assalamu alaikum yan uwa,
sabon posting daga shafinhausa
LAUNUKAN SOYAYYA
Soyayya ta kasu kashi daban-daban dangane da
dan tsiron da ya shuka ta tun farko da kuma
yadda aka gudanar da ita yayin da take girma da
kuma irin sakamakon da ake sa ran samu daga
gare ta.
A jimlace,soyayyar auratayya tana da launauka
guda biyu:
*cikakkiyar soyayya da kuma sarkakkiyar
soyayya.*
*1. Cikakkiyar Soyayya*
Ita ce kammalalliyar soyayya da ya kasance
komai ya ji a
cikinta; Ita ce soyayyar da ya kamata a ce
kowane aure a
kanta yake tafiya; ita ce soyayya mai cike da so,
kauna, rahma da tausayin juna; ita ce soyayyar
da ke cike da shakuwa, fahimtar juna, mutunta
juna da sha’awar juna; ita ce wacce ta kunshi
dukkan mafi kyawon sinadaran soyayyar nan
guda hudu da bayaninsu ya gabata.
Dadin dacewa da cikakkiya kuma kammalalliyar
soyayya, dadi ne da babu irinsa a zuciyar dan
Adam; yana daga ruhin dan Adam zuwa ga
kololuwar farin ciki; don haka babban al’amari ne
da ya kamata dukan ma’aurata su dage ga rike
shi da kyau; ya zama samun irin soyyaya shi ne
burinsu; su rike shi kamar wani muhimmin
kasuwanci mai cike arziki mai yawa; kar su bari
jarinsu a wannan kasuwanci ya karye,
in ma ya karye su yi dukkan kokarin da ya
kamata don kara samun jarin zubawa don guje
ma kasancewa cikin kuncin kishiyar hakan a
rayuwar aurensu.
Da fatan Allah Ya hore
ma dukkan ma’aurata wannan kyakkyawar
soyayya, amin.
*2. Sarkakkiyar Soyayya*
Ita ce soyayya da ba ta amfanar ma’aurata,
cikakken
amfani; ita ce soyayyar da ke takurawa ga duka
ko daya
daga cikin ma’aurata; ita ce gurguwar soyayya
mai nakasun biyu ko ukku daga cikin sinadaran
da suka gina soyayya.
Ita ce soyayya mai cike
rashin fahimtar juna, yawan fadace-fadace, zargi
juna; rashin yi ma juna uzuri; munana zato ga
juna.;
ita ce soyayyar da ba ta ba da yabanyar jin dadi
da kwanciyar hankali.
Ita ce soyayyar da ke nutsar da ma’aurata cikin
ramin kunci da tashin hankali; ita ce fankon
soyayyar da ba shakuwa, ba tausayi a cikinta
SHAFINHAUSA
No comments:
Post a Comment