Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su gaban kotu - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Tuesday, March 13, 2018

Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su gaban kotu

Assalamu alaikum
sabon posting daga shafinhausa

Jami'an NSCDC da na hukumar
JAMB sun kama ma su magudin
jarrabawa, za a gurfanar da su
gaban kotu

*Hukumar JAMB ta bayyana cewar an yi
nasarar kama ma su aikata magudin ne ta
hanyar amfani da na'urorin tsegumi dake
aika sako shelkwatar hukumar ta kasa

*Za a gurfanar da wadanda aka kama
gaban kotu domin girbar abinda su ka
shuka da kuma koyar da darasi ga ma su
irin halayyar
Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC tare
da ma'aikatan hukumar JAMB sun yi
bajakolin ma su aikata magudi a
jarrabawar UTME da ake rubutawa.

Kwamandan hukumar NSCDC, Patrick
Ukpen, ya gabatar da ma su laifin yau a
Abuja.

(shafinhausa)

Ya bayyana cewar biyu daga cikin
mutanen uku an kama su ne a
makarantar Baptist Academy dake Karu
a Abuja.

Ya kara da cewa, daya daga cikin ma su
laifin an kama ta ne saboda shiga dakin
jarrabawa da wayar hannu ta hanyar
boye ta a dan kamfai.

Jami'an NSCDC da na hukumar JAMB sun kama
ma su magudin jarrabawa, za a gurfanar da su
gaban kotu
"Mu na tsare da mutane uku da aka
samu da laifin aikata magudi a
jarrabawar UTME da ake rubutawa,
kuma sun aikata laifuka kamar haka:
Wata mai suna Joy Akpabio, ta shiga
dakin jarrabawa da wayar hannu, laifin
da ya saba da dokokin hukumar JAMB ,"
a cewar kwamandan.

(shafinhausa)

Ya cigaba da cewa, " Bayan mun yi ma ta
tambayoyi, mun gano abokin aikata
laifinta, Andrew, kuma shi ma mun
dakumo Shi ."

Kazalika, kwamanda Ukpen ya ce sun yi
nasarar kama wani mai suna Mista
Egwuonwu, saboda laifin karbar N1,000
daga hannun daliban dake rubuta
jarrabawar ba tare da wani dalili ba.
Hukumar JAMB ta gargadi ma su rubuta
jarrabawar a kan yin duk wani nau'i na
magudin jarrabawa domin, a cewar ta,
ta na ganin dukkan abinda ke faruwa a
dakunan jarrabawar UTME dake fadin
kasar nan ta hanyar amfani da
na'urorin tsegumi dake aike da faifan
bidiyo.
Hukumar ta ce zata gurfanar da
wadanda aka kama gaban kotu domin
su karbi bakuncin da zai zama darasi ga
ragowar ma su hali irin na su.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad