Guji aikata
wadannan abubuwa 5 bayan cin
abinci.
Akwai abubuwa da mutane ke yawan yi
bayan sun gama cin abinci kamar kishingida
ko yin barci da sauran su.
Da dama daga cikin abubuwan da aka saba
yi bayan cin abinci na da dadin aikatawa
amma ya zama dole a guje su don kare
lafiya.
Masana sun ce aikata hakan na da matukar
hatsari kuma yana iya haifar da matsala ga
lafiyar mutum.
A guji aikata wadannan abubuwan guda 5 da
zarar an gama cin abinci:
1) Shan sigari: Sigari nada sinadarin
”nicotine” wanda ya ke haifar da ciwon daji
da hunhu.
Wannan illa ta sigari tana zama ninki goma
idan aka sha sigarin da zarar an gama cin
abinci. Har wayau shan sigari bayan gama
cin abinci yana hana narkewar abincin da
wuri. Idan ya zama dole sai an sha sigarin
to a bari sai bayan kamar sa’a 2 (2 hours)
bayan gama cin abincin.
2) Cin ‘yayan itatuwa: ‘Yayan itatuwa na
dauke da sinadarai da suke daukan tsawon
lokaci kafin su narke su bi jikin dan adam.
Shan su kafin a ci abinci zai bada damar
amfana da sinadaran gina jiki da suke dauke
da su.
Shan su kuwa bayan gama cin abinci na
jinkirta narkewan abinci yana kuma gadar da
zafi a zuciya da kuma yawan gyatsa.
3) Barci: Mutane da dama na yawaita yin
barci da zarar sun gama cin abinci wanda
hakan na sa kumburin ciki kuma yana sa
barci na babu gaira babu dalili a lokutan da
basu kamata ba.
Bincike ya nuna cewa masu yawan yin barci
da zaran sun gama cin abinci sun fi saukin
samun cutar bugun zuciya (stroke).
Yana da kyau a dakata akalla sa’a 2 bayan
cin abinci kafin a yi barci.
4) Wanka: Yin wanka da ruwan dumi bayan
gama cin abinci yana tsinka jinin jiki wanda
hakan na hana jini isa ga tumbin dan adam.
Hakan yana kawo cikas ga narkewan abincin
da aka gama ci.
5) Shan Shayi: Shayi na da muhimmanci
amma shan sa bayan an gama cin abinci
yana kawo karancin sinadarin ”Iron”.
Hakan na iya sanya jiri da rashin kuzari da
gajiya. Har wayau karancin ”iron” na iya
kawo cutar (anaemia).
Post Top Ad
Your Ad Spot
Sunday, May 27, 2018
ABUBUWA 5 DAKE KAWO ILLA GA LAFIYAR DAN ADAM BAYAN CIN ABINCI
Tags
# Kiwan lafiya
About Arewa Tricks
Templatesyard is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of templatesyard is to provide the best quality blogger templates which are professionally designed and perfectlly seo optimized to deliver best result for your blog.
Kiwan lafiya
Category:
Kiwan lafiya
No comments:
Post a Comment