Dokin zuciya: Neman budurwa daya ya sanya wani mutum cinnawa dayan wuta - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Thursday, June 21, 2018

Dokin zuciya: Neman budurwa daya ya sanya wani mutum cinnawa dayan wuta

Kishi kumallon mata, amma a yau kishin
ya zama kumallon maza

- A jihar Naija wani mutum ne yayi
balangun abokin takararsa

- Tuni jami'an 'yan sanda suka damko shi
kuma har suna shirin gurfanar da shi
gaban kotu
Neman aure cikin nema ya sanya wani
mutum da aka bayyana sunansa da
Baba Muhammed mai shekaru 45
cinnnawa abokin karawarsa Usman
Tetengi wuta a jihar Naija.

Yanzu haka dai bayan babbaka abokin
neman budurwar tasa Mohammed dan
asalin kauyen Baba Edo ne dake
karamar hukumar Lavun a jihar na can
a hannun jami’an ‘yan sanda.

Neman budurwa daya ya sanya wani mutum
cinnawa dayan wuta
Tun da farko a cewar Muhammed ya
gargadi Usman da hawainiyarsa ta
kiyayi ramar matar da zai aura don
kuwa har yayi tambaya amma Usman
din yaki ji balle ya saurara.

Sannan ya bayyanawa ‘yan sanda cewa
ya dauki matakin ne domin yayi duk
mai yiwuwa don ganin usman din ya
kyale masa matar da yake mutukar son
aura, kuma ko kusa ba ya nadamar
wannan aika-aika da yayi.


“Ba na nadamar abinda na aikata
saboda inda ban kashe shi a lokacin ba
da ni zai kashe, gara ya tafi can don kar
ma ya sake hada hanya da ni”
“Ban yi aure ba, kuma ban damu da duk
matakin da zai biyo baya ba, abu mai
muhimmanci kawai shi ne nayi
maganinsa daga shiga sabga ta.

Akwai
mata da yawa amma sai ya zabi ya
cigaba da neman matar da na riga da
nayi tambayar aurenta, hukuncin da na
dauka shi ne ya dace da shi”. Baba ya
jaddada.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar
Muhammad Abubakar ya bayyana cewa
wanda ake zargin ya aika wani yaro ne
mai suna Abdul ya siyo masa kwalba
uku na fetir wanda yayi amfani da shi
wajen babbaka abokin neman
budurwar tasa.

Abubakar ya ce anyi sauri an garzaya
da wanda iftila’in ya faru da shi cibiyar
kula da lafiya ta tarayya (FMC) dake
Bida daga basani kuma aka mayar da
shi zuwa asibitin Gwagwalada na Abuja
inda ya cigaba da karbar magani kafin
daga bisani rai yayi halinsa.

Kuma za’a kai maganar gaban alkali da
zarar an kammala bincike.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad