KANA DAYA DAGA CIKIN WANDA WAYARSU BATA RIKON CHAJI KO DAUKAN ZAFI, TO GA YADDA ZA AMAGANCE MATSALAR - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Saturday, May 26, 2018

KANA DAYA DAGA CIKIN WANDA WAYARSU BATA RIKON CHAJI KO DAUKAN ZAFI, TO GA YADDA ZA AMAGANCE MATSALAR

Assalamu Alaikum barkanmu da war
haka, kuna tare da Muhammad Abba
Gana daga DUNIYAR FASAHA yau
insha Allah zamu tattauna kan
Matsalar shanyewar batirin waya da
sauri, zamanin mu na yau matsalar
shanyewat battery ya zama ruwan
dare, kayi cajin wayar ka amma sai
ya ringa sauka kamar ruwa ake diba
a cikin bokati wannan yana
faruwane saboda wasu dalilai wanda
da izinin ubangiji zamu taimaka
wurin kawo muku manyan
makasudin da suke kawo wananan
matsalar da kuma hanyar magance
su cikin sauki.

RAGE YAWAN APPLICATION
(UNINSTALL UN-USEFULL APP)

Abu na farko shine yawan tara
application a waya wanda basu aikin
komai kuma baka aiki dasu, sau
dayawa mutane na tara wasu
application wanda basu ma san aikin
me suke yi ba kawai suna sa wane
saboda a ga suna da abubuwa a
waya ko kuma dan ado, hakan yana
shan batter saboda akwai wasu da
dama wanda sukanyi aiki a
larkashin kasa ba tare da ka sani ba,
yana da kyau mutum ya kayyace
applications da yake aiki dasu
saboda wasun su suna zukan batteri
ne ko kuma su janye maka yan canji
da kake dashi, yana da kyau mutum
ya cire wanda baya aiki dasu ko
kuma bai san aikin me sukeyi saboda
mahancewa ko kuma kujewa
wayannan matsalar.

TSAYAR DA APPLICATION (STOP
RUNNING APPLICATIONS)

Abu na biyu shine sanin wasu
application da suke shanye batir da
wuri a waya, sannan mene ne
amfanin su a lokacin da suke yin
aiki. Domin a wani lokaci mutum zai
iya kunnan application a wayarsa
kuma bai rufe su ba sannan ya sake
bude wadansu. To barin application
a kunne suna aiki a karkashin kasa,
na daga cikin abubuwan da suke
janyo karewar batiri da sauri. domin
sanin wasu applications da suke aiki
a karkashin kasa kuma ya yanayin
jan batiri da suke yi, mutum na
bukatar ya shiga settings sai ya je
zuwaga Battery. Wannan zai sa kaga
wadansu Applictions ne suka fi zukar
cajin batir da kuma shin wadanda
kake son yin amfani da su, ko kuma
wanda dole wayar tana da bukatar
su domin ta yi aiki, Idan Application
na wayar ce ke butakarsu to dole ka
yi hakuri ka barsu su ci gaba da
aikin su, domin hana su aiki zai
kawo matsala da katsalanda ga aikin
da ita wayar take yi. Amma idan
application ne wadanda suke
taimaka maka wurin yin aiki to sai
ka danna force stop. Akwai
applications masu dinbin yawa a
Play Store wadanda suke taimakawa
wurin sanin hakikanin mai yake
faruwa da batirin wayar mutum. Mu
a nan zamu iya ba da shawarar
saukar da GSAM Battery Monitor.
Idan ka saukar da wannan
Application, zai iya daukan kwanaki
yana binciken lafiyar batirin wayar
da kuma abubuwan da suke zukarsa.
Bayan ya kammala zai baka
cikakken bayani dangane da batirin.
Canza sabon Batir Wani lokaci zaka
iya samu cewa wayar da mutum ke
amfani da ita tsohuwa ce. Misali
kamar yadda da yawa daga cikinmu
suke siyan wayar hannu wacce wani
yayi amfani da ita, To gaskiyar
magana shi ne, idan har ka duba
cewa babu irin wadancan
Application masu aiki a karkashin
kasa masu zuke batir, kuma ka rage
hasken fuskan wayar, to magana ta
gaskiya shi ne yana bukatar sabon
batir. Kamfanonin da suke yin
batirin waya sun ce ana iya yin
cikakken cajin waya har sau dubu
daya (1000) kafin ya fara saurin
zukewa, amma shima hakan ya
danganci wani kamfanin ne yayi
batir din. Idan ka yi dace wayar ana
iya cire batir din ta, to babu matsala
sai a cire batir din ka canza shi da
sabo, amma kuma idan irin wayoyin
da ba a cire batir din su ne, to yana
da kyau ka kaiwa kwararru ko ma
kamayar da wayar zuwa ga
kamfanin da suka kera ta idan a
garin da kake akwai su, su cire maka
batir din su mayar da sabo. A wurin
canjin batir akwai korafi da jama’a
suke yi musamman idan suka sa
sabon batir sai su ce shima sabon
baya dadewa, ko kuma yana dadewa
bai cika ba. To akwai matsaloli guda
uku ga hakan. Matsala ta farko shine
ba a duba karfin batirin da wayar
take bukata ba. Domin bakin da ake
zura batir yayi daidai da naka amma
kuma karfin da wayar take take
bukata bai kai ba, matsala ce, kuma
idan batir din bai kai karfin da
wayar ke bukata ba zai yi saurin
zuke batir din. Matsa ta biyu Cajar
Wayar bata aiki yadda ya dace
Matsala ta uku kin yin caji da sauri,
shima yana da alaka da sabon
batirin da ka saka, misali ka saka
batirin da yake da 1200mAh kuma
sai ka sami cajar wayar da take sa
karfin 240mAh to yana nuna maka
cewar sai kayi jira har sau uku kafin
ta cika. Wadannan matsalar abin
lura ce kuma haka ake magance su.
Shi yasa yake da kyau sosai duk
lokacin da mutum ya ke son sayan
caja to ya tabbatar ya sayi ta
kamfanin wayarsa. Wani lokaci
amfani da caja mai karfin da tafi na
batiri shima matsala ne, domin zai yi
saurin kona sinadaran da suke ajiyar
caji da wuri, kuma gasa batirin da
sauri zai iya lalata shi ba zai jima ba,
kuma wani lokaci koda ka samo
cajar asali da aka yi domin wayar sai
ka ga bata iya yin komai a wayar.
Tsarin wayar yana amfani da batir
sosai Daya daga cikin abin daya fi
komai zukar batir shi ne Android
System. Android System shine babbar
application da take taimakawa wayar
domin ta yi aiki kamar yadda ya
kamata, tsayar da ita tamkar tsayar
da wayar ne ko kuma lalata ta. Ga
ka’ida na wadanda suke yin OS na
Android sun ce Android System bai
kamata ya wuce kashi ashirin da
biyar cikin dari (25%) na batirin
wayar ba. To amma idan aka samu
ya wuce haka, to ya nuna cewa
akwai matsala sosai, kuma babu
wata hanya da za a iya magance
wannan sai ta hanyar ragewa wayar
babbar manhajar da ita kanta wayar
take amfani da ita. Misali ace wayar
tana amfani da android Lollipop ne
sai ka dawo da ita zuwa Android Kit-
kat. Akwai hanyoyi da dama da ake
amfani da su wurin ragewa OS an
Android daraja da ake samu a
shafukan intanet, kawai ka rubuta
downgrade (sunan wayarka). Yin
hakan shi ne kawai mafita, amma mu
sani hakan kuma na matsayin
kayiwa wayar flashin ne, amma
wani abun jin dadi koda lokacin da
kake kokarin rage mata daraja an
sami matsala zaka iya yin factory
reset, wayar zata dawo daidai.

MATSALA TA UKU:

Google Play Services yana zuke batir
Google Play Services shima yana
daga cikin abubuwan da suke zuke
batir da wuri, abin haushi shine ba
zai yiwu ka tsayar da shi ba, domin
shi ke taimakawa wurin ganin
applicaions da suke cikin wayar suna
da alaka tsakaninsu da wanin su,
musamman ta wurin musayar
bayanai. Amma duk da haka akwai
yadda zaka iya rage wannan cajin.
kaje Settings saike latsa Applications
sai kaje zuwa ga All sai ka danna
Google Play Services sai ka taba
maballin Clear cache. Wannan zai
goge duk wani abubuwa da wannan
application ta ke tattare da su
sannan ta fara gina wadansu, wanda
wannan zai rage shan batir, zaka iya
sake yin haka kowani farkon wata.

DAKATAR DA AUTO-
BRIGHTNESS (CANCEL
AUTO-BRIGHTNESS)

Dangane da matsalar hasken fuskar
waya, kusan da yawa daga cikin
matsalar mun fi barin cewar wayar
mu ta rinka lura da haske da kanta
wato auto brightness a turance.

Barin wayar ta rika lura da shi da
kanta ba shi ke nuna hakan ba daidai
bane. Matsalar a nan ita ce, sensor
da yake jikin wayar yana aiki tukuru
wurin sanin wani wuri ita wayar
take, shin akwai haske mai yawa ko
kuma babu, idan akwai haske to sai
fuskar wayar yayi duhu, idan kuma
akwai dubu a wurin sai ta yi haske,
saboda haka barin sa a auto yana
taimakawa wurin ganin cin batir.
Yadda idanun mu suke bukatar haske
ya sha banban da na kowa, saboda
haka yana da kyau ka tsayar da
wayar ka zuwa hasken da ka san shi
ya fi dace da kai, kuma hakan zai
taimaka wurin ganin batirin baya
karewa da wuri.

RAGE DADEWAR
DISASHEWAR HASKEN
WAYA (REDUCE DISPLAY
TIME)

Kamar yadda muka sani hasken da
ke fita ta fuskan waya na daya daga
cikin manyan abubuwan da suke
kawo shanye batir musamman
wayoyin Android.

Saboda haka a
lura da tsawon lokacin da wayar take
yi cikin haske sosai yana da amfani.
Lura da tsawon lokacin yana da
matukar muhimmanci domin a wani
lokaci wasu sukan bar hasken ya kai
kusan minti biyar ko goma kafin ta
tafi barci.

To kamar dai yadda na
fada dadewar hasken fuskar wayar
yana zukar batir sosai. Yana da kyau
mu rage daga dogon lokaci zuwa
gajere, misali daga minti guda zuwa
dakikoki ishirin ko kasa da haka.

zai
taimaka wurin kara rage shanyewar
batirin waya. Lura da ‘yan kanzagin
app wanda aka fi sani da widgets
turance da masu aiki karkashin kasa
Wadannan Application da ake kira
da Widgets su wakilan application ne
da suke tsayawa a fuskar wayar
mutum suna sanar da shi wadansu
al’amura da asalin manhajar take yi.

Misali manhajar duba yanayi, wato
Weather App, application ce mai
zaman kanta amma kuma wadanda
suke yinta sai su yi mata dan kanzagi
(widgets) wanda zai wakilci shi
babban da bai bukatar kodawane
lokaci sai an budeshi za’aga abin da
ke ciki. irin wadannan applications
kasancewar akwai guda daya ko biyu
nasan mutum ba zai damu ba, amma
yana da kyau mu sani cewar irin
wadannan applications suna aiki ne
a karkashin kasa domin aiwatar da
ayyukansu. To idan mutum yana da
su da yawa a cikin wayarsa to ya
sani yana saurin shanyewar batiri.

Saboda haka, irin wadannan
applications irin na labarai masu
neman shiga yanar gizo da yin aiki
ta karkashin kasa yana da kyau a
ciresu. Haka irin application da suke
bukatar yin update kodawane lokaci
suma suna da matsalar cin batiri
wani lokaci yana da kyau mutum ya
tsayar yin automatic update na
wayar sa ya sa shi zuwa wani
ayyanennen lokaci kamar sau daya a
wata. Shima hakan zai taimaka
wurin rage shan batiri.

Wannan su ne dan kadan daga wasu
abubuwa wanda muka ga suna daga
cikin musabbabin shanye karfin
wutar batiri, kana da wata matsala
ko abun cewa? Mu tattaunata a
wannan wuri! In kuma ka samu
wannan post da bansha’awa taimaka
ka turama yan uwa da abokan atziki
dan su amfana.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad