Bismillahir Rahmanir Rahim.
NI DA BODYGUARD DINA..
By khaleesi.
HELLO ma'abota karanta littafi, ga labarin Raees da Khadija wanda nace zan rubuta, a karshen littafina Atsakaninmu gashi Allah ya bani iko, ina fata zaku ji dadin wannan littafi, yours khaleesi.
1.
Tafiya sadaf sadaf yakeyi sai ya bada dakika biyu uku kafin ya kara taku, night vision goggles dinshi su suke taimaka mai wajen ganin inda yake takawa cikin duhun daren da koh taurari babu ballantana jaririn wata, har yadda numfashinshi ke fita yake controlling, cak ya tsaya dayaji kar yewar sanda yasan ba shi bane ya taka sandar sai ya nemi wurin boyewa sannan ya fara observing wurin dan sanin ko ya karaso inda mutanen da yake nema suke, tafiya yaji dap dap dap sai kuma aka tsaya kara yaji wacce ta tabbatar mai da cewa daya daga cikin kidnappers dinne ya dan zagaya dan fitsari,
"Samuel do quick na i need to take a leak too"
"Relax my guy them oga no dey nah"
"No bi that i know want the ppl to run away ne"
" we tie them well well, come i don finish"
Yana jin karan an ja zip sai tafiya dip dip ya mike tsaye ya fara tafiya a hankali Samuel ya koma gadi yana kallon wata bukka dan can nesa shi kuma dayan yana fitsari a jikin wata bishiya meh kauri, sai da ya bari mutumin ya shagala sannan ya afka mai wani abu ya sokamai a wuya take mutumin ya sume, a hankali ya tallaboshi ya jashi zuwa bayan bishiyar
"You don finish"
Beh yi wani tunani bah ya mike da sauri ya nufi meh magana, yasan yana da advantage dan shi yana ganin Samuel wanda baya rike da koh waya balle torch light, shima tsinke me dauke da poison ajiki ya coka mai sannan ya jashi zuwa bishiyar da dayan wand ya fara sokama wa yake, agogon hannunshi yayi ma seti alarm bayan minti 25,lokacin ne poison din ze sakesu su farfado, shi kuma by then yana fata ya bar wajen, luck dinshi ne mah ogan baya nan da sauran yan jagaliyarshi saidai biyun nan kawai
Duk da yasan baze samu kowa cikin bukkokin bah, saida ya shiga da sanda sannan ya bi duk bukka ya duba har yazo wacce ta sada shi da mutane guda biyu daure, suna ganinshi suka zare ido tare da matsawa baya, ko kuma kokarin matsawa baya ya lura dacewa kaffafu da hannaye duk daure suke, hannu ya dora samman bakinshi sannan ya fito da waya daga aljihunshi ya nuna masu wani mutum, lokaci daya su duka biyu sukayi ajiyar zuciya da sauri ya kwance su sannan ya musu jagora,
"Akawai wasu mutane cikin bukkokin nan ne"har sun kai kusa da dajin ya tamabaya
Girgiza kai kawai sukayi, kayan daya gani cikin bukkokin yasa shi tambaya, amma yanxu daya gano na yan fashin ne bukkokin yasan akwai matsala in suka dawo suka iske su saboda haka sai ya yanke shawarar raba jaha dasu shi yabi hanyar dake leading directly cikin gari dan su biyoshi su kuma subi hanyar da zata kaisu kauye na gaba in yaso sai ya fada a daukesu acan.
"Aa tare zamu tafi"
Daya ya fada tun kafin ya karasa fadan plan dinshi.
"Sorry but ku nake ba order ba the other way around bane, kuje can kauyen zansa azo a dauke ku ni kuma zan ja hankalin yan fashin"
Bayan sun bata time yana kokarin sasu su tafi amma sukaki, sai sukaji shewa ba shiri su duka suka fara gudu suka nufi titi direct, addua'r shi daya Allah yasa basuyi nisa da inda yayi parking van dinshi bah, dayake mutanen daya taimaka masu nawin jiki ne sun kara slowing dinshi down.
Sun fita daga cikin daji yanxu yasan sun kusa kaiwa titi headlights din mota kawai yake jira ya hasko koh zega direction din motarshi, magana da gudu yaji kusa kusa dasu
"Ku shiga gabana" ya fada musu sannan ya koma bayansu yana kokarin karesu daga bullets, bindigar shi ya ciro daga holsters dinsu dake daure kirjinshi sannan ya ciro karamar itama daga marikinta dake daure a guiwwar kafanshi, flash ya gani sannan ya kara ganin wani flash din haske.
"Ku kara gudu sun cin mana fah"
"Wai dama ba wani rescue team hakanan yusuf ya turoka"
"Ba lokacin explaining bane yanxu, yanxu lokacin gudu ne kaman hell hounds na binku a baya"
"Right zakuyi fast"
Ya fada yana kokarin maida wayarshi aljihu, bayan ya duba tracking device din motar a wayanshi yaga direction din da take, first shot din da akayi firing yasa su kara gudu shi kuma ya juya ya basu nashi shots din saida ya amayar da duka bullets din bindigoginshi dan ya watsa su kuma ya tsoratar da yan fashin sannan ya cigaba da gudu
"Key yana cikin motar ku tada motar koh ban karaso bah" ya fada masu da karfi dan sun kusan kaiwa cikin motar, sabon setin alburusai ya sama bindigarshi ya kara harbawa dan ya samu damar karsawa gurin motar kafin yan fashin su lura ya isa cikin motar, amma sai suka maida mai martani da nasu wankan bullets din
"Oh crap" yace dayaji zafi a left side of his chest tsaki yayi, wai a haka yasa bullet proof vest gashi bullet yayi penetrating har ya tabashi, amma yasan if hes lucky ciwon is not deep, fasa harbi yayi ya juya kuma harda kari ya kasa daga hannunshi balle yayi harbi harya kai motar wani bullet ya kara saminshi a shoulder blade sannan kafa, beh san meh yasashi murmushi bah amma yasan yaji dadi da Allah yasa yan fashin basu da saiti kaman yadda yake dashi yasan da saidai gawarshi yanxu tunda sune masu haskashi, saboda haka sai ya juya one last time yayi amfani da direction din da torch ke haskowa ya harba bindiga sabanin da dayake harbi kawai, wani murmushi ya karayi da yaji duka shots dinshi guda bakwai saida aka biyosu da ihu, alamin ya harbi target kenan, da kafa daya yayi hopping ya shiga mota sanna aka fara tuki,
"Nan zamuje" ya nuna masu wani address da aka tubuta jikin wata paper.
"Toh" kawai Alhaji Abdulrazaq babangida yace shi kuma Honourable Marwan isa turaki ya juyo yana tamabaya
"Ba a sameka bah?"
"A vest dinane ba matsala muje kawai"
"Indai an sameka toh zuwa wannan address yayi nisa ka fara ganin likita tukunnan"
"Am fyn kawai kuyi tuki fast but steady" yaji dadi a nijeriya ba a bada speeding ticket.
Ciwon kafarshi ya fara dubawa bullet din ya gurjeshi ne beh shiga jikinshi bah saboda haka ya daure gam, sannan ya cire vest din, true bullet din beh shiga deep bah dan yana ganinshi, bandage kawai yasa ya zagaye shoulder dinshi da chest sannan ya lalibo sabon riga cikin bag dinshi sannan yasa, tadashi yaji anayi beh masan yayi bacci bah koda ya bude ido gari ya dade dayin haske gashi kuma sun iso address din, da alamu har anzo tarban mutanen daya ceta dan yaga manyan motoci ga kuma na police.
"Kawu"
"Well done Raees,ni dama nasan cewa zaka iya ake cewa ayi inviting sojoji gashi kai one man ka dawo dasu"
"I was just doing my job"
"Kuma kayi da kyau"
Da wannan kawun nashi ya barshi ya nufi abokinshi senator marwan, shi kuma yasan meh ze biyo baya kuma Allah yasan baze iya going through it bah yanxu dan ji yake kaman an bashi kashi ga wani zafi daya isheshi, cikin motarshi ya shiga beyi tuki a hankali bah har saida ya ganshi a gidan daza a bashi taimako.
"Finally zanganki Asma'u".
No comments:
Post a Comment