SHIN MUNSAN MECECE SOYAYYA ? - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Monday, June 4, 2018

SHIN MUNSAN MECECE SOYAYYA ?

Assalamu Alaikum ya ’yan uwa ma’abota
soyayya. Dukkan wani manazarci a kan wani
abu zai so a ce ana aikata wannan abin da
yake nazarta yadda ya dace.

Na sani ku ma
kun sani, a yanzu mafi akasarinmu muna
ambatar soyayya a bakunanmu ne kawai, ba
tare da mun san ita kanta soyayyar ba
ballantana kuma ire-irenta.

Alhamdu lillahi, kwanakin baya na ga ’yan uwa
sun kokarta wajen ba da ma’anar kalmar
soyayya, ya dace a ce mu san ire-iren
soyayya domin tantance a wane aji muke a
soyayya.

Soyayya tana da azuzuwa guda uku ne, wato
Soyayyar Ma’aurata da Soyayyar Saurayi da
Budurwa da kuma Soyayya ta Gama-Gari,
wacce take wanzuwa tsakanin sauran
mutane. Duka wadannan sun kasu kasha-
kashi, ga su kamar haka:
Soyayyar Ma’aurata: Ita ce soyayyar da ke
sanya dukkan jiki ya amsa. Ta fi kowacce irin
soyayya dadi, ita ce mai dauke da kauna,
tausayi da jinkan juna.Ta kasu kashi biyu su
ne kamar haka:

1-Cikakkiyar Soyayya: Irin wannan soyayyar ce
dukkan wasu ma’aurata ke son tabbata a
cikinta, domin takan mantar da su bakin ciki
saboda tausayin juna, wato dai farin ciki da
kulawa sun fi yawa a cikinta.

2-Sarkakkiyar Soyayya: Ita kuma wannan
soyayyar tana kunshe ne da rashin jituwa
sosai a tsakanin ma’aurata, duk da suna son
junansu saboda wasu dalilai, sai ku ga ana ta
samun matsaloli, dalilan kuwa sun hada da
rashin tsaftar jiki ko rashin ilimi da sauransu.

Soyayyar Saurauyi da Budurwa: Ita ma
wannan soyayya ce mai matukar mahimmanci,
wacce a ita ce ake gina turakun
zamantakewar aure domin a kayace take.

Ta
kasu kashi uku, su ne kamar haka:

1-Soyayya Mai Gudana (Ka So An So): A mafi
akasarin lokuta irin wannan soyayyar ce ke kai
wa ga aure. Soyayya ce wacce take babu
tsunbure a cikinta, wato kowane sashe yana
ba da hakkin da ya rataya a kansa (namiji da
mace).

2-Soyayya Mai Gudana Tilo (Ka So An ki, Ka ki
An So): Wannan kuma mutum daya ne ke
kamuwa da ita, daya kuma bai ma san ana yi
ba, sannan wannan soyayyar tana azabtar da
zuciyar wanda ya kamu da irinta.

3-Soyayya Mai Gudana Kurma (Soyayyar
Zurfin Ciki): Da jin kalmar zurfin ciki ko kurma
lallai za a fahimci cewa wannan soyayyar ’yar
shiru-shiru ce amma akan samu nishadi a
cikinta, sannan kuma sashe biyu ne ke
kamuwa da irinta amma a mafi yawan lokuta
wanda suke zaune waje guda (namiji da
mace) sun fi kamuwa da irin wannan
soyayyar.

Soyayya Ta Gama Gari: Ita wannan soyayyar
kusan kowa yana tsintar kansa a ciki, domin
ta game dukkan abin da ake rayuwa da su, ta
hade dukkan abin da z aka ji kana so, ban da
wanda suke sama.

Ta kasu kashi uku, su ne
kamar haka:

1-Soyayyar Iyaye da ’Ya’yansu: Kamar yadda
kowa ya sani, babu soyayyar da ta kai wannan
soyayyar karko da karfi a zukatan mutane. Ita
ce wacce ba ta gushewa.

2-Soyayya Tsakanin Al’umma: Ita ce mai cike
da gaskiya da rikon amana, a wasu lokutan
cike take da rudani da rashin tabbas da
hayaniya.

3-Soyayyar Tilas: Ita ce soyayyar da dukkan
wanda yake numfashi yake tsintar kansa a
cikinta, domin son ita kanta rayuwar na cikin
son da duk wani abu wanda ya zama dole
mutum ya so a rayuwa. Allah Ya ba mu damar
zama da masoyanmu cikin lumana da jin dadi
da rayuwar da ba nadama cikinta amin. **

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad