*TA INA MA’AURATA ZA SU SAMI KWANCIYAR HANKALI?*
Assalamu alaikum
*KASHI KASHI HAR KASHI (5)*
*Ga Kashi Na Hudu (4)
*Amma bangare na uku a samun natsuwar aure shi ne tarbiyyar yara:* Hakika duk gidan da yaran cikinsa suka zamo masu nakasu wajen tarbiyya to wannan gida natsuwarsa mai karanci ce. Dalili akan hakan shi ne da yawa gida in yaran gidan ba su samu kyawun tarbiyya ba za a rika zargin juna tsakanin iyayen shi uba ya rika ganin laifin uwa ne. Ita ma tana ganin nasa. Da sannu za ka ga kwanciyar hankali da natsuwa ta kaura daga wannan iyali.
Hakuri da jarabawar da aka tsinci kai a zaman aure daga namijin har mace. Tabbas wannan ma wani jijjige ne a samar da natsuwar aure. Allah zai iya jarabtar auratayyarku da samun matsaloli na karancin abun hannu ko rashin lafiya daga daya bangaren ko daga yaranku ko matsalar dangi ta kowane bangare walau na mijin kona matar. Hakika idan ya kasance ba a samu hakuri da tawakkali ba. Aure zai zama kawai zamane ake yi ba natsuwa tare da shi.
A kalami na gana sai ubangiji (SWT) Ya ce: “..kuma muka sanya tsakanin kauna da tausayi…” To mun ga a nan ashe natsuwa ita ke jagortar kauna da tausayi har a samu zaman lafiya a aure.
Hakika ‘yan’uwa muna tafka kuskure wajen daukan wasu abubuwa a aure a kan suke samar da zaman lafiya. Mu sani a cewa ba wani zamananci ko al’ada da zai wanzar maka da zaman lafiya a auratayya face an gina shi a kan tsarin da za a samu natsuwa a cikinsa. Natsuwar kuwa dole ta kasance daga kowane bangare ma’ana duka bangaren biyu sun hada kai don samar da ita.
Inda za mu koma mu kalli zaman magabatanmu za mu fuskanci ba komai muke ba a zaman aure face dambarwa. A yau ‘yan bana-bakwai sun dage a kan cewa aurensu shi ne auren ‘yanci ka-ganni-kana-so, na-ganka-ina so!
✍🏽
shafinhausa
No comments:
Post a Comment