Assalamu alaiku
Zuciyarkita zama takarda, tawa ta zama bir
in rubata miki shafin kauna Kizama kofa na
Zano makulli, mu hadu mu bude kofar
soyayyyar lambun zuciyata! Na kasa tsaye
na
kasa zaune a lokacin da na fara ganin ki a
cikin taro , kin fita daban kaman wata daren
sha biyar!
Ya madarar zuciyata, ki zamo ciminti in
zamo bulo mu gina gidan
Quana a filin soyayya.Watau yau da na tashi,
sai na ga rana ta taso ta haske nan din nan
amma duk haskenta ba kai hasken fuskar
da haske zuciyata,domin ni a zuciyata
Hasken fuskar abun quana ta yafi duk
hasken raina Ki zama petur na zama inji mu
hadu
mutaa da lantarkin qaunaya shiba ta na baki
filin zuciyata ki shuka aduk wani lungun da
sako bushiyar so a kauna don mu sami
inuwar da zamu zaunamuyi soyayya.
Kece madubi abar dubawata duk safiya, kin
zamo min tamkar fetur a mota, rayuwata
bake
tamkr lami ce ya rabin raina
Ke ce makwarariyar madarar zuciyata,
wadda da na sha za ta
haska ka zuciyata ta yi fari.
Rayuwata babu ke tamkar wayar da chaji ce,
kuma babu layi, a mace ba amfani.Kunne ya
kur mance saboda rashin jin kallamen
quanar ki kullum, baki ya daina magana dai
dai saboda rashin begen zumar rayuwata
kullum.Ta tsagwaron zallar tsabar kwayar
tsokar zuciyata, idona zai makance saboda
rashinganinki a yau da kullumYa gangariyar
madarar zumar da batada gauraye, ya
tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske
zuciyar masoyinta. Idona ya bude ya ga
haske irin na walkiya don ya gan ki. Ziciyata
na shan lagwadar zuma da madarar
kaunaIdon
basira lafazin rayuwata
Alfijirna quana ya keto, tsuntsayen soyayya
sun tashi su na
yayo a sararin samaniyar zuciyata Ya fankar
da ke juya zuciyata, zan zamo kwale kwale
ki shigo bu haukan kogin so, in zamo katifa
ki zamo gado a cikin dakin kauna.Hadarin
begen ki ya hado, guguwar sonki ta taso, sai
ruwa mai karfi ake yi na kaunar ki afilin
zuciyata.Gaisuwa daga kamfanin so, harabar
kauna,gida mai lambar zuciyata layin begen
ki, zuwaga rabin rayuwata.ya zare da allurar
da ta dinken zuciya ta, bazan taba daina
sonki ba har sai wutar lantarki ta zauna a
nijeriya. ya majaujawar zuciya ta, zan zama
guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu cikin
rijiyar soyayya. Ya tsokar zuciya ta, zan so
ace ki zama furain zama nono mu hadu a
kwaryar soyayya.Ya sahiba ta ki zama
fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu
ta da tsuntsun soyayya.Ya masoyiyata ki
zamo bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta
kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar
da ke.Ya masoyiyata, ki zamo hanta
inzamo jini, muga mai raba mu. Ludayin
kaunar ki
ya mamaye min kokon zuciyata.Ya
masoyiyata ki zamo mai in zamo albasa mu
hadu mu
soye juna.'.ya masoyiyata, ki zama candir in
zamo ashana, ki zamo itace in zamo
makamashi mu hadu mu hura wutar so,
domin mu mutafasa tukunyar kauna Kixama
aruma naxama Sadauki mu hadu mu yaki
duk wani makiyin soyayyan mu daga naku
baban soyayya namalika
No comments:
Post a Comment