- A yanzu dai NCC ta sanyo su gaba saboda
satar tayi yawa
- Matsalar itace, ana kwashe kudi ace ka
sayi data bayan baka yi niyya ba
MTN zata biya tara saboda kwashe kudi don
saya wa kwastomomi data ba izini
Kamfanin MTN zai biya tarar
N5,000,000 ga gwamnatin Najeriya ta
hannun NCC muddin aka same shi da
laifin sake sace wa kwastomomi bayan
sun sanya kati a wayoyinsu na salula.
Satar tana zuwa ne ta hanyar sayen
data ko waka ko wasu shirmen dai da
mutum ya taba yi a baya, amma ba da
niyyar sake saya ba.
A yanzu NCC tace kada a sake saya wa
masu amfani da wayar salula
abubuwan da basu yi oda ba kuma basu
siya ba. Tarar zata shafi MTN ne amma
ana sa rai nan gaba zata shafi sauran
layuka.
Hukumar sadarwa ta Najeriya(NCC) ta
umarci kamfanonin sadarwar kasar,
dasu guji sabuntawa kwastomomi data
packages ba tare da izini ba. In kuwa
aka kamasu da laifin, za a ci su tarar
Naira miliyan 5.
NCC tace jan kunnen ya zama dole ne
sakamakon korafe korafen da masu
amfani da layikan keyi na kamfanonin.
A ranar 21 ga watan Mayu, 2018 ne NCC
ta bada umarni ga duk kamfanonin
sadarwan dasu guji sabuntawa
kwastomomi data packages ba tare da
yardar su ba.
Zababben mataimakin shugaban NCC
ya karanto zanga zangar tataunawa da
kwastomomi suka a ranar Alhamis, a
karu, jihar Nasarawa.
Zababben mataimakin shugaban,
wanda daraktan arewa ta NCC, Mrs
Helen Obi ta wakilta tayi bayanin
korafe korafen da suke samu yasa
bazasu jinkirta sanar da ma'aikatan
umarnin ba.
Bayan tarar Naira miliyan 5 da zata
biyo bayan karya dokar, ya kara
bayyanawa cewa duk rana daya da aka
yanke hukuncin ba a biya tarar ba, zai
janyo karuwar Naira 500,000.
"Yakamata kamfanonin sadarwan su
tura sakon karta kwana ga masu amfani
da layikan kafin sabunta, sannan su
kara maimaita tura sakon don tabbatar
da cewa an fahimci abinda sakon ya
kunsa. A duk lokacin da masu amfani da
layikan suka kawo karar kamfanin
sadarwan sakamakon karya dokar,
kamashon zai daukaka korafin.
Yanzu kam wannan na nufin
kwastomomi zasu daina rasa kudinsu ta
hanyar zamba da ake yi musu a
layukansu.
Source hausa.naija.com
No comments:
Post a Comment