baka mantaba nataba
fada muku zatayi daidai da tsarin danakeso
wurin gina business suit dina, Allah ya
taimakeka tafida sarkin fada ya fada,amma
yallabai wani hanzari ba gudu ba wannan gonar
itama ta sirikinka kace idan ban mantaba,
yatsina fuska tafida yayi koma tawaye a cikin
satin nan za afara yimin aiki, Allah yaja
kwana,Allah yasa kafi haka, sarkin fada yafada
amma acikin zuciyarsa cewa yake wannan
wanne irin mutum ne ace duk gonakin sirikinka
sai bi kakeyi kana karbewa kana gini marassa
dalili.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI
DANKO NE!
3⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Haka suka karaci shawaginsu suka koma gida
lokacin magriba tana daf da kawo jiki, suna isa
gida tafida yasauka daga dokinsa a gajiye ya
shige gida afalonsu ya zube akan carpet ya
kwanta gaba daya ya gama gajiya, jinsa yake
kamar yayi wani gagarumin aiki, fuskar wannan
yarinyar ya hango take yayi wani murmushi
insha Allahu sai na auri wannan yarinyar yafada
azuciyarsa domin kyakkyawa ce ajin karshe,
amma mamakinsa shine yadda take karatun
science alhalin kuma bata ji kuma bata magana
hakika ta cika yar baiwa gashi komai nata mai
kyaune tamkar ita tayi kanta saboda yadda
halittar ta tatsaru sosai, lumshe manyan
idanuwansa yayi oh ko meye sunanta? Tsabar
yarude yamanta bai tambayi sunanta ba
shigowar faisal cikin falon ne yasashi dago
kansa yakalleshi abokina daga ina? Zama faisal
yayi daga dambam nake kasan garin nawa
kullum basa rabo da rikicin manoma da
makiyaya, murmushi tafida yayi uhm dakyau
hakimi, dariya faisal yayi kaima dai dadinta
hakimin ne, murmushi tafida yayi masa wadda
har saida faisal yayi masa magana yau naga
kana ta fara'a kodai? Murmushi tafida yayi babu
abinda yafaru amma nazo maka da albishir
nasamo matar aure dariya faisal yafara yi
bakada seti tafida yaushe kayi aure da har zaka
fara neman wani? Tsaki tafida yayi kaga babu
ruwanka malam ni namanta ma wlh da wani
auren da mai martaba yayi min, kallonsa faisal
yayi to wlh kafadawa yarinya gaskiya tunda wuri
ka sanar da ita gaskiyar lamari kai bazawari ne
ba saurayi ba dan kanada mata yakarasa
maganar cikeda dariyar mugunta,shiru tafida
yayi masa bai bashi amsaba amma yatsani
faisal[truncated by WhatsApp]
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [12:16PM,
11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
Post Top Ad
Your Ad Spot
Monday, June 4, 2018
ALHERI DANKONE Complete
Tags
# HAUSA NOVELS
About Arewa Tricks
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.
HAUSA NOVELS
Category:
HAUSA NOVELS
No comments:
Post a Comment