aslm barka da war haka,
sabon posting daga shafin Hausa,
yadda za a magance kurajen fuska wato pimples
kurajen pimples a turance ko acne bulgaris a likitance suna daya daga cikin larurori masu addabar samari da ’yan mata.
Suna fitowa ne a daidai lokacin girma, domin a daidai lokacin ne sinadarin nan na testosterone ke yawa a jinin samari
maza da kuma wasu kadan daga cikin mata.
Wannan sinadari shi ke da alhakin sa maiko ya rika taruwa a fuska. Idan maiko ya taru a fuska sai kwayoyin cuta su zo su taru a wurin su kawo kurji.
Hanyoyin kariya su ne kiyayi taruwar maiko da kwayoyin cuta a fuska da kirji.
Wannan kan dan yi wahala amma ta
wadannan dabaru za a samu nasara:
(1)-Rage maiko a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kitchen wipe mai tsabta kafin a ci.
Idan an yi haka an rage man kusan da kashi hamsin cikin
dari ko ma fiye.
(2)-Yin amfani da sabulu mai kashe
kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma.
(3)-Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki a kai-a kai yakan tsane maikon cikin jini ya kara karfin
garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin
cuta.
(4)-Ga wanda wadannan dabaru ba su yi musu aiki ba, za su iya zuwa su nemi man shafawa a fuska da kirji mai dauke da sinadarin benzoyl perodide na
shafawa safe da yamma bayan an
wanke fuska.
(5)-Idan hakan ta ki wadatarwa sai an je asibiti an hada da karbar magungunan kashe kwayoyin cuta.
6-Ga wadanda wannan ma bai yi aiki ba, akwai dai magunguna masu karfi har ila yau irin samfurin bitaman ‘A’ da ake kira isotretoin da ake rubutawa a asibiti.
Akan samu nasara sosai idan aka jarraba wadannan. Amma ba a
bawa mai juna biyu shi.
(7)-Ba a so a rika matse kurajen saboda hakan kan iya jawo tabo, an fi so a bar su su fashe da kansu sai a wanke wurin
kukasace damu a shafinhausa
No comments:
Post a Comment