BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 4 - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, March 7, 2018

BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 4

*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_

                           🐲

_THE DARK FOREST_


0⃣4⃣



© *ZAINUDDEEN ZAIN*

® _pen writers association_
✍🏾


~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~




*Waiwaye*

_A shafin da yagabata, mun ji yadda shaye-shaye ya zamo har a cikin mata, da ake tunanin sune jigon tarbiyya, haka munji yadda ~Bible~ da addinin musulunci suka haramta wannan mummunar dabi'a. haka munji ashe masifaffiya Aseeya 'yar aikin jarida ce, munji Ameer da ke zaune tare da ita a kujerar gaba, marubuci ne kuma mai bincike._


*Ci gaba*



Junction din garin Diggi zai iya sadaka da garin Tilli idan ka tsallaka ruwa haka zuwa Zogirma har zuwa Bunza da sauransu.

''Tunanina 'yan Jarida basada masifa amma a naki labarin daban ne''

Ameer ya fada daidai lokacin da yake kokarin ajiye wayarsa a aljihun rigarsa na gaba.


''Ni kuma tunani Marubuta akwai su da surutu da iya feso karya.''

Ta fada ba tareda ta ko kalleshi ba.

''Ai abubuwan da muke rubutawa a littafai ba karya ba ce.''

''Okay now tell me, labaran da kuke yi na yaki, ya ma za ayi ya zama gaskiya, mutum daya sai kaga ya tarwatsa rundunar sadaukai dubu. Ko wai kaga mutum yana tashi a sararin samaniya.''

''Hmmm! 'yar Jarida; labaru da muke yi na rayukan jama' a hasashe ne, sau tari wasu are based on true life. Na yaki kuwa domin nishadi ne da kuma haskowa mai karatu wani abu da zai fadada tunaninshi.
Amma kinga ana zarginku da labarun kage ko sauya labari idan aka cika maku aljihunku..''

''Haba ai cin hanci na wadanda basusan aikin Jarida ba ne, amma ai Dan Jarida muryar al'umma ne, idan ya sayar da kansa talakawa ne ya sayar.''

''Hakane diyata'' tsoho ya fada

Haka suka ci gaba da tafiya har suka karaso garin DANGOMA

Abdul Samad ne yace 'yanzu idan inaso in zama marubuci ya zanyi abokina?
Ina sha'awar rubutu amma sai nake ganin kamar bazan iya ba'

''Ba abinda ba ya ke da wuya aboki matukar mutum zai bi daki-daki na ka'idoji na yadda aka tsara komai. matsawar za ka iya jure biyar dokoki zama marubuci abu ne mai sauki,
Misali akwai wanda shi da rubutu aka haifeshi a jininsa rubutu yake, irin wannan idan ya fahimci kansa sai yayi kokarin neman shawarwari wurin manyan marubuta da kuma dagewa wurin bincike
Akwai wanda koyon rubutu yake ba a haifeshi da shi ba, idan ya fahimci kansa sai ya yi kokarin gurfanawa gaban manyan marubuta suyi masa bita.
Inaga kana cikin kashi na biyunnan''

''Nagode abokina zan karbi lambarka idan mun sauka sai muji yadda ya dace infara domin inada labarai da nakeso na rubuta''

'Idan kuwa haka ne, kar ka saka wasa, yanada kyauka hanxarta, domin baiwar rubutu ba abin wasa ba ce.'

''Allah ya taimaka''

Driver ya fada dai dai lokacinda yake canja wakar da ya saka a motar



''Subhanallahi!''

Driver ya fada


Cikin nuna damuwa da matsanancin tsoro suka hada baki


'me ya faru'?

''Wallahi faci ne muka yi,''

a dai dai lokacin da yake parking na motar a gefen titi rabin kilometer daga fita garin DANGOMA.


'yanzu ya kakeso muyi, shi ne ake cewa 'yan tasha bakusan darajar mutane ba'

''Bauyar Allah ya kikeso nayi ne, ai ni ba Ubangiji ba ne da zan iya hana wani abu ya faru, kuma dai kowa shaida ne ba gudu nake yi ba
Ya kina magana kamar ba musulma ba, ko wannan aljihun bayar ai bazata fadi haka ba''

ya fada cikin bacin rai, kamar ya kai hannunsa kan ta.

''Dakata malam''

Fate ta fada cikin rashin iya Hausa sosai



''Meye aljihun baya kuma naga sai da ka nuna ni kafin ka fadi hakan?''


Saddam ne ya sarbe maganar da cewa

''Kafiri ne aljihun baya wanda bai yarda da Allah ba''

''TO ai mu kirostoci mun yarda da Ubangiji''


ta fada cikin izza


Ameer ne ya kwace maganar

''wane irin imani kuka yi da Ubangiji?''


''Don Allah ku fita''


Driver ya fada

''ku karasa cen a waje taya zan canja''



kamar fama jiransa take ta sarbe cikin fushi, 'Ai dole mu fita malam, domin ba zamu tsaya ba zafi ya illata mu''


Duka suka dugunzuma waje

Nan Ameer ya matso kusa da Fate yace

'' inajinki baki bani amsar tambaya ta ba''



Ku biyo ni har yanzu labarin bai fara ba

Dr. Zain

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad