*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
02
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~
08034840276
*waiwaye daga shafin baya*
kar maikaratu ya manta, mota ta cika, inda Ameer da Aeeya suke a kujerar gaba, a baya kuwa; mutum hudu ne, da kirista mai suna Fate, sai Abdulsamad da Saddam da tsoho.
sun dauki hanya ba tareda wani tsaiko ba.
_cigaba_
daga fitarka a tashar laulaya daya kadai zaka wuce wacce zata baka damar ficewa barka da zuwa ko ka dauki hannun hagu zuwa unguwar filin sukuwa.
Daf da laulayar ta hannun damma akwai gidajen mai guda biyu, da direba yazo gidan mai na farko sai ya tsaya domin ya karawa tankinsa mai.
Ai kuwa sukayi sa'a ba layi motoci uku ne kadai a gabansu sai masu mashin su biyar.
Bayan direban ya tsayarda mota sai Aseeya ta cewa Ameer 'Malam kayi hakuri inaso in fita insha iska'
Kamar baiji me ta fada ba, sai da ya dauki lokaci kafin ya motsa, a ranta tace, 'kar ma ka fita wallahi da sai in taka ka in fita'
Nan ta dinga zagayo gidan mai din, sosai fasalin ginin ya birgeta, abinka da mace bata ko kula da dinbin mutane da ke wurin ba, sai faman daukan hoto take.
Ameer kuwa ba abinda yakeyi in ba dannar waya ba, idan ya fita wannan shafin ya shiga wannan, sai bincike bincikensa yakeyi.
Bayan an kammala saka musu mai, suka koma cikin mota direba ya fara hanya.
A kujerar baya Abdul samad da Saddam sai gulma suke suna kus kus kan Aseeya lallai kyakkyawa ce, sai dai kash akwai ta da tsiya ga masifa, dukkansu har sun fara tsoronta.
Fate kuwa tun fara tafiyarsu bayan ta kammala addu'a irin nasu ta bude ~Bible~ ta ci gaba da karantawa.
Dai dai isowarsu barka da zuwa (welcome to) nan Ameer ya fara magana, yace 'tabbas canji ya fara duk da mu talakawa mun kasa hakuri yadda ya kamata'
''Me yasa ka fadi haka?" Aseeya ta fada dai dai lokacin da take juyowa ta fuskanceshi.
''A gwannatin da ta gabata'' Ameer ya cigaba, ''a nan barka da zuwa da zarar ka karaso hannunka a gaba, sojoji da 'yan sanda ba za ka wuce ba har sai ka bayar da wani abu na kudi, naira 20 ko 50, idan kaki ka fuskanci wulaqanci, amma ji yanzu duk sun kama aikin da ya dace, ko wannan ai ci gaba ne.'
'
''Haka ne'' Dattijo da ke baya ya fada, a daidai lokacin da yake kokarin gyara zamansa kasancewar a matse suke a baya.
Da zarar ka wuce barka da zuwa garin Sabon gari ne zakayi kicibis da shi wanda dama da hangun titi duk shi ne, sai dai a bangaren hagu garin yafi yawa a dama makaranta ce kawai sai gidaje marasa yawa.
Muatanen garin sun kware ne a noma da kamun kifi kasancewar suna makotaka da ruwa.
A titin bakin garin mutane ne cike da sana'o'insu kala kala.
Haka suka ci gaba da tafiya sai fira akeyi da juna cikin motar.
Lafiya lau suka karaso junction na garin Kalgo, junction ne da idan ka mike tsaye zaka isa Basaura sai Jega, idan ka shiga ta dama zaka iya karasawa zuwa Bunza ya zuwa Kamba.
Suka shiga kwanar dama kasancewar Kamba suka nufa.
Abin sha'awa yadda titin ya kawatu da shaguna da sana'o'i daban daban a hagu idan zaka wuce kasuwar garin ce, wacce ke ci duk ranar alkhamis.
Direba ya taki motarsa suka kara nutsawa cikin jeji, har suka karaso inda aka gina parmanent site na FUBK ( _federal university birnin kebbi_)
Ku biyoni har yanzu labarin bai fara ba
dr. Zain
No comments:
Post a Comment