Bidiyon ya nuna mata, kusan dukkaninsu
fuskar su rufe da niqab, suna rawa ga
wakar da wani mawaki ke rerawa a wani
gurin shakatawa a arewacin birnin Arar
- Ma'abota amfani da tweeter na kasar sun
bayyana damuwar su na rawan da mata
sukeyi wanda zai yuwu maza na kallon su
Juyin Zamani: Rawar mata a kasar Saudiyya a
kulob ta fara tayar wa da kasar hankali
Video din mata suna rawa a wani gidan
rawa Saudi Arabia ya fusata filayen
sada zumunta na, wadanda suke
ikirarin hakan ya sabawa tarbiyar
daular musuluncin.
Bidiyon ya nuna mata, kusan
dukkaninsu fuskar su rufe da niqab,
suna rawa ga wakar da wani mawaki ke
rerawa a wani gurin shakatawa a
arewacin birnin Arar.
Ma'abota amfani da tweeter na kasar
sun bayyana damuwar su na rawan da
mata sukeyi wanda zai yuwu maza na
kallon su.
"Idan mata suka zama fitsararru, toh
tabbas kasar nan na cikin masifa, " inji
ma'abota tweeter.
Wasu kuma suka ce "Wannan abin
bakin ciki ne, yakamata a tuhumi gurin
shakatawar"
Gurin shakatawar yayi gobara
sakamakon zargin da ake musu da hada
mata da maza, wanda ya haramta a
Saudi Arabia.
A bidiyon, an nuna katanga tsakanin
matan da mazan, amma katangar bata
rufe tsakanin su ba har zuwa kan
mumbarin.
A gaba an nuna mata da maza na rawa
suna fuskantar juna.
Bayan yaduwar bidiyon, Daraktan
gurin shakatawar yace sunyi kokarin
hana matan yin rawa ta hanyar basu
umarnin komawa mazaunin su, tare da
dakatar da mawakin.
Ya kuma ce katangar ta raba matan da
mazan, an dai dau bidiyon ne ta inda
ake hange kamar katangar bata kai
gurin mumbarin ba.
A watan fabrairu na shekarar nan ne,
aka kama wasu ma'aurata sakamakon
rawa da aka gansu suna yi akan titi.
A shekarar da ta gabata ne, yan sandan
suka kama yaro Dan shekaru 14, saboda
yana rawa akan Macarena a birnin
Jeddah. Sun kira hakan da rashin
tarbiya.
Source :- Hausa.naij.ng
No comments:
Post a Comment