MIJINA SIRRINA Complete - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Monday, June 4, 2018

MIJINA SIRRINA Complete

MIJINA SIRRINA 1-20
[7/4, 5:13 AM] Humaira Khaleel:
_©HASKE
WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
*​MIJINA SIRRINA​.....!*🌹
_(Labarin K'auna)_
**Based on a true life story**
_*NA​​*_
*_​​UMMI A'ISHA​​_*
_​Dedicated to Alh .I. Uba family​_
*_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA
MAI JIN
K'AI,Rabbishrahli sadri, wa yassirli
amri, yafqahu
qauli.._*
_Shafin farko nakine pherty b~b.._
*​1​*
~~~ "Oyoyo yaya kabeer...,oyoyo yaya
kabeer.."
Wannan shine ihun da yaran dake
zaune cikin
tsakar gida suna wasa suketa faman yi
daidai
lokacin da suka ga shigowar matashin
saurayin
wanda ke sanye cikin farar shadda
kansa babu
hula sai yar kyakkyawar suma da ya
dan ajiye,
Fuskarshi dauke da murmushi ya
rungume yaran
wadanda akalla zasu kai su kimanin
guda hudu,
Daga inda take acikin kitchen ta sake
lab'ewa
saboda bata son ya ganta duk da sanin
cewar
dominta yazo gidan, sadadawa tayi ta
buya a
bayan fridge gamida leka kanta ta
window ta
yadda tasan bazai iya hangota ba,
Ganinshi tayi rike da hannun Amira
da waleeda
kannenta sannan ga amir da husna
atsaye sai
faman jajja masa riga suke suna
tsalle,manyan
chocolate samfarin coconut chocolate
ya debo
daga cikin aljihunsa ya mimmikawa
yaran,
Sunkuyawa yayi wurin Amira saboda
itace babba
tafi su husna wayo,
"Amira ina mama?"
"Tana falon abba?"
"Yaya NADIYA fa?"
"Tana kitchen mama tasata aiki.."
Murmushi yayi ya mike saboda yasan
aduk inda
take taji shigowarsa shiyasa ta gudu ta
buya,
Yana rikeda hannun su Amira ya bi
hanyar da
zata sadashi da falon Abba,
Sai da ya tsaya yayi sallama mama ta
amsa ta
bashi izini sannan yasaka kai ya shiga
cikin
falon,
Mama yasamu zaune kusa da abba
suna yin
hira gefe daya kuma kwanukan
abincine da
abban yaci kasancewar bai jima da
dawowa
daga wurin aiki ba,
Su walida da amira na biye dashi har
cikin falon
sai da suka rakashi ciki sannan suka
ruga da
gudu suka fita,wuri yasamu ya zauna
kanshi a
kasa saboda kunya da kuma
girmamawa,
Ganinsa yasa abba sakin fara,a tareda
mikewa
daga kishingiden da yake ya gyara
zamansa
yana murmushi,
"Kabeeru yanzu kake tafe? Barka da
zuwa.."
Cikin jin kunya da sose sosen keya
kabeer ya
daga ido ya kalli Abba,
"Ehh wallahi abba, shigowata kenan
dama nazo
ne in gaisheku saboda kwana biyu ban
samu
damar shigowa ba.."
Murmushi Abba yasake yi ya kalli
kabeer din,
"Haba kabeer har yaushene rabonka
da gidan,
nazaci ai jiyane kawai baka zoba
amma ai
shekaran jiya ma kazo kodai ka manta
ne?"
Maganar da abba ya fadice tasa mama
tsoma
bakinta tana dan murmushi amma
fuskarta babu
yabo babu fallasa,
"To ai Alhaji tunda yasaba zuwa
kullum jiya
kuma baizo ba ai dole yaji kamar yafi
sati daya
rabonsa damu"
Dariya abba yayi yakoma ya
kishingida yana
kallon kabeer wanda ya gyara zama
yafara
gaisar da mama,
Shiru falon ya danyi nawani lokaci
saboda shi
kabeer nauyin mama da abba yakeji
yanzu sam
baya iya sakewa yayi hira dasu yanzu
kamar da,
Ganin yanata zaune shiru sai dai dan
lokaci
zuwa lokaci abba yana sakoshi cikin
zancen da
suke yi da mama yasashi mikewa,
"Abba bari naje waje.."
"To kabeer tafiya zakayi?" Abba
yafada yana
gyara zamanshi,
"A'a ba tafiya zanyi ba waje zanje"
Fita yayi daga cikin falon cikeda
kunya, yana fita
abba ya dubi mama yana fara,a,
"Nasan dama ba tafiya zaiyi ba wurin
mutuniyar
tasa zaije.."
Shiru mama tayi batace komai ba
saboda ita
kwata kwata bata son wannan
maganar saboda
wani dalili wanda ta barwa zuciyarta
ita daya
amma idan hali yayi zata bayyanar
dashi ga
abban shima yaji, ganin taki zancen
yasa abba
barin maganar ta hanyar shigo da
wani zancen
daban domin ya fahimci duk lokacin
da zaiyi
magana makamanciyar wannan
wadda ta shafi
kabeer da nadiya mama bata bada
goyon baya.
Yana fitowa daga falon abba cikin
kitchen
yawuce, a bakin kofar kitchen din ya
tsaya
saboda ganinta da yayi tsaye tana
mopping
bayan ta kammala share cikin kitchen
din,
Yarinyace yar budurwa wacce bazata
wuce
shekaru goma sha biyar aduniya ba,
tanada
hasken fata amma ba farace can ba,
tana sanye
da atamfa kalar koriya dinkin riga da
zani, daga
inda yake yana iya hango gashinta
dake
nannade cikin dan kwalin dake daure
akanta,
"Sannu da aiki.." Yafadi yana
murmushi har
lokacin yana tsaye akofar kitchen din,
"Sannu da zuwa yaya kabeer" tafada
ahankali
sannan maganar ma tayi tane cike da
kunya,
"Yawwa sannu sarki aiki.."
Tunowa da tayi cewar bata gaidashi
ba yasata
saurin dan rissinawa,
"Yaya kabeer ina wuni?"
"Bazan amsa ba har sai kin jiyo kin
kalleni ido
da ido.."
Murmushi yasaki bayan ya furta mata
hakan
saboda yasan ba karamin aiki ya
hadata dashi
ba domin kunyarshi da takeji bazai
taba barinta
ta iya hada ido dashi ba...
_*Ummi Shatu*_
[7/4, 5:13 AM] Humaira Khaleel:
_©HWA_
*MIJINA SIRRINA.....!*🌹
_(Labarin k'auna)_
**Based on a true life story**
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Alh .I. Uba family_
_Fatan alkhairi ga k'awata maryam
qaumi,
kina raina akoda yaushe yan matan
shaddad.._
_*2*_
aishaummi.blogspot.com
~~~Jin abinda ya fada ya sata sake
sinne kanta
kasa tana kallon tiles din dake malale
a kitchen
din,
"Bazaki gaida ni ba kenan in tafi ko?"
