Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Sunday, June 24, 2018

Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

Wannan lamarin ya faru ne a kauyen
Mudzami da ke Huchu a Gokwe ta kasar Zimbabwe, hakan yasa Sarkin
Nemangwe wanda kauyen ke karkashin
mulkinsa ya bayar da umurnin gudanar
da bincike kamar yadda Bulawayo24 ta
ruwaito.

Rahotanni sunce matar mahaifin
Bubbingeon Museika Ndaba, Naume
Langson ne ta yi masa dabara har ya
fara kwanciya da ita saboda a cewarta
mahaifinsa mai shekaru 67 baya iya
gamsar da ita.

Asirinsu ya tonu ne bayan wani dan
uwansu mai suna Bongani Ncube ta
gama su turmi da tabarya a kusa da
rafi.

An kuma ce kafin a gano abinda suke
aikatawa, an sha ganinsu suna zuwa
dajin tare kuma ana kyautata zaton tun
a lokacin suke aikata barnar tasu.
Bayan Ncube ta kama su, ya garzaya
gidan inda ta sanar da mahaifin
Museika Ndaba mai suna Isaac wanda
shi kuma ya kai maganar wajen mai
unguwa.

Museika Ndaba ya ce ya fara tarawa da
matar mahaifinsa ne wata rana da ta
shigo dakinsa ta iske shi zigidir yana
barci saboda zafi, daga nan ne wai ta
janyo hankalinsa har ta kai ga sun
kwanta tare.
Ya ce ya yi kokarin ture ta daga jikinsa
lokacin da ya farka daga barci amma
hakan bai yiwu ba.

"Abinda na yi ba kuskure bane laifin da
nayi kawai shine nayi da dan miji na
saboda a gaskiya mijina baya gamsar da
ni. Matsuwa ce ta janyo na aikata hakan
da dansa kuma na roki mijina gafara
kuma ya yafe min, " inji Langson.
Cif Nemange wanda aka kaiwa kara ya
ce wannan abin kunya ce matuka
hakan yasa ya yanke hukuncin cinsu
tara da shanu daya ko wannensu. Ya
kuma kara da cewa Museika Ndaba ya
kara wa mahaifinsa wani shanun
saboda irin cin amanar da ya yi masa.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad