Wani matashi, Saliu Ladayo, mai shekaru
24, ya kashe budurwar sa, Confidence
Nwamaka, ta hanyar daba mata wuka a
ciki.
Saliu ya kashe Nwamaka, mai shekaru
19 dake rubuta jarrabawar kammala
sakandire, rabar Talata bayan wani
sabani ya shiga tsakanin su.
Jaridar Sahara Reporters ta rawaito
cewar lamarin ya faru ne a layin
Falodun dake unguwar Oshinle a garin
Akure, babban birnin jihar Ondo.
Wani shaidar gani da ido ya ce
masoyan sun dade tare duk da suna
yawan samun sabani saboda Nwamaka
na yawan zargin Saliu da cin amanar
soyayyar su.
Matashi ya burmawa budurwar shi wuka saboda
tana zargin sa
Shaidar ya ce masoyan sun kaure da
fada bayan cacar baki a tsakanin su
kuma kafin jama'a su kai agaji tuni ya
burma mata wuka. Nwamaka ta mutu
yayin da ake kokarin garzayawa da ita
asibiti.
Daga baya ne Saliu ya shaidawa jama'a
cewar, zagi da tsinuwar da Nwamaka ke
yi masa a kan kula wasu 'yan matan ya
hada su fada.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar
Ondo, Femi Joseph, ya tabbatar da
faruwar lamarin tare da bayyana cewar
tuni sun kama matashin kuma tuni ya
amsa laifin sa.
Iyayen yarinyar sun roki 'yan sanda da
su gudanar da binciken kwakwaf tare
da tabbatar da na bi masu hakkin kisan
diyar su.
@ naij.com
No comments:
Post a Comment