_KISAN DA WAYE KIKE SOYAYYA_ part (2) - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, March 7, 2018

_KISAN DA WAYE KIKE SOYAYYA_ part (2)

*_KISAN DA WAYE KIKE SOYAYYA_*
.
.
.
Fitowa ta 02.

*JAN AJI A SOYAYYA BA ABIN DAYAKE HAIFARWA SAI NADAMA.*

Idan saurayinki ya tsaneki ko ya gudu ya barki ko kin rasa wani abu da yake baki, kiyi haquri kada ki juya masa baya, kisa masa shakka a ransa ya dinga tunanin anya kuwa kina son sa da gaske???
.
.
.
*KEDAI KAWAI KI KARE MUTUNCINKI DA IYA TAKUNKI.*

1. Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki fuska yana shigo miki da kalmomin da basu daceba ko dabi'u, kamar yace zai samiki zobe, ko zaiga awar waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga fulawarki, ko zai auna kaurinki dadai sauransu.
*SABODA HAKA KIZAMA ME BATA RAI A DUK SADDA KIKAGA HAKA, KODA YATAFI KIRABU DASHI, DAMAN BA NAGARI BANE, SOYAKE YA BATAKI.* Wakilin shaytanne.

2. Ki zama me yiwa saurayinki Al-qawarin nuna masa soyayya bayan aurenku, sannan dayi masa biyayya dai dai gwargwadon iyawarki.
*KISANI DAYAWAN SAMARI AKWAI MAKIRCI.* Wani yasan ba aure zaiyi ba amma zaizo yabata miki lokaci. Wani soyake yakoyi zance sai kawai yazo wajenki yayi tayi miki qarya batare dakin fargaba zai dasa miki ciwon so, *YA KORAR MIKI SAMARIN KI NAKIRKI.* Wani kuma kawai so yake yana zuwa wajen fati dake. Saboda haka zaina saya miki kaya kala kala yana fira da ke zai fake da cewa *SAI YAGAMA* School *KO SAI BAYAN YAGAMA KARATU ZAI TURO KUYI AURE.*
Duk party ko fikines zai daukeki kutafi.

Wani kuma soyake kawai yana taba jikinki yaji dadi koda bai kwanta dakeba, saboda haka zaita binki sauda qafa yana soyayya dake. Wani kuma so yake ya bataki. Irin wadannan samarin sunfi kowanne hatsari. Idan yaganki yana sonki yana fara karantar halayenki *IDAN YAGA KE USTAZIYACE TO ZAIYI SHIGAR USTAZAI HARDA LITTAFIN SA A HANNU, HAKA ZAITA KAFA MIKI TARKO HARSAI KIN FADA.* Idan yaga 'yar *BOKOCE* zai fito miki a dan boko. Idan yaga ke yar duniya ce to shima a hakan zai fita.

Irin wadannan samarin har kayan mungani munaso suna kaiwa budurwa, har iyayensu suna turowa daga qarshe daya kwanta dake shikenan yabiya buqatarsa, bazai bari kisami cikiba zaibaki qwaya da zarar yaga baki da ciki yasan yayi (free) tunda ya sami abinda yake nema, zai Qirqiri laifi yalaqa miki domin ku6ata a karbo kayan sa daga gidanku, koma yabar miki kayan... Irinsu akwai makirci da nuna tsagoran soyayya ga budurwa, domin sukanyi kukan hawaye a gaban budurwa duk da sunan so amma yawanci domin ya raunana zuciyar kine. Yakan maqale miki har unguwa yana rakaki koda yaushe.

Insha Allah zamuci gaba mu hadu a zama na 3.

Rubutawa: Ãbûbäkår Ëkä.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad