Yadda zaki kwalliya ba tare da amfani da kayan kwalliya mai yawa ba - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Thursday, March 8, 2018

Yadda zaki kwalliya ba tare da amfani da kayan kwalliya mai yawa ba

aslm sabon posting daga shafin Hausa

Yadda za a yi kwalliya ba tare da amfani da kayan kwalliya masu yawa ba
Samun fata mai laushi da sheki da santsi da kuma kyau na daya daga cikin ababen da kowace mace za ta yi fatan samu.

Akwai hanyiyo da dama wadanda za a bi domin gyaran fuska da kuma fata .

•Shan ruwa: Yawan shan ruwa na sanya shekin fata. Yana da kyau a rika shan ruwa a kullum ko da kuwa lokacin sanyi ne ko ruwan sama. Domin yawan shan ruwa yana wanke maikon fata domin rage kuraje.

•Shafa man fata (Moisturizer): Ya kamata a kullum a rika shafa wannan man a jiki kada a rika barin fata a bushe. Barin fata ba mai na sanya gautsin fata. Kuma a kullum a tabbata ana shafa man fuska da kuma na hannu domin rage tsufan fata.

•Ana amfani da sabulun wanke fuska; sabulun wanke fuska (face wash) ya zama a cikin kayan gyaran jikin ‘ya mace. Domin kuwa yana da kyau a wanke fuska a kullum kafin a kwanta bacci hakan na rage fesowar kurajen fuska.

•Ana amfani da man ‘toner’ domin dan dadawa fuskar haske kadan ba mai yawa ba wannan man na hana fuskar sakewa yana sanya fuskar ta zama sumul kamar ta mai shekara 16.

•Kada a manta amfani da man SPF; wannan man dai na kare fuska daga kunan rana.

Idan ana shafa shi, fuskar kullum za ta kasance kamar tana yini ne a daki wanda ake kunna mata na’urar sanyaya daki.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad