BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 3 - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, March 7, 2018

BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 3

*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_

                           🐲

_THE DARK FOREST_

0⃣3⃣



© *ZAINUDDEEN ZAIN*

® _pen writers association_
✍🏾


~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~


*Shafin masoya*

Queen (fake queen)
Rabeauty (gwauruwa)
zeety
Nordeen Amrabat
Maimartaba


*waiwaye*

_shafin da ya gabata, munji firar mahayan motar ta cigaba da akasamu fannin tsaro da sauransu, haka munji cewa motar ta cigaba da tafiya har suka karaso a ginin makarantar FUBK, har yanzu da saura, labarin bai fara ba_


*cigaba*




'Kai makarantarnan gaskiya ta ginu, sai dai akwai courses da dama wadanda basa cikin tsarin makarantar har yanzu'

Maganar da ta fito daga bakin Abdul-Samad kenan; 'kasan sabuwa ce' dattijo ya fada.

'Sai nake ganin kamar gate din school din yayi kusa da titi sosai lura da wannan titin babba ne'
inji Abdul-Samad.

'Kai malam injiniyoyin da sukayi aikin ne takkwalai ko me kake nufi? In ce, sai da aka tara manyan injiniyoyi kafin a fara wannan aikin, daga sama zaka zo kace gate din baiyi ba; duk wanda ya raina tsayuwar wata ai sai ya hau ya gyra'

Asiya ta fada a lokaci daya kanta na sunkuye sai karatu take zabgawa.


'Hahahahahaha'! Saddam ya fashe da dariya, ya dinga tokarar abokinsa da yatsa yana tsokanarsa.

Cike da tsarguwa Abdul samad ya ko kasa iya furta wata kalma, duk da a ransa ji yake kamar an tsoma shi a dakin dahuwar biredi.

Dattijo ne yace 'wai ke diyata wace iri ce? Sai angama fira da ke lafiya, lokaci kadan sai ki birkice? Gaki kyakkyawa wannan fadan zai kore maki samari fa'

Ameer tuni ya suku sai murmushin dole ke fita a lallausan kumatunsa

'Ai kai baba, duk wanda yace ya goya samarin zamani ai bansa hujewa zaiyi, ba abinda ya ragewa samari idan ba karya ba, bokonnan shi kadai mazajen nan kebbi suka dogara da shi, sai su gama aiki yazo yayi tsaye, gwannati tayi dasu su koma noma da kiwo, Ball da ji da kai da gayu sun hana, sun manta sam a farkon wannan kasar ta noma muka habbaka, wallahi baba mannan da kake gani zai baka mamaki, nomannan da kiwo da muka raina su ne dai abin kamawa'.

'Diyata zancenki dutse, gaki karama amma da tunani....'
Abdul ya kado bakinshi,

'ai matan yanzu ne basada alkibla, in banda kwadayi ba abinda suka saka a gabansu, shaye shaye da lesbianism sunyi yawa a cikinsu har basa ko kula samari...'

'Kajika tau shaye shayen tareda wa sukeyi? Wa ke dauko musu abubuwan da zasu sha? Mace zaka gani 'yar Islamiyya amma duk yadda za a lalata ta gayu sun sani.'

'Lallai da sauran ki 'yaruwa, mata ai yanzu sune diloli na miyagun kwayoyi, kedai Allah ya shigemuna gaba.'

Fate tace, 'hmmmm ai bantaba ganin masu yaudarar kansu irin miutanenku (musulmi) ba, kunce ku salihai ne, kuma kuke shan kayan maye'.

Cikin sauri Ameer ya waigo kamar dama jiranta yakeyi yace 'in banda ke ai gara mu littafinmu yasan matsayar da yayiwa shaye shaye, mutane ne a ko wanne addini sai ka sami bata gari wadanda basa biyar karantarwar addininsu, bari in karantomaki wasu ayoyi daga littafinku kiji kwamachalar da ke ciki'
A littafin *BIBLE* _in the book of_ ```Isaiah chapter 55 verse 1-2``` *Ho, every one that thirsteth, come ye to the waters, and he that has no money, come ye, buy, and eat; yea, come, buy wine and milk without money and without price.*
*2. Wherefore do ye spend money for that which is not bread? And your labour for that which satisfieth not? Hearken diligently unto me, and ear ye that which is good, and let your soul delight itself in fatness*
Wannan daga *KING JAMES VERSION* ne na *BIBLE*

'idan kika lura sun zargi sayen giya a cikin wannan ayar.'

'Ki duba kuma _book of_ ```Isaiah chapter 56 verse 10-12```
*his watchmen are blind : they are all ignorant, they are all dumb dogs, they cannot bark; sleeping, lying down, loving to slumber.*
*11. Yea, they are greedy dogs which can never have enough, and they are shepherds that cannot understand; they all look to their own way, every one for his gain, from his quarter.*
*12. Come ye, say they, i will fetch wine, and we will fill ourselves with strong drink; and tomorrow shall be as this day, and much more abundant.*
_KING JAMES VERSION_

'a nan ma an zargi shan giya idan kika natsu kika karanta.'

'Ga wasu'
*ISAIAH 5:12-13*
*PROVERBS 23:29-33,35*
*PROVERBS 23:30-31*
*PROVERBS 31:4-7*
Duka wadannan ayoyin sunyi kashedi ne da hannunka maisanda kan shaye shaye

*bible* bai barku ba har sai da yaimaku gargadi kan shaye shaye.

```Book of Isaiah chapter 28 verse 1```
*woe to crown of pride, to the drunkards of Ephraim, whose glorious beauty is a fading flower, which are on the head of the fat valleys of them that are overcome with wine.*
_KING JAMES VERSION_
Ki duba
*romans 13:13*
*luke 21:34-35*

'Idan har haramtawa ce gashi kin gani a littafinku, a yau a Birnin Kebbi ke a ma wurare daban duk inda ake shangiya zaki tararda *Pastors* ne kan gaba, me yasa ba za su hanu ba?
Ko wanne addini dole zaki zaki tarar da mashaya, amma ki daina kyamar wani addini shi kadai.'

Duk wadannan hujjojin yana fada tana buda littafinta na *bible* domin gasgata ko karyata shi, inda ta ga duk ayoyin haka ne.

'Kai musulmi ne kuwa' Asiya ta fada a lokacinda take kallonsa.

Cikin murmushi yace 'hala ke 'yar jarida ce? '
Naga duk nayi magana sai kinyi tambaya
Ba tareda tace komai ba sai ta mikamasa Id card inda ya tabbatar ita 'yar jarida ce da ke aiki karkashin *JARIDAR DIMOKURADIYYA* da ke da cibiya a garin kaduna.

'Ni musulmi ne, rubutu da bincike ne aikina.'

A dai lokacin suka karaso a junction da zaka dauke zuwa garin *diggi*

har yanzu labarin bai fara ba
dr. Zain

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad