Amina Muhammad wadda aka fi sani da Amina
Amal jarumar fina-finan Hausa ce da ta bar
kasar Kamaru zuwa Najeriya don ta ga jarumi
Adam A. Zango, don kuma ta fara yin fim, a
tattaunawar da jarumar ta yi da Aminiya, ta
bayyana dalilin da ya sa ta fara harkar fim,
matsalolin da ta fuskanta, nasarorin da ta cim
ma, soyayyarta da Adam A. Zango da kuma
yadda aka kusa kashe ta a Kasuwar Bacci a
Kaduna.
Jarumar ta kuma bayyana cewa za ta
iya sadaukar da rayuwarta don jarumi Adam A.
Zango. Ga yadda hirar ta kasance:
Daga farko za mu fara da jin takaitaccen tarihinki
Assalamu alaikum, sunana Amina Muhammad,
wacce aka fi sani da Amina Amal, an haife ni ne
a kasar Kamaru, a can na girma na kuma yi
karatu. An haife ni a Bamenda, Shiyyar Arewa
maso Yammacin Kamaru ne, amma na girma a
Douala, babba birnin kasar Kamaru. Na yi
makarantar GSS a Arewa maso Yammacin
Kamaru, sannan na yi sakandare ta GBS a
Douala.
Ga shi an haife ki a Kamaru, kin kuma girma
hade da karatu a Kamaru, sai kuma ga ki a
Najeriya, shin da ma kina da wadansu ’yan uwa
ne a nan Najeriya?
Ba zan ce ba ni da ’yan uwa a Najeriya ba,
amma dai inda na je a Najeriya ba ni da ’yan
uwa, duk da cewa ina da ’yan uwa a Najeriya,
amma a Yola suke da zama, amma lokacin da na
zo Najeriya a jihar da na zauna ba ni da ’yan
uwa.
Mene ne ya yi sanadiyyar zuwanki Najeriya har
ta kai ga kin sauka a wurin da ba ki da ’yan
uwa?
A lokacin da nake Kamaru wata rana sai na je
dakin wata makwabciyata sai na ga tana kallon
fim din Hausa, ba na kallon fina-finan Hausa a
lokacin, amma sai na zauna na kalli fim din, zan
iya tunawa sunan fim din ‘Hubbi’, bayan na gama
kallon fim din sai na fara sha’awar in yi fim, na
rika cewa ina ma ni ce jarumar cikin fim din, sai
na fara tambayar kaina ta yaya zan yi fim a
Kamaru, tun da ba a yin fim din Hausa a can, a
zahirin gaskiya jarumin fim din ya burge ni sosai,
na ce ina ma a ce wata rana in fito fim tare da
shi, daga lokacin sai na fara sha’awar zama
jaruma.
Wani jarumi ne ke nan?
Ba kowa ba ne illa Adam A Zango.
Kin ce ba kya kallon fim din Hausa sai a kan
‘Hubbi’ kika fara, to ta yaya Zango ya zama miki
jarumin da kika fi so?
E, to kamar yadda ka sani, ka san Adam A Zango
mawaki ne, duk da ba na kallon fim din Hausa
ina jin wakokinsa, kuma abin da ya sa nake jin
wakokinsa shi ne, suna yi mini dadi, sannan yana
sa Turanci a ciki, sannan ka san Kamaru ba wai
Turanci muke yi ba, amma dai akwai mutane da
yawa masu jin Turanci, don haka idan ya yi
Turanci sai abin ya rika yi mini dadi.
Yaya aka yi kika yanke shawarar zuwa Najeriya?
Ranar da muka kammala kallon fim din ‘Hubbi’ a
ranar da na koma dakina a cikin dare dai ban yi
barci ba, ina ta nazari, domin ban san ta yaya
zan bullo wa iyayena ba, hakan ya sa abin ya
rika damu na, idan na kwanta da rana sai in rika
mafarkin ina aktin, da daddare ma haka, kullum
dai ina cikin mafarkin ina aktin, sai abin ya fi
karfina sai na samu mahaifiyata na yi mata
bayani, sai ta ce mini ko na fara hauka ne, idan
na fara kuma in fada musu su kai ni asibiti, na ce
mata ban fara hauka ba, na dai yi musu bayani,
amma dai ba su ba ni goyon baya ba.
Abin dai ya fi karfina ya zamanto ko hira nake yi
da mahaifina to ina yi masa hirar Adam A. Zango
a ciki, haka ma dai mahaifiyita, abin dai ya fi
karfina har ya zama kamar zan yi hauka, to ka
san babu iyayen da za su so a ce ’yarsu ta
haukace saboda wani burinta na rayuwa. Bayan
sun zauna sun yi magana sai suka ce mini, tun
da abin da nake so ke nan to sun bar ni in zo
Najeriya in yi.
Daga nan sai kika shirya kika taho Najeriya ke
nan?
Bayan sun amince mini sai aka fara samun cee-
kuce a cikin danginmu, sai bayan kusan kamar
wata biyu na zo Najeriya, dalili kuwa shi ne abin
ya haifar da cece-kuce a wurin dangi, bayan sun
kammala tantancewa kuma na yi musu alkawarin
ba zan aikata duk wani mummuna abu ba, domin
sun san tarbiyyar da suka ba ni, don haka idan
har sun ba ni yardarsu to kada su ji komai, na
kuma yi alkawarin zan rike musu amana, hakan
ya sa suka sake amince mini in taho Najeriya,
suka ba ni guzuri mai yawa da zai rike ni zuwa
wani lokaci mai tsawo, sai na taho Najeriya.
Bayan zuwanki Najeriya ina kika nufa, kuma yaya
rayuwarki ta kasance?
Abin ba a cewa komai, kai ma ka yi tunanin
mutum ya je wurin da ba shi da kowa, ba shi da
dangin uwa bare na uba, ga shi ma ban ma iya
Hausa ba, na samu matsala sosai, a haka dai na
rika rayuwa.
Daga farko dai na sauka a Abuja, sai na ce a
kawo ni KD, kasancewar a lokacin nakan ji Zango
yana ambaton KD a cikin wakokinsa, bayan na
duba a intanet sai na fahimci KD na nufin
Kaduna ke nan, sai na ce a kawo ni Kaduna,
kuma a nan na sauka.
A cikin bayaninki kin ce lokacin da kika zo
Najeriya ba kya jin Hausa, to da wane yare kika
yi amfani da kika zo Najeriya har kika zo
Kaduna?
Ka san ta Arewacin Kamaru an fi yin Hausa, duk
da dai ina dan jin Turanci, to a Najeriya wani
lokaci ko na hadu da Hausawa in na yi musu
Turanci ba ji suke yi ba, sai mu rika yin na bebe,
to a haka na rika fahimtar mutane, a wani wuri
ko ina so in yi magana ma sai in fasa, su kuma
idan sun yi Hausa ba zan ji ba.
A kasar Kamaru da ma can kina jin Turanci ke
nan?
A’a, a wurin da na tashi dai Faransanci ake yi,
kuma makarantar da na yi duka da Faransanci
aka koyar da ni, amma daga lokacin da na fara
tunanin in zo Najeriya sai na tafi wata makaranta
a Kamaru da ake kira Linguistic Centre, sai na yi
rijista, sai ya zamo idan na dawo daga
makarantar boko da rana, idan yamma ta yi sai in
tafi makarantar koyon harsuna, kuma ana ba ni
darasin awa biyu ne kowace ranar da na je
daukar darasi, a cibiyar ana koyar da duk wani
yare na duniya, amma sai na zabi Turanci saboda
bayan na yi bincike na gano cewa Turanci shi ne
yaren da ake amfani da shi, sai na ce bari in koyi
Turanci, kuma a lokacin na ji an ce Hausar
Najeriya ita ce gangariya a cikin duka Hausar da
ake yi a duniya shi ya sa na ce ba zan koyi
Hausa a Kamaru ba, na ce idan na zo Najeriya na
koyi Hausa a nan.
Bayan kin zo Najeriya kin dauki tsawon wani
lokaci kafin kika hadu da Zango?
Na yi wata biyu zuwa uku kafin in hadu da Adam
A. Zango.
Me ya faru a ranar da kika fara haduwa da
Zango?
Ranar da na fara haduwa da Zango na yi farin
ciki sosai, a ranar da muka hadu wanda ya hada
ni da shi ya buga mini waya ya ce in shirya zan
hadu da Zango yau, bayan na shirya sai ya zo
muka je wurin da Zango yake, to ina sauka sai
aka ce in zo in gaishe shi, na je na same shi, sai
na ce kai ne Adam A. Zango? Sai ya ce ba ga ni
nan kina kallona ba? Sai na duba hotonsa da ke
kan wayata, sannan na kalle shi, sai na ce anya
kai ne kuwa? Sai ya ce wallahi ni ne, sai na ce
masa to shi ke nan, sannan na ce masa na zo
daga Kamaru don in yi Hausa fim, kuma kai ne
dalilin zuwana Najeriya, na ce kuma ni babbar
masoyiyarsa ce, sai ya fashe da dariya, ya ce ta
yaya za ki yi fim bayan ba kya jin Hausa? sai na
ce masa, idan har ya yi mini alkawarin zai yi mini
fim, to na yi masa alkawarin zan koyi Hausa, sai
ya ce to shi ke nan, sai na ce masa ya ba ni
wata biyar sai ya ce mini to ya ba ni shekara
daya, sai na ce masa to shi ke nan.
To, a wata nawa kika koyi Hausa?
A cikin wata biyar na koyi Hausa, amma a
lokacin idan na yi magana sai kowa ya yi dariya,
duk da cewa har zuwa yanzu ban kware sosai
ba.
Wadanne matsaloli kika fuskanta a lokacin da
kike koyar Hausa?
Na dan fuskanci wadansu matsaloli, kodayake ta
wani bangaren zan iya cewa ba matsala ba ce,
saboda idan zan yi magana zan iya in zagin
mutum, a wurina kawai kalmar ta yi mini dadi ne,
kai kuma za ka ga kamar zagi ne, amma a
wurina ba haka ba ne, sannan idan na je wurin
mutane zan ga ana ta magana ni sai in zauna in
rika kallon su, amma ba na iya magana, ko ana
cinikin sayar da ni ne ma ban sani ba.
Bayan duka wadannan abubuwa sun faru, to yaya
kika ji da aka ce za ki fara fitowa a fim?
Fim dina na farko shi ne ‘Amal’, kafin in yi ‘Amal’
an ba ni labarin fim din, inda ya yi kamar wata
shida a hannuna, domin sun san ba na jin Hausa
sosai, amma sun san ina karatun Hausa, sai suka
ba ni (script) suka ce in rika karantawa ina gwaji
(rehearsals) a gida. A ranar da aka ba ni (script)
din ban ma iya barci ba, saboda murnar cewa
burina ya kusa cika, haka na rike (script) har
tsawon wata shida, in fada maka a takaice dai na
haddace fiye da rabin (script) din, idan an zo
wuri ba sai an fada mini ba, domin na san abin
da aka rubuta a wurin.
No comments:
Post a Comment