BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 6 - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, March 7, 2018

BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_ Part 6

*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_

                           🐲

_THE DARK FOREST_


0⃣6⃣



© *ZAINUDDEEN ZAIN*

® _pen writers association_
✍🏾

08034840276


~dedicated to: Rumaisa'u Umar Geza~


*Qoute of the day*

_Frog's eyes never stop a cow from drinking_




*Waiwaye*


_A shafin da ya gabata, mun ji cewa Annabi Isah ba ubangiji ba ne, haka hujjar da kiristoci suka dogara da ita, ba makama ba ce, domin ayar sam ba ita a ~Bible~ na asali_



*Ci gaba*




'Ubangiji ne ya ya tada shi mana,' ta fada cikin nutsuwa da izza.

'idan da gaske shi ubangiji ne kuma ya mutu har na tsawon kwanaki uku, duniya a lokacin wanne hali ta shiga? me zai faru da sauran ubangizai guda biyun, inaga tun da kince duk daya ne dole suma mutuwa za su yi, kinga kuwa duniyar ta rayu ba ubangiji, maganar hankali ba zai dauka ba.'

Abdulsamad ne ke gayawa abokinsa Saddam cewa shi ko kusa ba zai iya jure yunwa ba, ya nemi abokin nasa da ya raka shi cikin garin domin ya samo dan abinda zai saka a ciknsa, 'abokina, dama nasan kai mai mugun ci ne, duka ko awa daya fa ba muyi ba da muka ci abinci a tasha kafin mu taso', 'wai ina ruwanka?'

Abdulsamad ya fada, 'idan za ka raka ni kazo mu tafi tun kafin lokaci ya kure, kaga driver ya fara aikin sauya tayar', 'ba inda xani, azo a kammala bana kusa.'

'haba abokina, zo muje mana', 'okay naira nawa zaka biya'? 'wallahi zan ci...don..ka manta yadda na samo kudin mota da kyar? sai da na sayar da wayata daya'. 'Na fasa, da nayi niyyar rakayar taka,' 'haba tau zo muje idan na hau kujerar shugaban kasa zan biya.' 'hahaha! muje, amma bari mu sanar da su', 'kar kayi, wadancen firarsu suke masifaffiya kuwa kaga kallonsu ne aikinta, duka ba zamu wuce minti goma ba, nasan zamu dawo kafin a kammala. ba damuwa.'


Dattijo da Aseeya sai suka dawo 'yan saurare da kallon Ameer da fate, inda driver yake kokarin saka jack ta kasan mota domin ya fitar da taya, bayan a jibge sifanu a gabansa.


'mun karanta a cikin littafinku,' Ameer ya cigaba, 'cewa Yahudawa da aka aika Annabi Isah a wurinsu, sun bukaci da ya xo masu da mu'jiza idan yana so suyi imani da shi, sai ya ce zai zo masu da mu'jiza irin ta Annabi Yunusa. Annabi Yunusa ya yi wa mutanensa wa'azi tsawon lokaci, amma mutane kalilan suka karba kiransa, sai ya fusata yayi yunkurin ya bar garin ya zuwa wani gari, kasancewar ubangiji bai bashi dama ba, akan hanyarsa sai kifi ya hadiye shi. yayi kwanaki uku a cikin cikin kifi (dare uku da wuni uku) yanayin addu'ah kana ubangiji ya fiddashi inda kifin ya amayo shi.'



tace 'eh! Haka labarin yake ko a namu littafin' (book of Jonah)


'bari na karanto daga littafinku.' Ameer ya fada


MATHEW 12:38-40. (Mathew chapter 12 verses 38 to 40). “ *Then certain of the scribes and of the Pharisees answered, saying”, ‘master we would see a sign from thee’. But he answered and said unto them, ‘an evil and adulterous generation seeketh after a sign; and there shall no sign be given to it, but the sign of the prophet Jonas: for as Jonas was three days and three nights in the whale’s belly; so shall the son of man be three days and three nights in the heart of the earth.’* (KING JAMES VERSION)

                  LUKE 11:29-30. “ *And when the people were gathered thick together, he began to say” ‘this is an evil generation: they seek a sign; and there shall no sign be given to it, but the sign of Jonas the Prophet. For as Jonas was a sign unto the Ninevites, so shall also the son of man be to this generation’* (KING JAMES VERSION)



'kinga idan Annabi Isah zai cika wannan, dole yayi wuni uku da kwana uku kan cross, kuma dole a isko shi a raye, kamar yadda Annabi Yunusa yake raye ba a mace ba.'


'a sharhin ~Bible~ munkaranta cewa ranar jumu'ah ce da misalin karfe shida na maraice abin ya faru, ~Bible~ ya sanar da mu cewa tun da safe ne ranar lahadi ya taso daga mutuwa, idan haka ne dare biyu kadai sai wuni daya yayi kan cross, kuma dole ya kasance a raye. wannan hujja ce kan lallai annabi Isah bai mutu kan cross ba.'


Nan ta dauki lokaci tana karatun hujjojin daga littafinta mai tsarki, a dayan bangaren kuwa Aseeya ce, sai daukar hotuna take yi, duk da hankalinta sarai yana kan firar da suke yi.


driver kuwa tuni ya cire tayar har ya fara canja wata.


Dattijo ne ya fahimci cewa su Saddam basa kusa, nan ya duba su ta gefen hanya kasancewar mai motar yayi parking ne a gefen titi daf da ciyawu, bai gan su ba, nan zuciyarsa ta darsa masa cewa a garin Dagoma suka shiga, ba tareda ya sanar da kowa ba ya sake dawowa,inda muhawara ke gudana tsakanin Ameer da Fate, wacce tuni jikinta yayi sanyi.


wasu mintuka driver ya kammala saka tayar, ya mayar da tayar da ta yi faci da sauran kayan aiki a bayan mota, sai ya umarci mutanen da su shiga, sai a lokacin suka fahimci cewa su Abdulsamad fa basa kusa, sai duban ta ina zasu fito ake yi. inda Aseeya ke cewa kawai  su wuce su bar su nan, a cewarta ya zaayi kan su biyu a batawa mutum kusan biyar rayuwa. driver yayi murmushi yace 'kiyi hakuri, ba zan iya barinsu ba, daga gareji, amanarsu ce aka bani, kuma alkawari ne na dauka cewa zan saukar da su a garin Kamba, kaddarar ubangiji kadai ta isa ta canja haka', bayan ta saki murmushi a cikin yanayi na hadiye fuska, tace, 'ai kaddarar ce yanzu ta hau kansu'...suna cikin musanyar zance, sai suka hango su tafe cikin gudu.


daga karasowarsu, suka bada hakuri, duk da Aseeya ta fara masifa, Dattijo ya shiga tsakaninsu. suka shiga, mota ta fara hanya.


bayan sun nutsu ne dajjijo ke nuna,musu kuskurensu na tafiya su bar mutane cikin irin wannan yanayin. suka kara bada hakuri.

ganin kowa a natse, sai Ameer ya juyo yace da Fate, 'ga hujjoji kan Ubangiji daya ne daga littafinku.'

'inajinka' ta fada, jikinta a sanyaye.


har yanzu labarin bai warware ba bare ya fara, ku biyoni kawai.
Dr. Zain

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad