Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasashen ketare jinya? - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Tuesday, May 8, 2018

Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasashen ketare jinya?

Shugabannin kasashen Najeriya da Angola da
Zimbabwe da Benin, da Algeria na da
abubuwan da suke kamanceceniya,

wato rashin
yarda da tsarin kiwon lafiyar kasashensu.

Ta fuskar lokutan da suka shafe suna jinya a
kasar waje, Shugaban kasar Najeriya
Muhammadu Buhari mai shekara 74, shi ne
na farko a cikinsu, amma a shekarun da suka
gabata dukkan wadannan shugabannin sun
ketara wasu kasashen don duba lafiyarsu.

A lokuta da dama suna tafiya su bar asibitoci
ba isasshen kudin da za a samar da
magunguna, wanda akasarin 'yan kasar suka
dogara da shi.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta Majalisar Dinkin
Duniya ta ce, a shekarar 2010, matsakaicin
kudin da ake kashe wa lafiyar dan Afirka daya
shi ne dala 135, idan aka kwatanta da dala
3,150 na kasashen da suka fi samun kudin
shiga.

A cewar wata kungiya mai sa ido a harkar
lafiya, misali a kasar Zimbabwe, an sha
samun yankewar magungunan da ake
tsananin bukatarsu irinsu na kashe radadin
ciwo da kuma masu yaki da kwayoyin cuta a
asibitocin gwamnati .

Kamar Najeriya, tsarin kula da asibitocin
gwamnati ya yi muni," saboda rashin
wadataccen kudi, in ji editan BBC na Abuja.

Tsarin inshorar lafiya na ma'aikatan gwamnti
da kuma sauran ma'aikata masu zaman
kansu, ya bai wa wasu mutane samun damar
magani na asibitoci masu zaman kansu,
amma mutane da yawa sun dogara ne da
wanda gwamnati take samarwa.
A dukkan wadancan kasashen, wadanda suke
da kudi ne suke samun cikakkkiyar kulawa a
asibitoci masu zaman kansu, amma a wasu
lokutan ana ganin cewa an fi samun hakan a
kasashen ketare.

Shugaban Najeriya ya shafe sama da uku
hudu a Londan yana jinyar cutar da ba a
bayyanata ba, wacce ta haddasa ce-ce ku-ce a
kasar.

Ba kamar irin ta takwaransa Umaru Musa
Yar'Adua ba, wanda ya tafi kasar Saudiyya
don ganawa da likita, shugaba Buhari ya bar
wa mataimakinsa ragamar mulkin kasar,
amma hakan bai hana mutane yin suka ba.

19 ga watan Janairu - Ya tafi Birtaniya domin
"hutun jinya"
5 ga watan Fabrairu - ya nemi Majalisar
Dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman
bai fara aiki nan-da-nan ba
7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin
jinya
6 ga watan Yuli- Aisha Buhari ta ce, "yana
samun sauki sosai"
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe,
wanda yake mulki tun shekarar 1980, shi ma
ya sha suka daga abokan hamayyar siyasa,
na jan ragamar kasar "daga gadon asibiti",
bayan tafiyar da ya yi Singapore domin duba
lafiyarsa karo na uku a wannan shekarar.

A watan Mayu ne gwamnatin Angola ta
bayyana cewa, Jose Eduardo dos Santos,
wanda yake shi ne shugaban kasar na tsawon
shekara 38 da ta gabata, ya je Spaniya don
duba lafiyarsa.

Amma a bangaren Najeriya, gwamnati ba ta
bayyana wani abu game da halin lafiyar
shugaban ba.

Batun rashin lafiyar shugaban Algeria
Abdelaziz Bouteflika, mai shekara 80,
sanannen al'amari ne tun tsawon lokaci.
Kamfanin dillanci labarai na AFP ya bayar da
rahoton cewa, a shekarar 2013 ne ya sha
fama da ciwon zuciya, inda ya yi amfani da
keken guragu wajen zuwa kada kuri'a, daga
baya kuma ya tafi jinya a sibitin Faransa.

A watan Nuwambar da ya gabata ne ya koma
gida, a matsayin daya daga cikin abin da
gwamnati ta kira "Takaitaccen duba lafiya"
Amma abin tambaya a nan shi ne, me yake
jan hankalinsu zuwa wata kasar jinya?
Ba mu yi mamaki ba, babu wani kakakin
shugaban kasa da ya fito ya ce suna hakan
ne saboda an fi samun cikakkkiyar kulawa a
kasashen ketare.

Ko da yake, mai magana da yawun Mista
Mugabe, ya yi martani game da tafiyar da
shugaban ya sha yi zuwa Singapore, inda a
watan Mayu ya tsaya kai da fata cewa, hakan
ba ya nufin ya juya wa tsarin lafiya na
Zimbabwe baya ne.

Jaridar kasar ta rawaito inda George
Charamba yake cewa, "Ba likitocin Zimbabwe
ba ne kawai suke duba shugaban, a zahiri
baki ne, baki sosai."

Batun dai kawai shi ne, a wata kasar ne
kawai za a iya duba matsalar idon da Mista
Mugabe ke fama da ita, "wacce take bukatar
wadanda suke da kwarewa a fannin lafiya".

Mai magana da yawunsa ya ce, saboda
wannan matsalar ce tasa, wani lokaci Mista
Mugabe yake lumshe idonsa a lokacin da ke
gabatar da taro, sai a ga kamar yana bacci.

Wani babban likita a Najeriya Osahon
Enabulele, ya ce, batun wadannan tafiye-tafiye
ba kawai suna nuna gazawar likitoci na gida
ba ne, suna ma yin zagon kasa ga bangaren
lafiya na kasar.

Ya kira wannan halayya da 'yin tafiye-tafiye
don neman lafiya, ya kuma ce hakan da
shugabanni ke yi yana jawowa kasar asarar
miliyoyin daloli.

A shekarar 2013, ya kiyasta cewa 'yan
Najeriya suna kashe dala biliyan daya a
kasashen waje don neman lafiya, inda ya ce a
yanzu kam wannan adadi zai iya nunka haka.

Idan aka kwatanta, kasafin kudin da
gwamnatin tarayya ta yi na shekarar 2016 an
ware wa bangaren lafiya dala miliyan 800.

Dr Enabulele, wanda mataimakin shugaban
kungiyar likitocin kasashe rainon Ingila ne, ya
ce kudin da 'yan Najeriya ke fitarwa zuwa
wasu kasashe don neman lafiya zai isa a
bunkasa tsarin lafiya a kasar.
Ya ce a game da hakan, manyan likitocin
Najeriya na ketarawa kasashe don samun
cikakkkiyar kulawa, abun kuma na kara
tabarbarewa.
Dokta Enabulele ya kara da cewa, yana fata
shugaban Najeriyar ya samu lafiya, yana
ganin zai iya samun dukkan kulawar da yake
bukata a kasar.

Babban abin da ya kamata a lura shi ne,
rashin wadataccen kudi a bangaren lafiya shi
ne matsalar.

Har wa yau, shugabanni ba lallai ne su mayar
da hankali wajen bunkasa asibibitoci ba, idan
dai har za su rinka tafiya wasu kasashe jinya.
Wata kila za su iya daukar darasi daga wurin
shugaban Sudan Omar al-Bashir.
A watan Janairu ne, ya yi wani abu da
kamfanin dillanci labarai ya bayyana a
matsayin "Ciwon zuciya," a wani asibitin da
ke babban birnin kasar, Khartoum.
Duk da cewa asibitin na kudi ne ba na
gwamnati ba.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad