TAMBAYA - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Monday, June 4, 2018

TAMBAYA

TAMBAYA
========
👇
Assalamu Alaikum Malam ya azumi Allah ya sa mudace ameen, Malam inada tambayoyi guda biyu
1. Malam macce ce budurwa ke ciyon mara koda ba lokacin al'adarta ba to shi ne Malam ko mi yake kawo wannan matsalar.
2. Malam Dan'uwana yana raba zakka dai dai wannan lokacin yana baiwa yan uwanshi to yanzu sai masuyin garkuwa da mutum sunka kama Dan uwanshi suka ce sai anbasu miliyan biyu da dubu Dari uku to Malam zai iya yin amfani da wadannan kudin na zakka da yake rabawa domin ya kwato Dan uwanshi a hannun wayannan azzalumai? kuma Malam muna Neman addu'a Allah ya kwato muna shi a hannunsu ya dawo gida cikin koshin lafiya.nagode.

AMSA
=====
👇
1. Aure zakuyi mata, wannan shine matsalarta, wato Rashin Namiji yana haddasawa mace irin Wannan matsalar.
  Sabida haka Ku daure kuyi mata Aure, insha Allahu zakuga ta sami sauki.

2. Wannan kuma bai Halatta a dauki kudin Zakka a baiwa masu garkuwa da mutane ba, sabida Allah bai sanya masu garkuwa da mutane a cikin jerin wadanda za'a baiwa zakka ba.
Abu na biyu kuma, yaya zaiyi inda Ace ba lokacin da zai bayar da zakka bane? Sai yace bazai fanshe shi ba, har sai lokacin fidda zakka yayi zai bayar ya fanshi dan uwansa kenan?
A takaice dai gaskiya bai Halatta ba.
Ita zakka ana bayar da ita ne ga mutanen da Allah yace a baiwa,  Wato Talakawa, Miskinai, wanda yayi aikin fitar da zakkar, wanda ake tsammanin zai iya shiga musulunci idan an masa kyautar kudi, matafiyi, da wanda Wata mummunar Hasara ta sameshi, kamar gobara ko aka masa sata ko ya dauki nauyin biyan bashi kuma bai sami dama ya biya ba.

Allah Shine Masani


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAXA MATA 08108605876

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad