ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Friday, June 15, 2018

ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE

Idan aka ce smartphone ana magana ne da
wayar da ta cika gari a wannan lokacin wacce
zai yi wahala ka samu mutum biyu wadanda
suke rike da waya amma kuma ba a samu mai
ita ba. Irin wadannan wayoyi sun cika ko’ina, ga
shi kuma kamfanonin da suke yin su kullum kara
fito da sababbi suke yi kasuwa.
Kodayake a irin tunani namu na bakaken fata
kasancewar waya na da tsada shi ne ke nuna
cewar wannan wayar tana da kyau, wani lokaci
kuma neman iyawa da bajinta da nuna isa shi
ke sa mu mallaki waya wacce take da tsada ba
yin la’akari da me ke cikin wannan wayar ba ko
kuma me wannan wayar zata iya yi mana.
Wani abu kuma da yake daurewa masu son su
siya sabuwar waya shine, idan na samu kudi
wace irin waya ya kamata in siya, ko kuma
mene ne abin yin la’akari da shi idan ina son
canza waya ko kuma sake sabuwa. Amsoshin
wannan tambayar ya danganta da me kake son
yi da wayar, domin wani yana yin la’kari da
karfin wayar wurin rike wuta ko caji, wani kuma
yana yin la’akari da kyau na hoto da take dauka,
wani kuma yana yin la’akari da karfin network da
take da shi, wani kuma yana yin la’akari da
girman fuskarta, da dai makamantan wadannan.

1. ==> GIRMAN FUSKAR WAYAR

A wurin siyan waya ko tablet mutane suna yin
la’akari da girman fuskar wayar wato (screen).
Wani yafi so ya ga waya faskekiya a wurin sa,
wani kuma baya son ganin haka. To shi dai
maganar fuskar waya ra’ayi ne, kuma wanda
yayi maka ba dole ba ne yayi wa wani. Amma
dai a zahiri idan kasan kai mutum ne mai son
wayarka ta rika zama da caji to girman fuskar
waya da barin ta cikin haske sosai na
taimakawa wurin cinye caji.

2. ==> KAURI DA NAUYI

Kauri da nauyin waya abu ne mai muhimmanci a
lokacin da mutum zai sayi waya ko tablet. Kauri
dai an fi lura da shi akan komai, wani lokaci
sirantaka a wurin kayan computer bai cika bayar
kaya masu inganci ba a wani lokaci. Saboda
haka ya danganta gare ka idan kana son kyau
fiye da inganci sai ka tsallaka siriyar waya ko
tablet. Kodayake wadansu wayoyin suna da jikin
karfe ne saboda haka tun kafin kabar wurin siya
ka tabbatar ka duba don kada karfen ne ya sata
tayi nauyi.

3. ==> MANHAJOJIN (Operating System) DA
WAYA TAKE AMFANI DA SU

Babbar Manhajar da take sarrafa komai da ke
jikin waya shi ake kira da Operating System, shi
yake lura da hatta maballan da kake tabawa
wurin kunnawa da kashewa, shi yake lura da
sauti da kalan da yake fita a wayar. To lallai
wurin siyan waya yana da kyau ka duba da kyau
domin ka san wane irin manhaja ce a cikin
wannan wayar. Kamar yadda da yawa daga cikin
mu suka sani cewar wayoyin da muke rikewa
suna da banbanci wurin gininsu da kuma wane
ne yayi su? Kunga dai wayoyi idan ya zo ga
maganar Operating System akwai na Android,
sannan ga iOS, sai Microsoft Phone 7, sai
Blackberry ga kuma web OS da Symbian, dukkan
wadannan da na lissafo da yawa daga cikin mu
sun dauka cewar waya ce. A a kamfani da yake
yin karfe da kyan da suke jikin waya daban
sannan manhajar da ake saka mata da ba.
Wadancan sunaye da aka ji na lissafo mutane
sun fi sabawa da su a matsayin waya maimakon
Babbar Manhaja ce.

4. ==> WURIN ADANA BAYANAI

Mafi yawan kanfanonin da suke yin wayoyi da
tablet a wannan lokaci suna kokarin ganin sun yi
mata mazubi da ya kai girman gig 16GB, wanda
zai baka dama domin a jiyar hotuna da rubutu
da sauti da hotuna masu motsi. Kodayake
wadansu saboda yanayin yadda suke tara
abubuwa a cikin wayoyinsu suna bukatar karin
abubuwa a ciki. To a nan yana da kyau ka sani
wayoyin da kamfani Apple suke yi su basa bada
ramin kara ma’ajiya wato Memory, saboda haka
idan kasan kai mai sun ajiyar abubuwa ne sai ka
nemi koda wayar Apple amma mai mafi girman
mazubi.

5. ==> KARFIN SHIGA INTERNET

Kusan dukkan wayoyin tafi da kidan ka suna
zuwa da tsarin sadarwa maras waya (wireless)
wanda ya ke basu damar iya kulla alaka
tsakaninsu da ko kamfanin layukansu ko kuma
hanyoyin shiga intanet da yake gida ko kuma
ofis da dai makamantansu. Irin wadannan
hanyar da ake amfani da ita domin samun
sinadarin shiga intanet ba tare da amfani da
layin waya ba shine ta hanyar amfani da Wai-Fai
(Wireless Fidility). Amma yana da kyau wanda
zai sayi waya a wannan lokaci ya san cewar
yanzu ma muna karni na uku bane 3G (Third
Generation) ta wurin shiga intanet, a’a a wannan
kasa yanzu haka akwai kamfanoni da suka
tsallaka karni na hudu 4G.
Wayoyin da aka yi a baya sun fara ne da 1G sai
kuma suka shiga 2G wanda irin wadannan
wayoyin ba sa ba msutum damar shiga intanet
da sauri, koda kuwa a inda mutum ya ke akwai
network mai kyau da karfi. Daga baya suka
shigo da 3G wanda yake bamu damar har kallon
hotuna masu motsi (video) muke yi ba tare da
yana tsayawa ba. Saboda haka yanzu mafi
yawan wayoyin da ake yi suna baka damar
amfani da karfin network na 3G da 4G, sai a
kiyaye idan an je siya.

6. ==> KANA NAN MANHAJOJI

Daya daga cikin abin da mutane da dama suke
yin la’akari da shi shine idan na sayi waya iri
kaza shin dawe application ne zan iya aiki,
kusan a wannan lokaci da muke ciki kasancewar
wayoyin Android sun fi yawa da kuma saukin
koyan yadda ake kirkiran manhajojinsu, yasa
mutane da dama suke son siyar wayar Android.
Amma kuma idan aka zo ga zafafan Manhajoji
to sai muce manhajojin da ake amfani da su a
waya kirar Apple sun fi shahara da kwarjini.
Misalia shagon Apple akwai manhajoji dubu dari
uku na kyauta da kuma na siyarwa, a kuma
shagon Android akwai manhajoji dubu dari biyu
da hamsin na kyauta da kuma siyarwa. Suma
sauran manhajoji irin su Blackberry da
makamantansu suma suna da shagunan da ake
samun manhajojinsu saidai ba su kai na Apple
da Android yawa ba.

7. ==> Kamara da Nado Sauti'

Hakika wadannan abubuwa guda biyu sun
karawa wayoyin tafi da gidanka daraja, kusan a
yanzu mutane da dama suna yin amfani da
kamarar jikin wayoyinsu domin daukar
shagulgulan biki da suna da taron siyasa, wa’azi,
wasan kwaikwayo da dai makamantansu.
Wannan dalilin ne ya sanya wayoyi a wannan
lokacin suke kara yin tsada, duk da cewar
mutane da dama basu cika kiyaye haka ba.
Kusan a yanzu akwai wayoyin da ake da su
wadanda saboda karfi da kyau yanayin hotuna
da suke dauka hatta mawaka suna amfani da su
wurin shirya wakokinsu. Haka yan jarida a
wannan lokaci suna yin amfani da wayoyi wurin
nado sauti da zasu iya kai rahoto da shi. Duk da
cewar karfin wata wayar ya fi na wata, amma
waya da kamara da kayan daukan sautin da ke
jikinta ya mayar da mutane ‘yan jaridan tafi da
gidanka amma wasu ba su sani ba. To ba
kowace waya bace ta ciki inganci a kan haka.
Sannan idan ka san kai baka damu da kyau na
hoto ba to ba sai ka sayi waya mai tsada ba.
8. ==> DADEWAR BATIRI
Lallai ko ba a fada maka ba kasan cewar batir
yana da matukar muhimmamci a jikin waya
domin duk irin aikin da waya zata yi maka idan
har batirin wayar baya dadewa abin ya zamo da
shirme ke nan. Shi yasa kuwan mafi yawan
kamfanonin da suke kirkirar waya suka fi mayar
da hankali wurin ganin batar na dadewa, duk da
irin kurakurai da ake samu wadansu kamfanonin
suna yi sai ka samu kamfani yayi waya kuma
cikawa batirin sinadari da idan ya ji rana zai
kama da wuta, amma dai suna kokari.
Zaka samu wayoyi a wannan lokaci ana inganta
batirinsu har kaga waya tana iya kwana uku
tana aiki, kodayake ba kowa yasan wayoyin
wannan lokacin suna haka ba, kasancewar idan
muka sayi waya bama karanta takardar da take
zuwa da ita.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad