assalamu alaikum barkan mu da war haka yan uwa,
sabon posting daga shafinhausa
ME KUKA SANI AJIKIN RAKUMI?
Rakumi baya bukatar gabatarwa awajen jama'a
an san sirrikansa don waraka da kuma yanda
ma'aurata zasu gyara jikinsu maza da mata don
haka zan fara da bayani akan kazar amarya da
kuma tsumin amarya kuma duka wadannan
nononsa kawai ake bukata
(1) duk lokacinda Zaki dafa kazar amarya kada ki
manta nonon rakumi shine miyarki idan kuma
baki iyaba bari kiji yanda zakiyi
Kaza budurwa ake samu Wanda bata taba kwai
ba idan aka yanka anaso ki cire hanjin da kai da
kafa sannan ki dafata da ruwa idan kinga ta dafu
to saiki zubar ruwan saiki zuba nonon rakumin
dama kin daka kanunfari da minanas da Dan
kumasau da ridi saiki zuba anaso man ayu ya
zama shine mayinki sai kuma ki zuba kayan hadi
yanda zai miki dadinci daga kin kara dafa
wannan kazar shikenan kin hada gaba daya
akeso mace ita kadai ta cinye har romon
(2)/shima tsumin amare idan baki iyaba ga yanda
zakiyi kawai Ki samu kwakwa da dabino ki jika su
ki markada ki tace sannan ki kawo nonon rakumi
ki zuba saiki zuba zuma kadan ki ajiyeshi har sai
yayi kwana uku to tsumi ya hadu sai Sha
Wadannan idan kikayisu cikowar gaba dum dum
ni ima kuwa lutsu lutsu ba kakkau tawa ki jarraba
ba sai lallai amaryaba uwargida kema kiyi.
No comments:
Post a Comment