Kabeer ya
fada har lokacin fuskarshi tana dauke
da
murmushi,
"To ba na gaisheka ba kaki amsawa"
nadiya
tabashi amsa tana mai sake juya masa
baya
dan kar yaga fuskarta,
"Nadiya kenan wai wannan kunyar
yaushe zaki
dainata ne? Kullum idan nazo sai ki
gudu ki
buya alhalin nikuma saboda ke nake
son zuwa
gidan nan, duk ranar da ban gankiba
idanuwana
radadi da zugi suke yimin, kuma nazo
sai ki
hanawa idanuwa tozali da
kyakkyawar fuskarki?
Uhm nadiya? Dan jiyo mana.."
Badan taso ba ta dan jiyo dakyar tana
kallon
kasa,
"Kinga kyankyaso nan a bayanki.."
Tun kafin ya karasa maganar ta dako
tsalle
tabar wurin sai gata a bakin kofar
kitchen din
kusa dashi, dariya ya fara yimata
domin dama
yasan tana mutukar jin tsoron
kyankyaso
shiyasa lokuta da dama yake tsoratata
dashi,
Ganin yanata dariya yasata gane
cewar ba
dagaske yake ba,
Fuska ta bata, "yaya kabeer ashe dama
tsokanata kake?"
Dariya ya sakeyi ya daga mata gira,
"Wasane matar yaya kabeer.."
Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cikeda
kunya
domin kowa adangi da haka yake
kiranta tun
tana yar jaririya har ta girma, kowa
matar
kabeer yake cemata,
"Yau ina ka bar hular taka ka taho
haka?"
Sai da ya dan matsa kusa da ita
sannan
ahankali yace,
"Wai duk zumudin zuwa ganinki ne
yasani
manto wayata da hulata adaki har sai
da nazo
nnpc sannan na ankara.."
Dariya itama tafara yi masa, yayinda
shikuma
ya tsaya yana kallon yanda kumatunta
ke
lobawa, hakan ba karamin burgeshi
yakeyi ba,
"Kici gaba da dariyar bana son ki
daina"
Tsagaitawa tayi daga dariyar da
takeyi,
"Yaya kabeer na kawo kayi min
assignment din
biology? Skeleton teacher dinmu yace
mu zana
nikuma ban iya drawing ba"
Makale kafada yayi,"nima ban iya
drawing ba.."
"Please yaya KB"
Jin abinda tace yasashi kallonta tareda
sakin
wani tattausan murmushi,
"Dauko nayi miki"
"Yawwa yaya kabeer thanks.."
Rabawa tayi ta gefenshi ta wuce
fuskarta dauke
da murmushi, juyawa yayi ya bita da
kallo,
yanzu SS 2 take a secondary school
alla alla
yake ta kammala domin so yake ya
zama
mijinta sirrinta,
Yana nan a tsaye har ta fito hannunta
rikeda
pencil, cleaner da note book dinta sai
kuma
modern biology, tsayawa tayi ta
bayanshi tana
kallonshi domin a zahirin gaskiya
yayi mutukar
tsaruwa sam bashida makusa ko
kadan.
Babu zato ya jiyo nan tayi gaggawar
dauke
idonta daga gareshi,
"Yaya KB gashi.." Tafada cikeda jin
kunyarsa
domin tasan yagane kallonsa ta tsaya
yi,
Hannu ya mika ya karbi books din
hannunta
sannan ya sakar mata wani
murmushi, ahankali
ya furta,
"Ki ware idanuwanki ki kalleni son
ranki kidaina
kunya saboda nidin nakine...."
Fuskarta ta rufe da hannayenta ta
juya ta nufi
cikin kitchen tana cewa "kai yaya
kabeer.."
Murmushi yayi kawai ya nemi wuri ya
zauna kan
wani dan dakali dake zagaye da wasu
flowers
wanda yake opposite da kitchen din,
Zana mata skeleton din yafara yi
yayinda ita
kuma ta kafeshi da ido tana daga cikin
kitchen
din bayan ta kammala mopping din
da take yi,
Kallonshi ta tsaya take tayi ko kiftawa
batayi,dago kanshi yayi da niyyar yi
mata
magana nan ya kamata tana aikin
kallonshi,
Saurin kawar da kanta tayi ta juya
zata koma
cikin kitchen nan yayi gaggawar
dakatar da ita,
"Nadiya zo nan.."
Tana rufe da fuskarta ta karasa
gabanshi ta
tsugunna,
"Meye kike satar kallona?? Ba nace
miki idan
kina son kallona kawai ki kalleni
kanki tsaye
batare da kunya ba..?"
"Nifa ba kai nake kalloba yaya kabeer"
tafada
muryarta na rawa dan jin kunyarsa,
"To naji, idan nazana miki skeleton
din ai basai
nayi miki labelling ba ko?"
Kai ta daga masa batare da tayi
magana ba,
Murmushi yayi yaci gaba da zanen,
"to bani
labari inji.."
"Yaya kabeer nikuma wanne labari na
iya bare in
baka?"
"Ko na makarantarku ma idan kika
bani ina so.."
"Ai makarantarmu babu wani labari
acikinta"
"Kedai kawai bakya son ki fada min
labarin
makarantarku..."
Kafin ta bashi amsa mama ta zo daf
dasu zata
shiga kitchen domin dora tuwon dare,
batare da
mama tayi magana ba tasaka kai ta
shige cikin
kitchen,
Ganin mama yasa hirar tasu takare sai
aikin
murmushi da suke aikawa junansu,
Littattafanta ya mika mata ya tashi
tsaye yana
yimata wani murmushi wanda ita
kadai ce ta
fahimci sakon da yake son isar mata,
Kitchen yabi mama yayi mata sallama
ya wuce
batare da yayiwa nadiya magana ba
amma
kuma yana ta kokarin aika mata da
sakon
bankwana ta cikin idanuwansa sai dai
ita ta
kasa kallonshi, tana tsaye tana satar
kallonsa
har ya fice daga gidan,wucewa tayi ta
nufi
dakinsu itada su amira,
Akan gadonsu ta zube tana mai tuno
yaya
kabeer acikin zuciyarta duk da cewar
har yanzu
bai bude baki ya furta mata kalmar so
ba amma
tasan soyayya suke yi a boye ita dashi
batare
da sun bayyanawa junansu sirrin dake
cikin
zuciyoyinsu ba.
*_Ummi Shatu_*
[7/5, 3:35 PM] Ummi A'isha🏻:
*MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*HASKE WRITERS ASSO.*
**True life story**
*3*
aishaummi.blogspot.com
~~~Note book dinta ta bude tafara
kallon zanen
skeleton din da yaya kabeer yayi
mata, gefe
daya kuma kamshin turarenshi ne
yake tashi
daga cikin littafin,
Bin zanen kawai take yi da kallo tana
murmushi
wanda ita kanta bata san ko na
menene ba
amma kuma zuciyarta tafi aminta da
cewar
kawai na tsantsar farin cikine,
"I love you yaya kabeer.."
Tafadi ahankali tareda lumshe
idonta,waleeda ce
ta shigo cikin dakin da gudu,
"Yaya nadiya kizo inji abba.."
Ajiye littafin tayi ta dauki hijabinta ta
fita
saboda al'adar abbansu ce haka duk
lokacin da
ya dawo daga office ko kasuwa to
tattara
yaranshi yake yi a falonsa suyi hira
masu wasa
suyi wasansu yana zaune yana
kallonsu masu
karatu kuma suyi har lokacin sallar
magrib yayi
a lokacin ne kowa zai dauro alwala
yajasu jam'i,
haka sallar isha ma, wannan dalilin
ne yasa su
nadiya basa fita ko ina idan ba
makarantar
islamiyya ko boko ba sannan hakan
ya haifar da
shakuwa mai karfi a tsakaninsu dashi,
Ahankali ta tura kofar falon abbansu
ta shiga,
kishingide ta sameshi yana kallon
labaran
yamma a tashar AIT, can gefe daya
kuma Amira
ce da amir suke rubuce rubuce ajikin
littafinsu
na makaranta da alama home work
suke yi, sai
husna da walida daketa aikin
mammatsa game
wanda duk karar game din ta cika
cikin falon,
"Sannu da hutawa abba.." Nadiya
tafada tana
kokarin zama kusa da abban nasu,
"Yawwa nadiya, kabirun har ya tafi
ne?"
"Ehh abba ya tafi yanzu bai jima da
tafiya ba.."
Shiru abban yayi ya maida hankalinsa
ga kallon
labaran da yake yi, ita kuma nadiya
wurinsu
Amira taje tasa ido tana ganin yanda
suke yin
home work din har mama ta shigo ta
iskesu.
K'arfe 9 nadare bayan su nadiya sun
kammala
cin abincin dare mama tace suje su
kwanta
domin har waleeda da husna sunyi
bacci su
amir ne kawai idonsu biyu,
D'aukar husna nadiya tayi zuwa
dakinsu ta
kwantar da ita akan katifarsu sannan
ta sake
zuwa ta dauki waleeda taje ta kwantar
da ita su
Amira suna biye da ita, gyarawa amir
wurin
kwanciyarsa tayi ya kwanta sannan
itada Amira
suka haye gadon dake cikin dakin
suka kwanta,
Wayar mama dake ajiye a karkashin
pillow dinta
ta zaro ta yiwa yaya kabeer plashing,
kusan
kullum haka suke raba dare suna hira
a wayar
mama amma ita maman sam bata taba
sani ba
ita dai kawai tasan nadiya bata taba
barin
wayarta ta huta mutukar tana gida sai
dai idan
makaranta ta tafi to lokacin ne
wayarta zata
samu lafiya.
Ko minti biyu da yi masa plashing din
bata yiba
ya kirata,da murmushi akan fuskarta
ta daga
wayar,
"Yaya kabeer kaje gida lafiya?"
"Lafiya lau nadiya, yasu mama?"
"Suna nan lafiya"
"Ya kunya?"
Dariya tasa saboda jin abinda ya fada,
"Yaya kabeer kenan kaima ai ya
kamata ka rinka
jin kunyata.."
"Saboda me?.. "
"Saboda na cancanci hakan.."
Murmushi ya saki kafin ya bata amsa,
"See you, idan a wayane kibi ki isheni
da surutu
amma idan nazo sai kiyi shiru ki kasa
magana
kamar wanda zan kamaki"
Itama dariyar tayi, "to ba kaine ba"
"Nine me?"
"Kaine idan naganka sai naji nakasa
yin
maganar.."
Dariya ya sake yi, "nadiya kenan.."
"Meya faru yaya kabeeru?"
Murmushi yayi saboda jin ta kirashi
da kabeeru,
"Kin ganki ko? Bakinki ya iya fadin
kabeeru sake
fada naji"
"Yaya KB.."
Dariya suka yi dukkaninsu
musamman ma shi
kabeer din wanda yake cike da
nishadi cikin
wannan dare,
"Yaushe zaka zo? Zaka zo gobe?"
"Yaushe kike son kara ganina? Duk
lokacin da
kike son sake ganina zanzo.."
"Koda kuwa yanzu ne?" Ta tambayeshi
tana
murmushi,
"Yes even now i shall come if you
wish..."
"To ina jiranka idan har dagaske kake
zaka zo
din"
"Dagaske kike kina son ganina
yanzun..?"
"Kaji yaya kabeer da dawasa nake?
Dagaske
nake mana"
K'arar bude kofa ta jiyo hakan yasata
saurin
dakatar dashi,
"Ina zaka zo da tsohon daren nan?"
"Sabon dare dai ba tsohon
dareba,wurinki zanzo
ki ganni"
"To yi zamanka na hakura da wasa
nake yi.."
"Inama kiyi dagaske kigani idan
zanzo ko bazan
zoba"
"Yaya kabeer kenan ai nasan zaka zo"
Murmushi yayi, "to yaushe zan kawo
miki
budurwata ne ku gaisa?"
Jin abinda yafada yasata mikewa da
sauri bayan
zuciyarta ta harba, nan taji wani shiru
ya ziyarci
cikin kunnenta duhu ya mamaye
ganinta yayinda
bacin rai ya lullube zuciyarta gaba
daya.
*_Ummi Shatu_[7/8, 6:42 AM]
Humaira Khaleel:
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*_4_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Hannu tasa ta danne zuciyarta
gudun kada
ta faso ta fito waje,
"Nadiya... Yanaji kinyi shiru ko bazaki
gaisa da
budurwar tawaba?"
Ajiyar zuciya ta ajiye ahankali, dakyar
ta iya
sassaita tunaninta tayi magana
ahankali,
"Yaya kabeer me zai hana ingaisa da
ita idan
har ka kawo min ita?"
Dan murmushi yayi mai kayatarwa
kamar yana
gabanta tana kallonshi,
"Ina fata dai har zuciyarki kika fada
ma'ana da
zuciya daya.."
"Yaya kabeer kenan.."
"Nadiya kenan, nadiya yanmata"
Murmushin dole tayi kafin tayi
magana,
"Yaya kabeer nafara jin bacci gashi
kaga gobe
zanje school"
"Nadiya nifa da wasa nake yimiki
banida wata
budurwa so karki dauka dagaske ne.."
Duk da cewar taji dadin maganarshi
amma sai
ta basar,
"Kaji yaya kabeer da wani zance, to
idanma
dagaske ne ni ba abin in tayaka
murna bane??
Sanyayyen murmushi ya saki,
"Hakane to balle ma ba dagaske bane
da
wasane"
Itama murmushin jin dadi da farin
ciki tayi,
"Shikenan tunda kaji tsoro ka sauya
magana.."
Yar dariya yayi wadda har tana iya
jiyo sautinta,
"Nayarda naji tsoron..."
Juyi nadiya tayi taja bargo ta dan rufe
rabin
jikinta,
"Yaya kabeer zan barka haka yanzu
saboda
kasan gobe zan je makaranta"
"To ya nadiya babu komai, Allah ya
kaimu goben
sai kin jini" yafada cikeda tsokana,
"Ok tom bye bye" tabashi amsa bayan
ta lumshe
idanuwanta, katse wayar tayi lokacin
da taji
yace "bye bye good night and have a
nice sweet
dream"
Addu'ar kwanciya bacci tayi ta shafe
jikinta, da
tunanin kabeer bacci yayi awon gaba
da ita.
Washe gari da misalin karfe biyu
nadiya ta
dawo daga makaranta dama ba
makarantarsu
daya dasu amir ba su akusa da gida
suke ita
kuma nadiya makarantarsu da dan
tazara da
unguwarsu, a gaggauce ta shiga gida
tana shiga
tasan cewar yaya kabeer yana gidan
saboda taji
kamshin turarensa sannan ta hango
takalmanshi
a kofar falon mama dan haka bata
bari kowa
yaji dawowarta ba ta wuce dakinsu ta
ajiye
school bag dinta ta fito ta shiga
kitchen,
Abinci ta zuba ta zauna tana ci kamar
ance kalli
window tana kallon wurin tayi ido
biyu dashi
tsaye yana kallonta yana yi mata
murmushi,
Sunkuyar da kanta tayi tadaina cin
abincin,
murmushi kabeer yayi ya saki karfen
dake jikin
window din,
"Kici abincinki dama kawai nazo
ganinki ne, bari
natafi inyaso sai nadawo da yamma
lokacin kin
gama laumar.."
Bai jira abinda zatace ba ya juya
yawuce,
murmushi tayi ta tashi ta leka sai da
ta
tabbatar da cewar yatafi baya gidan
sannan ta
koma ta dauki abincinta ta nufi dakin
mama
tana tafe tana cin abincin,
A falo tasamu mama tana shirya
husna da
alama wanka tayi mata,
"A'a kekuma yaushe kika shigo? Jibeki
kina
tafiya kina cin abinci, keda zaki yiwa
wani fada
amma kece meyi"
Zama nadiya tayi saboda mama
kamar yayarta
take sam batayi kamada mahaifiyarta
ba kai
idanma ba sani kayiba zaka zaci ya da
kanwa
ne domin kamar yadda abba yake
jansu ajiki
haka itama maman ke jansu ajikinta
musamman
ma nadiya domin kowanne abune
yake damunta
to ita take fadawa sannan idan
shawarane ma
da ita take yi,
"Hajiya mama kenan wallahi wata
yunwa na
debo kuma ina zuwa sai na iske yaya
kabeer
agidan shine nagudu kitchen na buya
acan
nazuba abincin nafara ci, yanzu kuma
da ya tafi
shine nadawo nan dan kisan
nadawo.."
Tsayawa da shafa man da take yiwa
husna
mama tayi tana kallon nadiya,
"Nadiya wai menene tsakaninki da
kabeer ne?"
Nadiya jin maganar tayi tazo mata a
bazata dan
haka tayi shiru tagagara bawa mama
amsa
wanda har sai da mama ta maimaita
mata
tambayar sannan tayi gaggawar
zakulo amsa ta
bawa Maman,
"Mama babu komai kawai zumunci
muke yi
tunda ni yar uwarsa ce shi dan
uwanane"
"Nasani nadiya, amma bayaga
wannan bana son
wani abu ya hadaku muddin ba
zumunci bane"
"Amma mama saboda..."
Katseta mama tayi bata barta ta
karasa abinda
take son tambaya ba,
"Ya isa haka bana son tambaya, ki
maida
hankalinki kawai kici abincin da yake
gabanki"
Shiru nadiya tayi taja abincin taci
gaba da ci
tana ta sakar zuci saboda bata san
dalilin mama
na rashin son wani abu ya hadata da
yaya
kabeer ba amma
Koma dai menene sannu ahankali zata
tambayi
Maman....
*_Ummi Shatu_*
[7/8, 6:42 AM] Humaira Khaleel: ®
*HASKE
WRITERS ASSO*
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin K'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*5*
aishaummi.blogspot.com
~~~Bata kara bi takan maganar ba
suka cigaba
da hirarsu ita da maman har ta
kammala cin
abincin da takeyi ta tashi tabar falon
ta koma
dakinta tana rikeda wayar mama,
lafewa tayi
akan gadonta suna yin waya da yaya
kabeer,
sun dauki lokaci mai tsawo kafin suyi
sallama
nadiya ta tashi ta shiga wanka ta fito
ta shirya
tasaka uniform din islamiyyarta
domin karfe uku
suke tafiya su dawo karfe shida na
yamma,
Hannen kannenta ta kama suka yiwa
mama
sallama suka tafi, sai da misalin karfe
shida da
yan mintuna suka dawo, dawowarsu
tayi daidai
da zuwan yaya kabeer shi da wani
abokinsa,
Nadiya bata bari sunga fuskarta ba
tafara
gaidasu,
"Baiwar Allah ya kiketa boye kaine
kamar marar
gaskiya,kodai bakida gaskiya?" Abokin
yaya
kabeer din yace da ita,
"Kabarta kawai musty domin yar
kauye ce" yaya
kabeer yafada cikin barkwanci da
tsokana, ita
dai nadiya shiru tayi musu tana jinsu
sai dai ta
lura wannan abokin na yaya kabeer
wanda aka
kira da musty sai faman binta da kallo
yake, duk
inda ta waiga sai taga yanata kare
mata kallo,
Ganin haka yasa ta takura ta shige
gida yayinda
yaya kabeer ya mara mata baya,
A soron gidan suka tsaya kowannensu
fuskarsa
dauke da murmushin kauna,
"Yaya kabeer ina ka samo wannan
abokin mai
shegen kallon tsiya?"
Dariya maganarta ta bashi dan haka
ya fara
darawa yana kallonta,
"Wai musty? Abokinane unguwarmu
daya
sannan tare muka yi karatu dashi"
Dan karamin tsaki taja, "Allah na tsani
mutum
ya tisani agaba yayita kallona"
"To yanzu dai nayi laifi tunda har na
kawo
wanda yayi miki abinda bakya so, ayi
min
afuwa..."
Murmushi tayi, "ni ai ba laifi nace
maka kayi
minba amma dai wannan abokin naka
gaskiya
ya fiya kallo da yawa"
"To ai nabaki hakuri"
"Nahakura"
"To zan iya tafiya?" Yace da ita cikin
tsokana,
"Zaka iya mana yaya kabeer..."
"To fara shiga gida nagani"
Wucewa tayi tana murmushi ta shige
cikin gida
sannan shima kabeer din ya juya
yafita.
Fuskarta dauke da fara'a ta shiga
cikin gidan,
zaune ta tarar da mama da kannenta
tana
yimusu shari'a wanda kusan kullum
aikin kenan
amir da amira kamar zasuga hanjin
cikin
junansu,
"Ke kuma a ina kika tsaya su Amira
suka rigaki
shigowa?" Mama ta tambayeta
idanuwanta
akanta,
"Mama yaya kabeer ne ya tsayar ni
wallahi.."
Shiru Maman tayi ta mayar da
hankalinta gasu
amir taci gaba da yimusu sulhu,
yayinda ita
kuma nadiya ta ajiye jakar
islamiyyarta ta shiga
kitchen domin ta jiyo tuwon da mama
keyi ya
fara kauri alamun ya kama,
Itace ta karasa girkin sannan ta fito
daidai
lokacin abbansu ya dawo nan kuma
dukkaninsu
suka dunguma zuwa falonsa kamar
yadda suka
saba.
Tunda musty abokin kabeer yaga
nadiya yaji
ta kwanta masa arai domin yarinya ce
mai
hankali sannan kuma mai nutsuwa
gata da
kunya da ganin girman nagaba, gani
daya da
yayi mata yasashi kamuwa da sonta
dan haka
batare da ya shawarci abokinsa
kabeer ba ya
samu mahaifinsa yayi masa maganar
nadiya
domin shi dagaske yake sonta bada
wasa ba
sannan son aure yake yimata ba na
yaudara ba
shiyasa ma yake son mahaifinsa yaje
ya
tambayo masa aurenta,
Aranar da ya sanar da mahaifinsa
aranar yaje
ya samu baban nadiya daf da lokacin
sallar
magrib, kasancewar abba mutum ne
mai
karrama bako sai da ya karrama
baban musty
sosai ya fito musu da ruwa sukayi
salla kamar
dama sun san juna sannan baban
musty
yafadawa abba abinda ke tafe dashi,
Shiru abba yayi kafin ya cewa baban
musty zai
tambayi nadiyan ko tasan musty din
inyaso duk
yadda sukayi da ita zai kirashi a waya
ya fada
masa, anan suka yi exchanging din
phone
numbers dinsu abba ya shiga gida,
Lokacin da yashiga falonsa nadiyan ya
samu ita
da mama suna cin tuwo tare, su kuma
yaran an
zuba musu taliya suna ci,
Sai da abba ya bari sun gama cin
abincin
sannan yayi gyaran murya yace,
"Nadiya zo nan"
Kusa dashi ta koma ta zauna, "gani
abba"
"Bakon da nayi dazu saboda ke yazo.."
Ras,ras gaban nadiya ya fadi saboda
bata san
abinda tayiba,
"Abba laifi yace nayi masa?"
Murmushi abba yayi,
"Ba laifi kikayi masa ba nadiya, yazo
nemawa
dansa aurenki ne, sunan yaron wai
Mustapha
abokin kabeeru ne yayanki"
Ba karamin faduwa gaban nadiya ya
sake yiba,
nan fuskar musty ta bayyana acikin
zuciyarta
lokacin da ya kafeta da ido yana yi
mata
wannan kallon kurullar....
*_Ummi Shatu_*
[7/11, 7:58 AM] Ummi A'isha *MIJINA
SIRRINAH...!*🌹
_(Labarin K'auna)_
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*6*
aishaummi.blogspot.com
~~~Shiru nadiya tayi saboda bazata
iya fadawa
abba cewar yaya kabeer take so ba,
"Nadiya ya naji kinyi shiru ne?"
Muryar abba ta dawo da ita cikin
hayyacinta,
"Abba babu komai.."
"To Mustapha dai ya turo mahaifinsa
tunda
babu wata matsala zan sanar dasu
inyaso
yafara zuwa har kusamu ku daidaita"
"To abba" ta fada kanta akasa, ita dai
mama
tana zaune tana jinsu amma har akayi
aka
gama batace ko uffan ba,
Mikewa nadiya tayi ta fita zuwa
dakinta gaba
daya tama rasa abinda yake yimata
dadi acikin
zuciyarta, gashi bata son fadawa yaya
kabeer
domin gudun sakashi cikin
damuwa,please call
me ta tura masa nan take ya kirata,
"Yaya kabeer yau ban ganka ba"
"Nidinma yau ban samu ganin fuskar
gimbiya
nadiya ba amma nasan dalili.."
"Wanne daliline?" Ta tambayeshi cikin
dokin jin
abinda zai fada,
"Yau naje unguwa ne sai dazunnan
nadawo
shiyasa ban shigoba, amma gobe
sammako zan
dako da sassafe inyi karin kumallo da
kyakkyawar fuskarki"
Dariya abinda yafada ya bata dan
haka tafara
dariya,
"Kaji yaya kabeer da abin dariya sai
kace wani
abinci da zakace zakayi karin kumallo
da
fuskata"
"Ni ai kinfi abinci, da ace za a ajiye
min ke inyita
kallonki to da na tabbata bazanji
yunwa ba.."
Wata dariyar ta sake yi har tana
kokarin fadowa
daga kan gadonta,
"Yaya kabeer zaka sa cikina ya fashe
dan dariya
gashi dama naci tuwo na koshi
dayawa.."
"Wai wai, wai, overfeeding kikayi ai?
Oya tashi ki
fara exercise ina jiyoki daga nan"
Tashi tayi tana dan murmushi,
"Allah yaya KB jina nakeyi nagaji
nidai ban son
exercise dinnan.."
"To yi tsalle guda goma ina kirga miki,
oya fara"
Tsalle tafara tanayi yana kirga mata
har sai da
tayi guda ishirin sannan ya barta
takoma saman
gado ta kwanta tana haki,
"Washh, yaya kabeer wlhi kabani
wahala da
yawa"
"Waye yasa kici abinci yayi miki
over?"
"Kaine.."
"A'a ni karki yimin sharri.."
Murmushi tayi kafin tabashi amsa
wayar tayi
shutdown, komawa tayi ta kwanta
tana cikeda
farin ciki.
Kamar yadda kabeer yafada kuwa da
safe sai
gashi yazo lokacin ko school su nadiya
basu
tafiba, asalima lokacin suke shiryawa,
kanta
babu ko dan kwali tana cikin kitchen
tana cin
soyayyen dankalin da mama ke
soyawa sai
gashi ya shigo, ba karamin mamaki
nadiya
tayiba domin ta zaci wasa yake
yimata da yace
zaizo da sassafe ya ganta,
Dan tsananin kunya kasa gaisheshi
tayi tana
jinshi da mama suna gaisawa daga
nan yawuce
ciki falon abba,
Bata bari yaji fitarta zuwa makaranta
ba ta zare
jiki tagudu.
Abangaren Mustapha kuwa ba
karamin dadin
labarin da mahaifinsa yazo mishi
dashi yajiba
musamman ma da yaji cewar ba
ayiwa nadiya
mijiba asalima ko tsayawa da samari
bata fara
yiba,wanka ya dauka ya shirya ya fito
ya nufi
gidansu nadiyan,
Tana falon abba tana yiwa su amir
homework
yaro yayi sallama yace wai nadiya taje
inji
Mustapha, kamar bazata yi motsiba
har saida
taji mama tayi magana sannan ta
tashi tafita
zuciyarta babu dadi,
Tsaye ta sameshi ya saka
hannuwanshi acikin
aljihu yana yimata murmushi sai dai
ita ko
kadan bai burgeta ba, sallama tayi
masa ya
amsa cikeda kulawa nan suka gaisa
yafara koro
mata jawabi,
"Nadiya wato tun ranar farko dana
soma ganinki
Allah ya jarrabi zuciyata da sonki da
kaunarki
saboda yabawa da nayi da hankalinki
da
nutsuwarki,ina fata zaki bani hadin
kai har nakai
ga cimma burina da muradina na
mallakarki..."
Saida taji yayi shiru sannan tayi
magana,
"Yaya Mustapha nagode da soyayyar
ka
agareni,hakika duk Wanda yace yana
sonka to
ya gama yimaka komai kuma bakada
kamarshi,to amma nikuma inada
wanda nakeso"
Cikeda mamaki ya kalleta saboda
shidai
mahaifinsa yace mahaifinta ya sanar
dashi babu
wanda yake zuwa wurinta,
"Kina da wanda kikeso? Waye?"
"Yaya kabeer ne abokinka"
Jin abinda tace yasashi yin shiru
nawasu yan
lokuta kafin daga bisani ya kalleta,
"Shikenan nadiya nagode da kika fada
min
gaskiya baki rufeni ba, kuma nayi
farin ciki da
jin cewa kabeer ne wanda kike so
domin
mutumne shi mai kyakkyawan hali da
dabi'a mai
kyau, Allah ya tabbatar da alkhairi"
Sallama yayi mata ya tafi nan itama ta
juya ta
shiga cikin gida tana dauke da farin
cikin cewar
tagama da babin Mustapha..
*_Ummi Shatu_*
[7/13, 7:02 AM] Ummi A'isha *MIJINA
SIRRINA..!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*7*
aishaummi.blogspot.com
~~~Hankali kwance nadiya ta koma
gida taci
gaba da gudanar da harkokinta,
soyayyarsu
itada yaya kabeer kuwa kullum sake
yin gaba
take tana kara kulluwa, koda yaushe
suna
makale awaya suna hira, sannan
kusan koda
wanne lokaci yana gidan mutukar
nadiyan tana
nan.
Tunda nadiya ta sanarwa da mustapha
cewar
tanada wanda take so yaji hankalinsa
ya dan
tashi amma idan yatuno da cewar
kabeer ne
wanda take so din sai yaji ranshi ya
danyi fari
saboda yasan kabeer zai riketa riko na
gaskiya
wannan dalilin ne ma yasashi
sanarwa da
mahaifinsa yanda suka yi da ita,
shima mahaifin
nasa baiyi k'asa a gwiwa ba ya kira
abban
nadiya ya fada masa abinda yafaru
gudun kar
aga musty din yadaina zuwa bayan
kuma manya
sun shiga, shiru abban nadiya yayi
saboda
shidai a iya saninshi nadiya bata da
wani
saurayi amma tunda yaji haka to ya
zama dole
ya tuntubeta da zarar ya koma gida.
Kamar yadda al'adar gidan take
yauma zaune
suke dukkaninsu a falon abba suna
kallon tashar
mbc drama, rage karar volume din tv
din Abba
yayi yace,
"Yawwa nadiya kafin na manta zo ina
son
magana dake.."
Kusa da mama ta dan matsa tana
kallon abba,
"Nadiya yaron nan mustapha da yazo
wurinki
yace kince masa kinada wanda kikeso
hakane..?"
Kai ta dagawa abba, "hakane Abba"
"To waye?" Abba yasake tambayarta,
kamar
bazata yi magana ba dan kunya ta
daure tace,
"Abba yaya kabeer ne"
Shiru abban ya danyi fuskarsa dauke
da
murmushi,
"To kira min kabeer din, dama yau ai
naga baizo
gidanba"
Tashi tayi ta fita tana cikeda murna,
wayar
mama ta dauka ta kirashi,
"Yan mata.."
"Yaya kabeer albishirinka?"
"Goro" yafada yana murmushi,
"To kazo abba yana kiranka"
"To ai baki fada min albishir din da
kika yimin
ba"
"Idan kazo zakaji"
"To gani nan zuwa"
Katse wayar tayi ta koma falon abba
tana jin
kamar ta daka tsalle dan tsananin
murna,
Tana shiga falon abba ta dan saci
kallon mama
nan taga fuskar Maman babu walwala
sosai
amma dai batayi magana ba,
Nan kuma taji ranta ya dan sosu
saboda tasan
bacin ran mama yanada alaka da
maganarsu
itada kabeer tunda tun jimawa Maman
ke
yimata gargadin cewar karta bari
soyayya ta
shiga tsakaninta da kabeer,
Tana ta tunanin abinda zaije yazo
aranta taji
sallamar yaya kabeer nan tayi
hanzarin jan
hijabinta ta rufe fuskarta saboda
kunya sai dai
amma tun kafin ya karaso kamshin
turarensa ya
rigashi karasowa,
Cikin nutsuwa yayi sallama ya shiga
bayan abba
ya amsa masa, nan kuma su amir
sukayi kansa
suka cuccukumeshi domin yasaba basu
sweet
duk lokacin da yazo,
Yau dinma saida yabisu ya basu daya
bayan
daya sannan suka kyaleshi ya nemi
wuri ya
zauna, cikeda girmamawa ya gaisheda
abba da
mama,
"Kabeeru dalilin da yasa kaji nace
kazo shine
nadiya ce tazo min da wani zance
cewar kai da
ita kuna son junanku hakane?"
Sunkuyar da kai kabeer yayi cikeda
kunya yace
"hakane abba"
Dan fara'a abba ya fadada cikeda jin
dadi yace,
"To kabeeru babu shakka naji dadin
wannan
labari domin hakan zai kara dankon
zumunci da
aminci a tsakaninmu domin nadiya
yar
uwarkace, sannan ni mahaifinka ne
ako ina zan
iya tsayawa in nema maka aure bare
agidana,dan haka ni a matsayina na
mahaifin
nadiya nabaka ita a matsayin matar
aure ko
bana raye ban yadda nadiya ta auri
kowanne
namiji ba face kai har sai dai idan
kaine ka
sauya akalarka, dan haka abinda nake
so dakai
shine da zarar ka koma gida ka
sanarda yaya
cewa ga abinda mukayi dakai saboda
sonake yi
nadiya na gama makaranta ayi
bikinku da ita
batare da andauki dogon lokaci ba"
Ai kabeer najin abinda Abba yace yaji
kamar an
yimishi bushara da gidan aljanna, nan
wani dadi
ya rufeshi zuciyarsa ta samu wata
nutsuwa mai
kayatarwa tuni yafara yiwa abba
godiya,
"Abba nagode madalla, Allah yasaka
da alkhairi,
Allah yabar zumunci abba.."
"Babu komai kabeer ai duk abinda
nayi maka
kaina nayiwa domin kai d'anane
halak malak"
Saida kabeer ya sake jaddada wata
godiyar
sannan ya tashi ya fita, cikeda jin
kunya nadiya
tabi bayanshi, tana zuwa tsakar gida
kuwa ta
iskeshi lafe ajikin bango dama ita yake
jira ya
harde hannuwansa ajikin kirjinshi,
Kallonshi tayi yasha gaye cikin wata
rantsattsiyar purple colour din shadda
galila
wacce tasha dinkin buba dan haka ba
karamin
kyau yayiba,
"Yanzu kaji albishir din da nayi maka
dazu?"
Tafada cikeda murmushin kunya,
"Naji wannan dalilinne ma yasani
shirya baki
tukwici, rufe idonki"
Rufe idonta tayi tana murmushi, "yaya
kabeer
Allah dai yasa nima chocolate din zaka
bani irin
wacce kabawa su amir..."
Bata iya karasawa ba saboda jin
lebenshi akan
nata, take jikinta yafara rawa tayi
gaggawar
bude idonta, nan ta juya zata gudu
yayi saurin
rikota,
"Ai abba yace yabani ke ko baya raye
nine
mijinki, tsananin farin cikine yasa
kikaga nayi
miki haka so karki fassara ni da wata
manufa,
ko ba komai dai kin san ni yayanki ne
dan haka
bazan taba cutar dakeba"
Har lokacin bata iya yin magana ba
saboda
tsantsar kunyar da ya haddasa mata,
"Yaya kabeer nidai.."
Hannunta ya rike ya matsa kusa da ita
tareda
leka fuskarta wadda ta kawar gefe
guda,
"Kedai me?"
"Nidai kasani jin kunya"
Murmushi yayi ya mike tsaye yana
kallonta
zuciyarsa cikeda farin ciki...
*_Ummi Shatu_*
[7/13, 6:59 AM] Ummi A'isha: ®
_HASKE
WRITERS ASSO._
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
*8*
aishaummi.blogspot.com
~~~ "Wai kina nufin haka zamuje
gidan kina
yimin wannan kunyar?"
Murmushi ta danyi "wai yaya kabeer
ni duk ba
wannan ba yaushe zaka zo muyi hira
irin wacce
muka dade ba muyiba?"
Daga kai yayi yana kallon sararin
samaniya
alamun tunani fuskarsa kuma kunshe
da
murmushi,
"Uhmmm, ina jin zanzo a weekend
saboda ranar
ne banida aiki da yawa sannan kema
kina
gida.."
"To Allah ya kaimu, yanzu dai bari
nakoma ciki
saboda kai naga kana cikin farin
ciki.."
Dakatar da ita yayi ya hanata tafiya,
"Ina kuma zakije bayan akwai labarai
da yawa
da nake burin ji daga gareki"
"Labari kuma yaya kabeer? A wannan
daren?"
"To da sai awanne daren?" Ya
tambayeta yana
murmushi,
"A'a yaya kabeer karfa ka sauya min
maganata
zuwa wata daban"
Murmushinsa ne yasake karuwa, "kaji
min
yarinya da wayo, wai ke waye ya koya
miki
wayone? Ni ban taba ganin first born
mai wayo
irin nakiba"
Dariya tayi ta rufe fuskarta, "har
nakaika wayo?
Kaima fa first born dinne amma
kafini wayo ma"
"A'a ban fiki wayoba zadai muzo
daya,
musamman ma tunda zuciyoyinmu
sun kasance
guda daya, sannan nan bada dadewa
ba zamu
zama abu daya..."
Dariyace ta kwace mata nan tayi baya
da sauri
tana dariya,
"Nidai yaya kabeer natafi da wannan
sai
anjima.."
Shima dariyar yayi ya daga hannu
alamun bye
bye yana cewa,
"Ok bye yanmatan yaya kabeer"
Har taje daf da dakin mama dariyar
take, a kofar
daki taga mama tsaye fuskarta babu
walwala
sannan da alama ita take jira,
"Mama..."
"Zo nadiya" Maman ta fada idonta har
ya danyi
ja saboda bacin rai, jiki asanyaye
nadiya tabi
bayanta zuwa cikin bedroom dinta
domin basu
tsaya a falo ba,
Zama mama tayi agefen gado itama
nadiyan ta
zauna,
Kamo hannuwan nadiya mama tayi
tana
kallonta,
"Nadiya nasan ke yarinyace karama
wacce bata
gama sanin rayuwa ba, wadda hankali
bai gama
ratsata ba, wacce bata san rayuwar
aure ba,
wacce bata san irin gwagwarmayar da
kowacce
mace keyi agidan aurenta ba, bawai
ina son
rabaki da kabeer bane nadiya a'a sai
dai ina son
kisani shi auren zumunci yafi komai
gyara
zumunci idan har yayi dadi amma
yafi komai
b'ata zumunci mutukar baiyi dadiba
shiyasa
zakiga tun farko ban so soyayyarku da
kabeer
ba saboda kabeer dan dakinane akwai
zumunci
mai karfi tsakanina dashi haka
iyayensa, bana
son azo ayi abu ba aji dadinsa ba
zumunci ya
baci.."
Gaba daya jikin nadiya yagama yin
sanyi saboda
jin abubuwan da mama ta fada dan
haka take
taji jikinta ya fara yar rawa,
"Mama kiyi mana addu'a kawai akan
Allah
yasanya albarka acikin al'amarin
amma ni sam
bazan iya rabuwa da ya kabeer ba
saboda
nafara sonsa tun ban san wacece
niba.."
Shiru mama tayi tana kallonta batare
da tace
komaiba, ita akwai abinda ta dade
tana
hangowa wanda ita nadiya ko kadan
bazata iya
hangoshi ba domin akwai kuruciya
atattare da
ita sosai saboda gaba daya yanzu
bazata wuce
shekaru 15 ba aduniya dan haka
yanzune tafara
saninma menene rayuwar,
"Shikenan nadiya tunda kin kasa
fahimtata
shikenan bazan hanaki abinda kikeso
ba Allah ya
sanya alkhairi da albarka acikin
tarayyarki da
kabeer"
Idanuwan nadiyane suka ciko da
kwalla nan tayi
saurin tashi ta fita saboda sai take jin
kamar
yanzu ne zata tafi tabar mamanta da
yan
uwanta,
Duk da cewar mama sunyi haka da
nadiya bata
iya hakura ba tashi tayi taje ta iske
abba a
falonsa yana zaune shida su amir da
waleeda
nan ta tashesu tace sutafi dakinsu suje
su
kwanta,bayan fitarsu ta samu wuri ta
zauna
kusa da abba,
"Abban nadiya wata magana nake son
muyi
dakai amma ta fahimta, dafarko ina
son ka
fahimceni ka gane cewar ni bawai
bana son
kabeer ne ko kuma yana da wani
mummunan
tabo awurina ba, kawai nidai bana
son maganar
aurensa da nadiya ne saboda auren
zuminci
bashida alfanu mutukar ba ayi daceba
amma
idan har aka dace yayi dadi to
zumunci yana
sake kulluwa,
Ban so lokaci daya farat daya ka
amince ka
bawa kabeer nadiya ba saboda
gaskiya nidai
auren zumunci baya daya daga cikin
abinda
nake son yiwa 'yayana.."
Abba bai tanka ba har saida yaji tayi
shiru
alamun ta gama sannan yafara
magana da
tausasashiyar murya,
"Haba hajiya bilkisu, ai kabeeru dan
dakinki ne,
kin sanshi kin san halinsa sannan kin
san ko
wanene shi tun yana yaro dan haka
bakida
kokwanta acikin halayyarsa, kuma
insha Allah
wannan auren akwai alkhairi acikinsa
ba
kadanba da yardar Allah sai kowa
yayi alfahari
dashi kedai kawai kiyi musu addu'a
kuma ni ina
ganin da ace mu dauki nadiya mu
baiwa wani
wanda bamu saniba, bamu san
asalinsa ba
bamu san halinsa ba bamu san ko
waye shiba
gara mu baiwa na gida wanda muka
san
tushensa muka san komai nasa.."
Jijjiga kai mama tayi alamar gamsuwa
da
bayanin da yayi mata sai yanzu ta
danji ta
samu nutsuwa akan zancen,
"Shikenan to Allah ya tabbatar da
alkhairi"
"Yawwa hajiya bilkisu addu'ar da
zamuyi kenan,
kinga yanzu tana aji biyar next term
zata shiga
aji 6 nan da wata shekarar insha Allah
zamu yi
bikinta mu kaita gidan mijinta, amma
kafin nan
ina so nayi miki albishir da cewar
keda ita yar
taki na biya muku saudiyya zakuje ku
sauke
farali sannan ku iyo addu'a akan
Allah ya basu
zama lafiya da zuri'a dayyaba"
Murna ce ta kama mama saboda jin
albishir din
da abba yayi mata nan ta hau fara'a
tana mai
yimasa addu'ar Allah ya kara masa
budi acikin
harkokinsa...
*_Ummi Shatu_*
[7/14, 9:20 PM] Ummi A'isha🏻:
*MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
_Anty maijidda musa (maman twins)
shafi na
9 zuwa shafi na 13 nakine ke kadai
domin jin
dadinki, ina mutukar ji dake anty
Jidda..._
*9*
aishaummi.blogspot.com
~~~Nadiya na shiga d'aki ta kifa kanta
jikin
gado tafara rera kuka ahankali wanda
ita kanta
bata san dalili ba amma dai tafi zargin
cewa na
fargabar rabuwa dasu mama ne,
shigowar su
Amira da taji ne yasata yin shiru ta
tashi ta
shiga toilet, sai da ta gyara fuskarta
sannan ta
fito lokacin harsu waleeda sun
kwanta,
Itama kwanciyar tayi ta dauki wayar
mama dake
wurinta tafara yin game, kiran yaya
kabeer ne
ya shigo nan ta d'aga jikinta a
sanyaye,
"Yaya KB ya kaje gida?"
"Ni ai nayi fushi dake, wato ko ki
kirani kiji yaya
naje gida ko?"
"Ayya haba yaya KB ai kasan dai
inada niyyar
kiranka kawai dai Allah ne baiyi ba"
Jin yanda ta marerece murya ya sashi
yin yar
dariya mai dan sauti,
"Dadina dake ba a kada ke a magana
mutukar a
wayane amma idan a filine kuma
kinfi kowa
shiru"
"Ai kai dinne yaya kabeer kwarjini
gareka,
kwarjini kake yimin"
"Wanne irin kwarjini kuma?" Ya
tambayeta
ranshi cikeda farin ciki,
"Yaya kabeer in tambayeka mana"
"Allah yasa nasani yanmatan yaya
kabeer"
Murmushi tayi ta sake makale wayar a
kunnenta,
"Yaya kabeer kuma idan muka yi aure
shikenan
bazaka rinka kawoni gidan mama
kullum ba ko?"
Dariya ya fara yi mata saboda jin
yarinta afili,
"Haba nadiya kuma idan kikace
kullum zan rinka
kawoki ai sai su maman ma su gaji
dake"
"To yaya kabeer kazo mu zauna
agidan su
Maman mana gaba daya basai munje
gidanmu
ba"
"Nadiya kenan, ke karamar yarinyace
baki san
menene aure ba, ko kin sani?"
"Nasani mana yaya kabeer"
"To fada min menene aure"
Shiru ta danyi tafara tunani kafin tayi
magana,
"Yaya kabeer aure shine idan saurayi
yaga
budurwa yake sonta itama take sonshi
sai ayi
musu aure.."
"Daga nanfa?" Ya sake tambayarta,
"Sai akaita gidan da ya gina mata,
iyayenta su
siya mata kayan daki"
"Uhum daga nan kuma fa?"
Dan shiru ta sakeyi sannan taci gaba,
"Sai ya siyo kayan abinci ta rinka yi
masa girki
tana share gida tana yin wanke
wanke"
"Shikenan?"
"Ehh" tabashi amsa tana murmushi,
shima
murmushin yayi,
"Shikenan kin gama?"
"Nagama mana"
Dariya yafara yi yana dad'awa har na
tsawon
wani lokaci domin sai yau yagama
tabbatarwa
da nadiya karamar yarinya ce wadda
kuruciya ke
dawainiya da ita,
"Ba ayi muku biology ne nadiya?"
"Ana koya mana.."
Shiru yayi saboda baya son yasata taji
kunya
shiyasa bai son fada mata kai tsaye,
"To tunda baki san menene aureba
nabaki
assignment ki zauna ki nutsu ki gano
min
menene aure"
"To yaya kabeer zan yi"
Murmushi ya dan yimata sannan yayi
mata
sallama,ajiye wayar tayi tanata
tunanin
maganganun da sukayi da yaya kabeer
yanzu,
To ita yanzu tayaya zata samo
wannan
assignment din da yaya kabeer yace
ya bata?
Ta raya hakan acikin ranta, gyara
kwanciyarta
tayi taci gaba da tunani can sai ta
tuno cewar
yan ajinsu dayawa tana ganinsu suna
karanta
littattafan hausa sannan kuma tana
yawan jinsu
suna labarin aure ko labarin soyayya
amma ita
bata taba tsoma bakinta aciki ba
amma itama
daga gobe zata fara aro littattafai tana
karantawa domin ganin abinda ke
tattare aciki,
Sati biyu da kiran da abba yayiwa
kabeer
mahaifin kabeer suka zo domin su
tattauna da
abban nadiya.
***
Alhaji Bashar Usman da Alhaji Mu'az
usman yan
uwan junane ciki daya uwa daya uba
daya suna
da kanne mata guda uku wadanda
yanzu haka
kowaccensu tana can agidan mijinta
tareda
yaranta, Alh Bashar shine babba sai
mai bi
masa alh mu'az daga nan sai Hajiya
Kubra sai
haj sa'ade sai yar autarsu hajiya
Maimuna,
Asalinsu yan jahar kano ne cikin wata
karamar
hukuma wacce ake kira da Rano, anan
suka
taso dukkaninsu sannan har yanzu
anan
kowannensu yake zaune tareda
iyalinsa hajiya
kubra ce kadai ke zaune a karamar
hukumar
sumaila, shi abbansu kabeer yana
zaune a
tsohuwar G. R. A, shi kuma abbansu
nadiya
yana zaune a unguwar Rano Quarters,
Alh bashar yana da 'yaya guda hudu
biyu maza
biyu mata, kabeer shine babba sai Fati
wacce ke
binsa daga nan sai Muhammad sai
autarsu
A'isha,
Tun lokacin da aka haifi nadiya yan
uwa da
dangi keta tsokanar kabeer suna cewa
an haifa
masa mata, haka itama nadiyan koda
yaushe
dangi da yan uwa cikin tsokanarta
suke suna
kiranta da matar kabeer, tun kabeer
bai dauki
abun da gaskeba har yazo ya fara
yarda da
abinda 'yan uwa ke fadi tsakaninsa da
nadiya,
Ita kuwa nadiya lokacin ma bawani
kwakkwaran
sani ta yiwa yaya kabeer dinba amma
kowa
yazo gidan sai taji yana cewa "matar
kabeeru"
duk sanda aka tsokaneta da wannan
sunan kuka
take yi domin bata sanshi ba.....
*_Ummi Shatu_*🏻
[7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻:
*MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad