Ta tabbata a rayuwarnan wasu mutanen
gaba suka baiwa abin kunya, inda a nan
ma an kama wani Uba mai suna Femi
Adelegan da Dancikinsa Daniel Adelegan
da laifin satar kudi naira miliyan biyu da
dubu dari hudu, mallakin wani
Maigidansu.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta
ruwaito Femi mai shekaru 61 da Dansa
Daniel mai shekaru 30, dukkaninsu
mazauna unguwar Ori Oke, yankin Magodo
dake jihar Legas sun gurfana a gaban wata
Kotun majistri dake garin Ikeja, inda ake
tuhumarsu da laifin hadin baki, da kuma
aikata sata.
Dansanda mai shigar d akara, Sufeta
Raphael Donny ya bayyana ma Kotu cewa
Uba da Dan sun aikata laifin ne a tsakanin
watan Agusta na shekarar 2015 da watan
Oktoba na shekarar 2017, a kamfanin Deva
Access and Empowerment International
Ltd, inda suke aiki a matsayin jami’ai
masu bada bashin kudi.
Gudumar Kotu
“Bayan da kamfanin ta gudanar da bincike
kudadenta, sai ta gani an batar da kudi
naira miliyan 2.4, daga nan ta kai kara ga
Yansanda, inda Yansandan suka kama
wadanda ake zargi, su kuma suka tabbatar
ma Yansandan cewa su suka saci kudin.”
Inji Sufeta Donny.
Sai dai majiyar hausatech, ta ruwaito
wadanda ake tuhumar sun musanta zarge
zargen, inda bayan sauraron dukkanin
bangarorin, Alkali mai shari’a A.O
Adeboye ta bada belin kowannensu akan
kudi naira dubu dari biyar tare da mutane
biyu da zasu tsaya musu akan kudi
N500,000.
Daga nan kuma mai shari’a ta dage cigaba
da sauraron kara har sai ranar 22 ga
watan Mayu na shekarar 2018.
No comments:
Post a Comment