YADDA AKE BUDE SIM CARD DIN DA AKAYI BLOCKED DINSA - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Saturday, May 26, 2018

YADDA AKE BUDE SIM CARD DIN DA AKAYI BLOCKED DINSA

yau kuma mun zo muku da wata
kasidar da zata bayyana muku
hanyar da zaku bi domin bude
kulallen layinku na waya wato
“Blocked Sim Card”.

Sanin kowa ne da zaran an kulle
maka layinka na waya to hanya
daya tilo da zaka bi domin bude
layin shine ta amfani da lambar
PUK, wacce ke rubuce a jikin “Sim
Pack” dinka. Sau da yawa zaka
samu wasu mutanen gashi an kulle
musu layin amma kuma basu da
“Sim Pack” din a wajensu, ka ga
kenan basu da lambar da za su yi
amfani da ita domin bude layin.
Wasu mutanen suna hakura ne da
layin sai su sake wani sabo, wasu
kuma sukan yi “Welcome Back” ne
da wani sabon layin. Yau mun zo
muku da wata hanya mai sauki da
zaku bi kai tsaye domin bude
layukanku idan an kulle muku, ba
tare da kun yi amfani da “Sim pack
” na layin ba.

Domin bude layinka da aka
rufe, sai ka bi wadannan matakan:

1. da farko dai ka tabbatar ka sanya
layin a cikin wayar da idan kulle
layi bata wuce sai idan an bude
(kamar irin Nokia da dai
sauransu).

2. Daga nan sai ka sanya wadannan
lambobin: *22233421# sai ka sanya
OK.

3. Daga nan za’a baka dama domin
sanya sabon PUK din.
4. Sai ka samo biro da takarda ka
tabbatar ka dauki lambar da ka
sanya a matsayin sabon PUK din
naka domin ita ce zaka yi amfani
da ita a gaba idan bukatar hakan
ta taso.

5. Ita wannan lamba mafi yawancinta
zaka ga guda takwas ce (8), ka
tabbatar lambar da ka zaba a
matsayin sabon PUK dinka ta kai
guda takwas.
Da fatan wannan kasida zata
amfane ku. Ku ci gaba da kasancewa
tare da mu domin samin irin
wadannan kasidu dama Karin haske
akan wani abubuwan da suka shige
muku a duhu. Fatanmu dai shine a
ci gaba.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad