Kungiyoyin addini zasu fara biyan gwamnati harajin sayar da Qur’ani da Injila - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, May 16, 2018

Kungiyoyin addini zasu fara biyan gwamnati harajin sayar da Qur’ani da Injila

Kasar Uganda ta kakabawa kungiyoyin
addini biyan harajin sayar sayar da
Qur’ani, Injila (Bible) da ragowar wasu
litattafan addu’o’I na addini.

Hukumar tattara haraji ta kasar Uganda
(URA) ta tilastawa kungiyoyin addinai a
kasar biyan haraji a kan sayar da
litattafan addini da na addu’o’i.

Saidai kungiyoyin addinai da malamai
sun nuna rashin jin dadin su da juyayi
a kan wannan sabuwar doka tare da
bayyana cewar bai kamata a saka haraji
a kan litattafan addini ba saboda suna
amfani das u ne domin tsarkake
zukatan mutanen kasar.

Kwamishinan URA, Uwargida Doris
Akol, t ace tun farko an yi kuskuren
rashin saka masu sayar da litattafan
addinai cikin masu biyan haraji.
Qur’ani da Injila
Yayin mayar da martini a kan wata
takardar koke da limamin wata Cocin
Uganda, Archbishop Stanley Ntagali, ya
aike mata, Doris ta bayyana cewar
gwamnati ba zata cigaba da barin
kungiyoyin addinai na shigo da
littatafai kasar ba tare da biya masu
kudin haraji ba.

Archbishop Ntagali, ya yi korafin cewar
gwamnatin kasar Uganda ta rike wasu
litattafan addini 9,120 da ya shigo das u
daga kasar Kenya, saboda bai biya
masu haraji ba.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad