GIMBIYA ZAJLAT BABI NA 'DAYA. - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Monday, June 4, 2018

GIMBIYA ZAJLAT BABI NA 'DAYA.

Gaba ɗaya garin ya yi wani irin yin baki kirin
da shi da kyar mazauna garin ke ganun tafin
hannuwansu, a hankali duhun ya yayye sai
wata irin gugguwa ta taso jajjur da ita ta
soma shawagi da mutane tana makawa a
bango. Duk wanda hakan ya kasance a
kansa to kuwa baya faɗowa da rai sai ya
sheka barzahu, shekaru goma sha uku kenan
wannan annoba na adabar ɗaucin mazauna
birnin bisa wani gaggarumin laifi da suka
aikata babban tashin hankaƙin Sarkin garin
duk sanda hakan ya kasance ya kan rasa
dakaru da yawa abu mafi muni ya kan rasa
ɗan da ya haifa a cikinsa yau kimanin
shekara goma sha uku kenan wanda ya yi
daidai da rasa yaransa guda goma.
*ZAJLAT* Ita ce yar da yafi so fiye da
sauran yaransa shi yasa yake takaicin
rasata a wannan *GUGGUWAR ANNOBAR*.
A yau da wannan iska ke kaɗawa gaba ɗaya
hankalinsa ya yi masifar tashi jikinsa ko ina
rawa yake tamkar mazari zuciyarsa ta
cunkushe tamkar bakar kwalta idanunsa sun
kaɗa sunyi jajjur kamar ɗan buda a cikin
ruwan barkono.
Bayan kurar ta lafa ne, kuma katangun birnin
suka fara girgiza kamar zasu rufta inda sabo
sun saba da hakan sai iface-iface ke tashi
da guje-guje tare da kukkan kanannu yara da
sauri ya faɗa cikin gida ga mammakinsa
Zajlaht zaune tana karanta wasu surutai da
kunnuwansa suka juyo masa tamkar na
makiyansa tabbas kunnuwansa basu suka
jiyo masa karya ba ya shiga tunani yaushe
ne Zajlah ta samu keɓewa da makiyansa?.
Bai bi takanta ba ya sureta bai zame ko ina
ba sai ɗakin mahaifiyarsa bokanya Sharmila
ya direta tare da juyo wa a fusace ya bar
gidan sarautar.
Nan ne ya zama wajan ɓoyan Gimbiya
Zaljah duk shekarar da hakan ƴya kasance
sabida hakane take kuɓuta daga wannan
gugguwar annoba.
***
Fuskarta ɗauke da matsanancin fushi,
tamkar wadda aka aikowa sakon mutuwa
take duban dakarun dake zagaye da ita
wanda babu komai a jikinsu sai shigar silken
yaki baki yana walwali. Kowa ne daga
saman kansa akwai hular karfe baka an
mata ado da zaiba mai kyau tare da
ɗamarar adon wani gunki a rike da mashi.
Ta cigaba da zazzare idanu tana muzurai.
"Na rantse da abin bauta bazan ɗauki
wannan ba, a haifi ya a a gabana a tafin
hannuna tazo ta na neman gaggarata ina
karya ne! Abin bauta! Abin bauta!!".
Haka muryarta ta cigaba da amo da amsa
kuwa har zuwa lokacin da wasu dakaru suka
gurfanar da wata matashiya yar shekaru
kimanin goma sha biyu zuwa sha uku a
gabanta. Suturarta ta bambanta da tasu
sossai doguwar riga ce a jikinta fara mai
faɗi an mata adon da koron launi da kuma
zaiba mai daukar idanu kanta sanye da wani
kambu na sarauta mai ɗaukar idanu
gashinta ya zubo baki siɗik da shi tana da
idanu manya sossai a kwai kyawu tare da ita
duk da karancin shekarunta tana da girman
jiki sossai.
A hankali ta sauke idanunta a kan kakkaurar
matar wadda sabida muni in a ka ce ka
yankata hatta wukar saika ɓoyeta, hancinta
kato idanunta kulu-kulu jajjaye kamar idanun
ɗan buda a cikin ruwan barkono. Ta
sunkuyar da kai,
"Zajlat!".
Bata ɗago ba ta cigaba,
"me kike zuwa yi wajan waɗancan ɓatattun
mutanan? Ko kin manta fushin da abar bauta
ta yi damu a zuwanki na wancan karon?".
"Kiyi hakuri ya ke Kakata bazan kuma ba".
"Karya ki ke, indai waɗancan mutanan ne ba
zaki barsu ba sau nawa kina faɗa?. Ta
karasa tare da sunkuyowa ta ɗago fuskarta
suna jin numfashin juna,
"ba zaki gane ba amma zan koya miki
hankali ku tafi da ita ɗakin azaba!".
Ta faɗa da matsananciyar tsawa mai
firgitarwa, kafin kiftawar idanu sun kwasheta
sun tafi da ita ta kyalkkyale da dariya tare
da ɗaukar tambulan giya dake kusa da ita ta
soma kafa kai tana sha tana yi wa kanta
kirari.
2
MASARAUTAR SAMBASU
Birnin *SAMBASU* babban birnine dake
ɗauke da mutane kimanun miliyan dubu
goma. Birnin kewaye yake da kayan jin
daɗi da more rayuwa, gari ne daya shafe
shekaru sama da shekara ɗari da ashirin da
tara ana mulki a cikinsa mulki irin na bakin
zallunci. Sarkin dake mulkar wannan gari ya
kasance takadiri kuma gawurtacan sadauki
wanda ake matukar tsoronsa halima asalin
sarautar kwacanta ya yi ba gada ba, babu
abinda ya tsana a duniya irin musulmi da
musulunci.
Asalin Sarkin garin sunansa Sarki Markahu
yana da matar aure mai suna Sharmila tare
da yara goma sha biyu dukkaninsu maza
kuma babu wanda ba gawurtacan sadauki
ba cikinsu daga mafarauta sai mayaka yana
alfahari dasu sossai. Matarsa kuwa
gawurtaciyar matsafiya ce wadda ta amsa
sunanta asalinta ɗiya ce ga sarkin
sarakunan bokayan garin kafin ya rasu ta
haye kujerarsa, Sarki Markahu ya aureta ne
sabida ita jaruma ce kuma da taimakonta ya
kwaci sarauta yana matukar ji da ita kuma
baya tsallake duk abin da ta gindaya masa.
Tsanar da ya yi wa musulnci ta shahara
matuka hakan yasa bida shawarar mai
ɗakinsa ya gidana *GIDAN AZABA* kawai
sabida azabtar da musulmi. Mutanan
masarautar Sambusa basu da abin bauta
face wani katon taswirar suffar wani gunki
ne da aka kera wato JARBUBA. Duk wata
bukata tasu idan ba ranar bauta ba sukan
kawota ne ga SHARMILA ita kuma ta mikata
gareshi ko kuma mutum ya hakura sai ranar
bauta wato kowace Talata.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad