*_LOKUTA GUDA 5 MAFI TSADA A WATAN
RAMADHANA_*
Hakika lokacin watan Ramadhana lokaci ne
mafi tsada gaba dayansa,amma akwai
lokacuta mafi tsada cikinsu,wanda sunfi
tsada a dukkan sauran lokuta baki daya.
1-Lokaci na Farko
*"Lokacin Shan Sahur"*
Wato daga da fitowar alfijir,wannan lokacin
yana da albarka guda ukku:
-Lokacin mai albarkane,
-Abincin sahur din mai albarkane
-sannan lokacine na amsa addua.
■Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Allah ya sanya albarka acikin abubuwa
guda ukku,acikin jama'a da Sahur......)*
@Dhabarany
■Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Lallai Allah ya sanya albarka acikin Sahur
da Awo)*
@Jami'i Sagheer
2-Lokaci na Biyu
*"Lokacin Bude baki*
Lokacin mai albarka guda ukku
-Lokacine na amsa addua
-Lokacin ne na farin cikin masu azumi
lokacin buda bakinsu
-Lokacine na samun cin nasarar musulmai
idan suna gaggauta buda baki.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Mutane guda ukku ba'a mayar da
addu'o'insu,adduar mai Azumi lokacin bude
baki,da adduar Shugaba adali da adduar
wanda aka zalumta)*
@Tirmzy da Bn Majah da ibn Hibban
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Mai Azumi yana da addua karbabbiya
lokacin bude bakinsa)*
@Ibn Majah
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Addinin Allah bazai gushe ba yana mai
samun rinjaye matuqar suna gaggauta bude
baki)*
@Abu Dauda.
3-Lokaci na Ukku
*"Daren lailatul Qadri*
Lokacin mai albarka guda ukku
-Samun gafarar zunubai
-Lokacin na amsa addua
-Lokacin na rubanya ladar ibada
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Duk wanda ya raya daren lailatul Qadri,
yana mai Imani yana mai neman Lada,an
gafarta masa abinda ya gabatar na
zunubansa)*
@Bukhari da Muslim
Mafi tsadar Abinda ake su karokin Allah
shine,afuwa da gafara sannan karoki abinda
kake so bayan haka,kamar yadda Hadisin
Nana A'sha R.A ta tabbatar daga Manzon
Allah s.a.w
4-Lokaci na Hudu
*"Lokacin da dare ya raba tsakiya,ko ya kai
kashi ukku na karshe"*
Manzon Allah ِﷺ yana cewa:
*(Idan dare ya wuce tsakiya,Ubangiji
Tabaraka wata'ala yana saukowa zuwa
samar duniya,sai ya riqa cewa:"Shin akwai
mai rokona na bashi,Shin akwai mai wata
buqata abiya masa,shin akwai mai neman
gafara a gafarta masa,yana ta fadar hakan
har zuwa fitowar alfijir)*
@ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻞ : (758 )
-5 Lokaci na biyar
*"Bayan sallar Assuba zuwa fitowar rana *"
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(.....Wanda ya zauna yana ambaton Allah
bayan sallar assuba yana zaune a inda yayi
sallah,yana ambaton Allah,har rana ta
fito,sannan ya tashi yayi sallar raka'a
biyu,bayan fitowar rana,za'a rubuta masa
ladar Aikin hajji cikakkiya...)*
@Saheehul jami'i
Allah ne mafi sani.
Yan uwana muyi kokari wajan kula da murar
wadan nan lokuta masu albarka.
Allah ka gafarta mini ni da mahaifana da
sauran musulman duniya baki daya.
*_Rubutawar: ✍🏼_*
*_Malam Mustapha Musa Abu Aisha
{Hafizahullah}._*
Daga: *_ZAUREN ADDIINU ANNASIHATU._*
Post Top Ad
Your Ad Spot
Monday, June 4, 2018
Home
Unlabelled
LOKUTA GUDA 5 MAFI TSADA
A WATAN RAMADHANA
LOKUTA GUDA 5 MAFI TSADA A WATAN RAMADHANA
About Arewa Tricks
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.
No comments:
Post a Comment