Assalamu alaikum yan uwa barka da warhaka
MAGANIN MATA KO MUSIBA
Wallahi mata mu shiga hankalin mu,musan abinda ke gaban mu,mu san menene aure da zamantakewar aure.
Shin jima'i ne kadai abin da ke cikin aure?
Shin da jima'i kadai ake farantawa miji?
Shin jima'i ne zai kai ki ga hanyar tsira bayan kin kaucewa dokokin ubangiji wajen neman maganin mata?
Yau kece bin wannan grp na maganin mata,kece xua neman lakani,kece sa laya kasan gado,kece yin hatimi a sa sunan miji ciki,kece gun malami kaza duk kan namiji,shi mijin da kike yi don shi me yake yi ko yake sha don ke,wace laya ya saka sbd ke,wace shirka yayi don ya gamsar dake a gado? Wllh muji tsoron Allah mahaliccin mu.
Shin akwai wani halitta daya isa ya juya hukuncin ubangiji kan ki ko kan maigidan ki?
Shin akwai wani malami daya isa ya chanja miki halayyar mijin ki da Allah yayo shi da ita?
Wallahil Azeem babu wani mahaluki daya isa ya chanja abin da ubangiji yayi. Wai yau mata ke tona asirin kwanciyar su da mazajen su,abinda ubangiji ya lullube ku ya baku karia amma mata sun fito suna bayyana shi,
Yau wannan tace ai yayi ihu,yayi min kuka,yayi nishi,kaiiii wa'iyazubillahi,,,,TIR DA MATA MASU BAYYANA SIRRIN MAZAJEN SU DA MASU YADA SU.
Idan baku sani ba to ku sani yau,magungunan da kuke dirkawa cikin ku sune ummul abaisin cututtuka da yawa na jikin ku,km matan da suke wannan haukan shaye shayen da sake saken abubuwa a farjin su basu cika diban shekaru ba masu yawa suke lalacewa sabida duk sun gama takura gwayoyin halittar su sun sa su sunyi aikin daya wuce kima.
Yar uwa ki bi Allah,kibi annabi kiyi addua km sannan kiyi biyayya ga mijin ki wallahi sai kin zama abin kwatance ba tare da yin shirka ba. Akwai abubuwa da yawa cikin cimar mu da zasu taimaka mana. Misali,AYA,KWAKWA,YAYAN ITATUWA,ZUMA,ZAMZAM,GANYAYYAKI IRIN SU ZOGALE,ALAYYAHU DA SAURAN SU.
GARE KU MASU SIYAR DA MAGANI......KUJI TSORON MAHALICCIN KU,KU SANI CEWA AKWAI RANAR DA ZA'A TSAYA GABAN UBANGIJI,KUSANI DUK RANTSUWAR DA KUKE YI DA KARAIRAYI KAN MAGUNGUNAN KU DA KAUCE HANYA DA KUKE YI WAJEN ZUWA GUN BOKAYE A KWAI RANAR DA ZAKU GIRBE SHI,DON BA MALAMAI SUKE BA MALIN MALIN NE KAWAI. KU SANI DUK WANDA YAYI AMFANI DA LAKANIN DA KUKE SAIDAWA TO KUNA DA BAB BAN KAMASHO CIKI GURIN UBANGIJI.DUK CUTARWAR DA MAGANIN KU YAYI KUNA DA KAMASHO. SHIN KU DA KUKE YIN LAKANIN DA MAGUNGUNAN ME KUKA SAMU GUN MAZAJEN? SHIN BAKU SAMIN SABANI DA SU? SHIN NAWA YA BAKI? SHIN JUYA SHI KIKE YI YADDA RANKI YAKE SO? SHIN MAGANIN KU KO LAKANIN KU YA HANA MAZA DUKAN MATA? SHIN AN DAINA SAKIN MATA A AURE? SHIN MAZA SUN DAINA JIBGAR MATA?
IN KURA NA MAGANIN ZAWO TAYIWA KANTA MANA JAMA'A😃😃DA SAI KU DAINA WAHALAR DA KAN KU WAJEN NEMAN KASUA KUYI TA AMFANI DA LAKANIN KU MAZAJEN KU NA MUKU KYAUTAR BANMAMAKI.
A KARSHE YA YAR UWA MAI NEMAN ALJANNA TA BIYAYYAR AURE KI YI
ABINDA ALLAH YA UMARCE KI DA YI,KI KARE JIKIN KI,KI NISAN CI FASIKANCI,KI BI UMARNIN ALLAH DA MANZON SA.
KIYI ADDUA KAN NEMAN DACEWA DA YARDAR UBANGIJIN KI. KIYI ADDUA UBANGIJI YA SAUKAR DA RAHMA,SALAMA,YARDA DA KUMA AMINCHI TSAKANIN KI DA MAIGIDAN KI.
KIYIWA MAIGIDAN KI BIYAYYA,KI CIRE GIRMAN KAI DA JIJI DA KAI, KI NUNAWA MAI GIDAN KI LALLAI SHINE SHUGABA WAJEN KI MUDDIN BA SABAWA UBANGIJI YAYI BA. KIYI MASA BIYAYYA IYA BIYAYYA,KI SO SHI KI KAUNACE SHI.
DA KUDIN KI KALILAN KI GYARA KAN KI WAJEN SIYAN YAR KANKANA,DABINO,KWAKWA,ZUMA,ZOGALE,YAR AYAR KI,DAN ALAYYAHU,DA RAKEN KI,DA ZAMZAM DUK ZAKI GYARA JIKIN KI YAR UWA KIN HUTA DA ADASHIN DA BA RANAR DAUKAR SA😃😃😃
A karshe nake mana fatan ubangiji yasa mu gyara wannan halayya da muke, ubangiji ya saukar da nutsuwa a cikin zukatan mu da ruhin mu,Allah ya saukar da rahma da aminchi da salama da yarda a gidajen auren mu.
Wassalamu Alaikum
No comments:
Post a Comment