*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 5 - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, March 7, 2018

*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 5

*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_

                           🐲

_THE DARK FOREST_

0⃣5⃣

© *ZAINUDDEEN ZAIN*

® _pen writers association_
✍🏾

08034840276

~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~


*Waiwaye*

_A shafin da ya gabata, mun ji yadda ya dace 'yan jarida su kasance, haka mun ji kalar marubuta da matakan farko da ya dace sabon marubuci ya bi domin ganin ya zama marubuci_

*ci gaba*

```
'mu kirostoci mun yi imani cewa Ubangiji shi ya halicci sammai da kassai da dukkanin halittu a cikin kwanaki shida. Kamar yadda yazo a littafi mai tsarki ```book of genesis``` *1:1-29*
Haka kamar yadda yazo wurare har bakwai a naku littafin'

'Eh naji wannan amma har yanzu baki sosa inda ke yin kaikayi ba.'

'Me kake so kace ne?' ta fada a lokacin da take kallonsa cikin idanu

'Kuna fadar cewa Annabi Isah Allah ne ya sauko daga sama in flesh domin yazo ya wanke zunuban duniya ta hanyar mutuwa kan cross'

'Sosai hakane, Isah Allah ne kuma ya mutu ne domin ya wanke zunuban duniya bayan kwana uku ya taso daga kabari'

'Idan haka ne a lokacinda Annabi Isah ya mutu din, wa ke kula da lamurran duniya?'

'Ubangiji mana. Allah uku ne amma daya ne, baka taba Jin trinity ba ne? Akwai God the father God the son da kuma God the holy spirit amma abu daya ne'

'Ko zaki iya kawo ayar da ta fadi haka a littafinku na ~Bible~?'

'Sosai zan iya
```first epistle of John 5:7```
*for there are three that bear records in heaven, the father, the word and the holy ghost and these three are one*'

'Wannan ayar da kika karanto daga littafin king James version ne'

'Eh daga gare shi ne'

'Ina zuwa ya fada a dai dai lokacinda yake komawa a mazauninsa ya dauko yar jakarsa ta ratayawa ya fara tono littafai da su Kadai ne sai laptop a cikinta. Cen ya fiddo da wani ~Bible~ na daban da wanda ke hannun Fate.
A jikin Bible din anrubuta *REVISED STANDARD VERSION OF THE BIBLE* bugun 1957
Sai ya budomata daidai first epistle of John 5:7 yace 'karanta'

Sai ta karanto kamar haka...

'there are three that bear witness'

Cikin damuwa da matsanancin sauri ta juya littafin ta sake karanta sunansa da ke jikin bango ta kuma kalli Ameer. Ta kasa hakuri tace 'anya kuwa wannan ~Bible~ ne'?

' kar dai ki gayamin cewa ko sunayen littafanku musawa kuke yi '?

Ya fada cikin murmushi

'Ki karanta shimfidar littafin wato preface zaki gamsu'

Bayan ta karanta sai yace 'me aka rubuta'?

'Sunce King James version na ~Bible~ yanada kurakurai kuma kurakuren sunyi yawa ta yadda dole sai anyi gyara shi ne aka yi shi wannan Revise standard version of the Bible domin fassararsa tafi kusa da ainihin ~Bible~ na asali'

'Haka ne' Ameer ya fada 'a littafai da dama manyan malaman kirostoci Sunce wannan ayar sam babu ita a ~Bible~ na asali.
Bugu da kari a littafinku an nuna Allah daya ne'

'Ko zaka iya nunamin'

'Sosai kuwa
Amma kafin imfara kawo maki nawu hujjoji bari infara rusa wadanda kika kawo.
Kikace Annabi Isah yazo nan duniya kuma a surar mutum a matsayinsa na Ubangiji ya kuma mutu domin ya wanke zunuban duniya ma'ana zunubin da Annabi Adam ya aikata na cin haramtacciyar itaciya cikin aljanna?'

'Sosai haka ne
Mun karanta a ~Bible~ cewa Ubangiji ba ya mutuwa
Misali
```Habakkuk 1:12 "are u not from everlasting, O. Long my God, my holy one who never dies"? ```

```1 Timothy 6:15-16" *and this will be made manifest at the proper time by the blessed and only sovereign, the king of kings, long of lords who alone never die. And dwells in unapproachable list whom no man has ever seen nor can see. TO him belong honour and eternal dominion Amen".*
(Jerussalam Bible)

'Wadannan ayoyin suna kokarin hasaso muna cewa lallai Ubangiji ba ya mutuwa. Kinga ko idan har Annabi Isah ya mutu ya taso to ba Ubangiji ba ne, nasan kinji cikon dayan ayar da tace ba wanda ya taba ganin Ubangiji kuma ba wanda zai iya ganinshi, Annabi Isah ba ganinshi Kadai ba ~Bible~ ya gaya muna har marinsa anyi.
Tambaya anan itace da ya mutu din wa ya tada shi?'

Har yanzu labarin bai fara ba Ku biyo ni

Dr. Zain

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad