assalamu alaikum
sabon posting daga shafinhausa
dadimi diminsa,
- Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta
rasa budurcin ta
- Tayi wannan bayanin ne yayin da take yin
fira da majiyar mu a satin da ya gabata
- Ta ce an taba yi mata fyade ne alokacin tana
yarinya karama ne
-Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan
Hausa a masana'antar Kannywood
Rahma Sadau ta yi karin haske game da
yadda ta rasa budurcin ta kamar dai
yadda ta taba bada labarin cewa ita ba
cikakkiyar budurwa bace ba a watannin
baya.
Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta bada
labarin yadda ta rasa budurcin ta
Jarumar dai ta yi wannan karin haske
ne yayin da take yin fira da majiyar mu
ta Mujallar fim a satin da ya gabata
karon farko tun bayan dawowar ta daga
kasar Turkiyya inda taje karatu.
SHAFINHAUSA ta samu cewa jarumar ta
bayyana cewa maganar da tayi a
watannin bayan na cewa ita ba
cikakkiyar budurwa bace ba wai tana
nufin ta taba zina ba ne domin ita
hasali ma ba ta taba zina ba tun da
Allah ya halicce ta.
Jarumar ta kara da cewa abunda take so
ta fadawa duniya shine an taba yi mata
fyade ne sadda tana yarinya karama
kuma a lokacin ne ma ta rasa budurcin
na ta kamar dai yadda ta fada.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa
muhawara ta zafafa a watannin baya
lokacin da jarumar ta bayar da ansa ga
wani masoyin ta da ya tambayeta
matsayin budurcin ta a kafar sadarwar
zamani ta Instagram inda ta ba shi ansa
da cewar ita ba cikakkiyar budurwa
bace.
Kuci gaba da kasancewa damu a
www.shafinhausa.tk
No comments:
Post a Comment