Assalamu alaikum barkanmu da war haka,
shafinhausa yakawo muku sabon posting
babu shakka wannan hanyace da ake bi don rike
martabar soyayya har zuwa tsufa, uwar gida
mutafi a hankali kamar haka:
abu na farko (1) shine:
zama mai nuna soyayya ga mijinki, da 'yan
uwansa da ya'yansa, ki nuna masa kauna, da
soyayya,ki nuna shi mai darajane a gareki, ki
nuna cewa shi mai mutuncine a gareki da kima,
idan zai je aiki sai kiyi mashi rakiya ki rike masa
jaka kina cewa mai gida Allah ya baka nasara ya
kareka, Allah yasa kadawo lafiya ya Kareka daga
sharrin makiya,ni wallahi idan kaje gurin aiki sai
naji kamar na biyoka, karka dade dan Allah( da
sunan da kike kiransa mai dadi) sannan kuma
kafin ya dawo kin gama abinci kinyi wanka, kin
shirya masa abubuwa masu dadi, kin shirya tsab
kina jiran shigowarsa,ki tarbeshi kina fara'a da
nuna farin ciki da dawowarsa, da karbar kayan
dake hannunsa, ki tayashi zama, da nuna masa
ruwan wanka, da ya natsu sai kice masa
mikakeso.
*(my love , my sweety ) da kalamai masu kyau,
kirki kawo masa damuwa sai ya natsu, sannan ki
nunawa kowa kina sonshi kuma ki rinka fada
masa gaskiya kowane lokaci da bashi uzuri,
kuma ki rinka bashi shawara cikin murya mai
sanyi.*
❦ *ZAI KARA SONKI* ❦
*uwar gida idan kina son soyayyarku ta karu
karki bari wasu su san sirrinku.*
_sannan karki bari wani namiji yasa mu dama
gareki, ki rinka sanardashi kuskurenshi cikin
ladabi da girmamawa, idan wani abun farinciki ya
sameshi ki nuna farinciki mai yawa, da nuna
damuwa da matsalarshi._
No comments:
Post a Comment