*DR.AHMAD*
39
*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻♀
Edit by Dota *Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*I*nnalillahi haba khadijatu toh kuma menene na kuka? kiyi hakuri kinji dama haka ne kowa ce mace da kalar yadda take yin natq laulayin, kiyi shiru kinji ina ke miki ciwo yanzu?"
"Mama babu inda kemin ciwo, kawai dai banijin dad'i ne."
"Toh Allah ya baki lafiya ai kuma yanzu ke dajin dai-dai sai dai idan Allah ya saukeki lafiya sannu."
A bincin su aminu ya jera musu kamin ya fice gidan su khadija sabida sam be san zaman gidan sabida babu abokan wasa amma gidan su khadija akwai.
Cin karo ya kusa yi da ita tafito daga toilet daga ita sai karamin tawul wanda iyakar shi cinyoyinta had'iyar miyau yayi jikake k'uttt kamin ya nufeta yana murmushi mai cike da ma'anoni daban-daban ya sakalata jikin shi tare da cewa,
"Babyna kin k'ara kyau da cika wallahi cikin nan yayi matukar yi miki kyau."
k'okarin zame jikinta ta keyi daga jikin shi shi kuma tuni ya fara sunsunarta yana lumshe idanuwa sabida kamshin sabulun da tayi amfani dashi, daurewa tayi ta biye mishi sabida tasan yayi hakurima sabida yanda yake da zalama tasan sam beda hakuri amma gashi yayi wajan kwana biyar sabida rashin lafiyar da tayi.
Kusan babu kalar shirmen da bemata ba sabida tsabar gigicewar da yayi, jiyayi kamar ranar ya fara saninta sabida irin samun nutsuwar da yayi akanta jikinta yayi zam-zam ta k'ara armashi har ya kasa gane farkon yinshi da na yanzu.
Cikin sanyin murya ya fara mata magana yayin da hannun shi ke cigaba da yawo ajikinta,
"Babyna kin gaji ko?"
"Uhumm..!"
Kawai ta iya cewa sabida gajiyar da tayi.
Ganin tayi shiru yasa shi cigaba da lalubarta da alama sake yi zai yi sabida ba karamin dad'i yajiba yanzu saima ji yayi kamar ya tsokano ma kanshi buk'atarta.
Cigaba da murzarta yayi har saida yaji ta sakar mishi kukan ta gaji sannan ya saura mata tare da rungumeta ajikin shi yana d'an jijjigata jikin shi saida yaga tayi lamo tana sauke nunfashi sannan ya tashi a hankali yana cewa,
"Bari in had'a mana ruwan wanka kinji ko..?!"
Tare suka yo wankan su har lokacin bebar lakud'ar jikinta ba ita ko kasala sai dai kawai tabishi da manyan idanuwan ta farare kal.
****
Sun jima tsaye kofar gidan suna jiran ganin yaron da zasu aika cikin gidan domin sam basu yadda da cewa wai wannan gidan nasu Ahmad bane, domin cikin suma akwai wa in da basu yarda da cewa Ahmad d'in likita bane.
Cikin ikon Allah saiga malam Mamuda zai shiga gidan domin tunda suka tare bezo yayi musu Allah ya sanya alkhairi ba, shine yaga yau tunda asabar ce yasan duk suna gida bari yaje.
Saida sukai kallon-kallon tsakaninsu kamin malam Mamudan ya mika musu hannu sukai musabaha domin shi yaga basu da niyyar bashi hannun da alama dai mamaki ne ya kusa kashe su.
"Kushigo mana kuzo mushiga ai sunanan ciki yau hutun karshen mako har Dr d'in ma nasan yana nan ciki."
Cikin sanyin jiki suka bi bayan shi, yayin da idanunsu keta yawo acikin gidan domin ba wata k'arya aka tsaraba agidan ammafa bak'aramin kyau yayi ba musamman da har yanzu yake kamshin sabon fenti.
Zaune suka taddasu d'akin Maman Ahmad na kusa da Maman shi yayin da khadija ke kwance acinyar Maman Ahmad d'in na mata matsar kafafu ita kuma Maman nata shafar gashin kanta tuni ita tayi barcinta sukuma hira kawai suke abunsu bazaka tab'a gane cewar suruka akewa wannan gatan ba.
"Sannu da zuwa Ahmad d'in da Maman kema malam Mamuda kamin idanun su ya sauka akan wa inda ke bayan shi.
Fuskar Maman babu wata damuwa sai dai tuni ta Ahmad ta canza dan haka komawa yayi kawai ya zauna tare da gyarama khadijan kafafunta wa inda ya sauke daga jikin shi yanzu.
Malam salisu ne ya fara magana cikin alhini da karayar zuciya yace,
"Dama mun zone domin muyi zumunci tunda kun yaddar damu sai kace ba jinin kuba."
Wani mugun kallon takaici Ahmad yayi mishi kamin yace cikin gadara,
"Ahh zumuncifa kace malam? kanaso kuyi shari'a da zumunci a gaban Allah kenan tunda har zaka iya zuwa wajan mu da sunan wai zumunci, koda yake kila ka manta irin korar dabbobin da kukai mana tare da yanke duk wata alaka datake tsakanin mu? kamanta ranar da ka dinga kiranmu da shegu karnuka kuma lalatattu dan kawai munje sada zumunci daku? ka manta ranar da kace mu d'auka bamu da sauran dangi acikin garin charanci sabida kun ruga kun ya femu? kun manta ranar da kuka tasani nida kanina kuka dinga tsine mana albarka da zagin cin mutunci ga mahafiyar mu kuma a gaban idanun mu?
Kamanta ranar da kake furta cewa kune kuka kashe mana mahaifi kuma kani agareku sabida kawai beyi muku d'in kunan daya saba mukuba?
Kun manta kace duk ranar da muka sake waiwayar charanci lallai sai kunyi sanadin ajalina musamman ni danake babba?
a hakan kuke tunanin zamu kuma waiwayarku harmu sada zumuncin?"
Ckin matukar sanyin murya ya furta,
"Ina yawan zuwa charanci ba tare da sanin kuba haka ma Mama sabida inaso inga ko zuciyarku ta sauya kunfara son mu, sai dai kash! kullum baku da aiki saina binmu da mugun kalaima na b'atanci da lalacewa, idan ban manta ba ko wata hudu da suka shige ankama yaronku musa yayima wata yarinya ciki, me kace a ranar? cewa kayi inama me sunan babane aka samu da laifin nan.
sabida haka kunga wannan ya nuna musu malam Mamuda wanda ya zabga tagumin mamaki da tsoran halin mutanen ya hanashi ko motsin kirki, Ahmad yaci gaba, to wannan shine uba agaremu nida k'anina bamu da kowa saishi shine ya tsaya mana haihuwar mune kawai beyi ba sannan daga karshe kun san gatan da yayi min wanda Ku kuka kekashe kuka kasa yimin? nasan baku saniba to wannan d'iyarshi ce ya aura min kamar yadda kukemin fatan inyima yaran mutane ciki to hakan be faruba sabida ya bani d'iyar shi tun kamin ta mallaki hankalin kanta, yanzu haka cikina ne na halal a cikin jikinta kuma ban tab'a shaye-shaye ba kamar yadda kuke min fata, ni _AHMAD BANI DA SAURAN WATA ALAKA DAKU_, dan haka kuyi gaggawar barin gidan nan kamin in had'aku da hukuma."
"Kai Ahmad gidan ku, nace kajiko gidan ku, nace iyayen naka zaka kai ga hukuma dan iya shege to inji kafara kaga yanda zanyi dakai..."
Cewar malam Mamuda da yayi karfin halin yin maganar, itako Mama ai kuka kawai take yi sabida jitai komai ya dawo mata sabo sannan bata tab'a tunanin shi Ahmad d'in ya rike abubuwan da suka faruba a baya ba.
Ahmad da takaici ya kusa kashewa share kwallar idanunshi yayi kamin d'auki khadija cak! daketa barcinta yasab'ata akafad'a yabar d'akin, gaba d"aya suka bishi da idanu domin har yanzu anrasa wanda zai kuma tankawa cikin su, saima sheshshekar kukan Maman dake tashi kadan-kadan cikin dakin.
Sunjima cikin shiru kamin sufara bata hakuri daya-bayan daya, tare da neman gafararta data yaranta duk da cewa sunga rashin sauki dagashi gurin *DR.AHMAD* d'in amma dai suna so ta yafe musu.
Malam salisu ne ya d'ora da cewa,
"Tabbas muncika azzalumai Habiba domin tun tasowar iro muke cutar dashi sai gashi duk da abinda muke mushi hakan besa Allah ya tabar da shiba sai ma yayi mishi d'aukaka sama damu, muna cikin wani hali munsan cewa alhakin kune yake bibiyarmu kuduba irin gidan da kuke ciki babu abunda kuka rasa, muko kullum cikin tashin hankali muke sabida yanzu tun a duniya Allah kefara sakayya dan Allah kuya femana kuyi mana afuwa tabbas masu hali irin namu nanan sunada yawa a duniya, munafatan Allah ya shirya su tunkamin lokaci ya kuremusu kamar yadda muka sami kanmu aciki kuyi hakuri Habiba muntub'a wallahi harga Allah kuma bazamu kuma aikata wani abuba makamancin wannan domin munga ishara."
Saida malam Mamuda yasa baki sannan tace ta yafe, aiko sukai ta godiya tare da cewa zasu kawo iyalansu domin suka waje.
MALAM Mamuda ne ya fara magana cikin farin ciki domin tabbas yajima yana fatan zuwan wannan ranar yacce,
"Tabbas mun godewa Allah daya nuna mana wannan lokaci munafatan Allah ya kuma kare zumuncin shi, gaskiya nayi farin ciki sosai wallahi na tabbata malam ibrahim shima zai yi farin ciki duk da yake kwance cikin k'abari Allah yaji kanshi yayi mai rahma."
Gaba d'aya suka amsa amin cikin jimami.
Malam Mamuda ya d'ora da cewa,
"Tabbas mutane da dama sukan aikata kuskure batare da tunanin kuskurene ba misali zaka sami yaron wani kaita zagi tare da aibatashi da munanan kalamai sai-dai sani ne da ba muyi ba amma a duk lokacin da kai hakan to tabbas mala'iku sukan maido da wa'innan muyagun kalaman ne akan iyalinka, shi yasa sai kaga kaima acikin iyalinka kasami me irin wannan halin koma fiye,
Haka kuma idan kayima iyalan wani kyakykyawan addu'a to tabbas saita sami naka iyalin sabida haka yaka mata mu kula sannan mudaina kullatar marayu domin dayawansu Allah baya tabar dasu kuma tabbas wataran sai kaci arzikinsu Allah yasa mugane.
Sannan ina iyaye masu tsatstsauran ra'ayi akan yaran su? kanada yaro namiji kuma baligi cikakken mabukaci amma ku hanashi aure harsai ya gama karatu ya sami aiki kuma ya gina gida yasai mota tsawon wannan lokacin kasan iyakar zunubin daya kwasarma kanshi? to karka manta kuma iyayenshi akwai naku kason na zunubin domin laifin kune duk wani abu da zai aikata
.
Yima yara k'ana nu fyad'e ya yawaita sabida haka aure da iyaye suke yi sabida wani buri nasu nada ban, yarinya zata nuna tana son aure amma iyaye suk'i yi mata sai tasami me kud'i ko kuma sai tayi zurfin karatu wannan kuskureni domin sha'awa babu abinda baza tasa mutun ya aika taba, misali yanzu shi Ahmad me yarasa?
Babu, itace amsar anyi mishi aure alokacin da ya bukata kuma gashi yayi karatun shi hankali kwance, yanzu inda ba ayi mishi ba mun san iyakar yaran da zai lalata? bamu saniba dan haka yaka mata mu iyaye mu kula tunkamin ranar da Allah zai tirkemu da tambayar yaya muka tafiyar da amanar daya bamu.
Bari muje sallah Habiba a sama musu abinda za suci kamin mu dawo zan shawo kan shi Ahmad d'in insha Allah."
Godiya suka yima malam Mamuda kamar zasu yi mai sujjada sabida farin ciki, a haka duk suka yi alwala suka fice, itako Maman kitchen ta shige domin ganin ta dafa abu me sauki wanda zasu ci......
*MAMAN KHADIJA*🙇🏻♀
No comments:
Post a Comment