TRUE LIFE STORY
*
MATAR ABOKINA.
*
Bayan abokina ya dawo daga, kasuwa ne sai matar sa ta dubeshi ta ce, yayana idan ka sami natsuwa, za muyi magana da kai sai ya dubeta cikin, natsuwa ya ce, to kanwata.
*
Bayan ya yi wanka ya ci abinci, suka dawo falo, ya dubeta ya ce, kanwata ina sauraronki dazun kin ce, zamuyi magana ko? Sai ta ce eh yayana.
*
Sai ta dubeshi a karon farko ta ce, yayana dazun ina sauraron freedom radio kano ne na ji wani malami yana cewa: Akwai wata rana wani sahabi yana tafiya sai ya ga dan uwansa sahabi sai dayan yake tambayar dayan, cewa haltazawwaj? Ma'ana ka yi aure ne? Sai dayan ya ce a'ah.
*
Sai dayan ya ga kamar dayan yanada kyamar yin, aure sai dayan yake ce masa
INNAH KAIRA HAZIHIL UMMA AKSARUHA NISA'I.
Ma'ana wanda ya fi kowa alkairi a cikin wannan al'ummar shi ne wanda ya fi kowa tara mata.
*
Don haka na ke maka kwadayin kasancewa cikin, maza mafiya alkairi na ke son ka karo aure, kuma a shirye nake dana biya maka sadaki.
*
Kuna ganin za a sami irin wadannan matan yanzu kuwa.?
No comments:
Post a Comment