Maryam Gidado tana daya daga cikin manyan
jarumai mata a masana’antar fina-finan
Hausa. Aminiya ta tattauna da ita kan harkar,
inda jarumar ta tabo batutuwan da suka shafi
harkar fim da kuma rayuwarta.
Ga yadda hirar ta kasance:
A Gabatarwa, wace ce Maryam Gidado?
Kamar yadda aka sani, sunana Maryam Jibril
Gidado, wacce aka fi sani da ‘Maryam Babban
Yaro.’
Na samu wannan suna ne tun daga lokacin
da muka yi fim da Adam A. Zango mai suna
‘Babban Yaro.’ An haife ni a watan Disamba a
1988 a garin Jos.
Na fara makaranta a
Hassan Memorial, sai aka mayar da ni
firamare ta LGA Gangare, sannan na yi
makarantar Arabiyya ta Sakandire a Bauchi
Road, duka a Jos.
Sannan na je na yi Diploma a bangaren
kwamfuta a wata makaranta daban. Daga nan
na koma Bauchi na nemi in yi HND, amma
ban samu ba sai na yi diploma a bangaren
kididdiga.
Sai kuma na ci gaba har na yi HND
a nan, sai na dawo Jos na yi digirina a
Jami’ar Jos.
Ko Maryam ta taba yin aure?
To yanzu idan na ce ma ban taba yin aure ba
sai a yi mini dariya a matsayina na
Bafulatana, kasancewar kowa dai ya san
ka’idar Fulanin daji yi wa ’ya’yansu aure da
wuri. Bayan na gama jarrabawar WAEC da
NECO aka yi mini aure.
Ina shekara sha hudu na haifi ’yata ta farko,
bayan shekara daya da auren ke nan. Don
haka shekara goma sha hudu na ba ’yata ta
fari. Yanzu ka ga ta shiga shekara sha daya
ke nan.
To yaya aka yi kika samu kanki a harkar fim?
Ni dai gaskiya da ina kallon fim ne kawai,
amma ina tunanin shirme ne kawai, domin
idan na ga ’yan fim har zaginsu nake yi don
ban taba tunanin zan yi fim ba.
Daga baya sai na ga yadda abin yake
fadakarwa. Na ga wasu ma sun Musulunta ta
hanyar fim. Sai na ga abin wa’azi ne.
To, a baya kin fada mana yadda aka yi miki
aure har kika haihu. Sai dai ba ki fada mana
ko kun rabu da mijin ko mutuwa ya yi ko
kuma da aurenki kike yin fim ba?
To, a gaskiya ba zan iya fada ba.
Saboda a
duniya babu abin da ya kai sirri dadi. Idan ka
rufa wa wani asiri Allah Zai rufa naka. Kuma
tsakanin mata da miji sai Allah. Don haka
wannan mutane su yi hakuri.
Shin wannan dan naki na biyu babansu daya
da ’yarki ta farko?
Ba daya ba ne.
Bayan mun rabu da mijina na
yi wani sabon aure. Lokacin da na auri
mahaifin dana ma har na fara harkar fim. Ina
da cikinsa ya gudu ya bar ni har na haife shi
yanzu shekarun dana na biyu bakwai ke nan.
Abin nufi a nan shi ne, kun rabu da shi ne ko
rasuwa ya yi?
To, in dai wannan ne ba rasuwa ya yi ba, yana
nan da ransa, sannan ina da cikin dana na
biyu wata daya ya tafi ya bar ni, har zuwa
yanzu mahaifinsa bai zo wajen da yake ba.
Sai dai ya turo a dauki hotonsa, kuma zai iya
kira ta waya su yi magana, amma dai yana
nan a Kaduna kawai dai tafiyar da ya yi ya
bar ni don wani dalili ne na daban.
To daga nan sai me ya biyo baya?
Kai dai a bar maganar haka, don sirri yana da
dadi.
Ki fada mana yadda aka yi kika samu kanki a
harkar fim da kuma shekarar da kika fara?
A gaskiya na manta shekarar da na shigo,
amma dai na fara ne da albam din Mahmud
Nagudu mai wakar ‘Garin So Nisa’ amma fim
din da aka fara yi mini shi ne wani fim mai
suna ‘Ragowar Yaki,’ lokacin da muke yi a Jos
da ni da Ali Nuhu.
Shi ne fim dina na farko da na fara yi a
duniya, kuma da ma tun da na fara fim ban
fara da mai tallafa wa jaruma ba, da jaruma
na fara. Kodayake da farko mutane sun dauka
albam nake yi ba fim ba, saboda shi ne na
fara. Sai daga baya na zo na shiga fim din su
Alma, inda na yi ‘Ragaya’ da ‘bingyal da
‘Mukaddari’ da sauransu.
Ko za ki iya bayyana yawan fina-finan da kika
yi?
Gaskiya ba zan iya fadar adadinsu ba. Don ka
ga a wata zan iya yin fim biyu ko uku, to yaya
zan iya sanin fim din da na yi a tsawon
lokacin da na yi a harkar fim? Sai dai zan iya
fadar wasu kadan daga cikinsu, musamman
wadanda ba su dade ba kamar ‘Babban Yaro’
da ‘Wata Hudu’ da ‘Munafikin Mata’ da
‘Al’ajabi’ da ‘Zawarawa’ da ‘Fulani’ da ‘Sultan’
da ‘Basaja.’ Ina ji da su a cikin fina-finaina.
Akwai lokacin da kika yi wani tashe sai kuma
aka daina ganin ki a harkar fim. Hakan ya sa
ake cewa ko kin yi aure ne, ko kuma harkar
kika bari…?
To gaskiya ba aure na yi ba, kuma ba barin
harkar na yi ba, ina yi kadan-kadan ne, sai dai
mutane ba za su gane ba, saboda ba sa gani
na sosai, amma dai kafin na fara sai da na
fada wa mahaifina, sai ya ce shi ma ga dokar
da zai kafa mini, ya ce makaranta yake so in
yi, kuma ya matsa sai da na yi, to da na ga
na samu wannan sunan na daukaka, sai na
koma makaranta. Hakan ya sa ake ganin
kamar na bari ne, amma dai ina yin fim lokaci
zuwa lokaci. Amma dai yanzu na gama na
dawo.
A baya an fi ganin ki tare da Adam A. Zango,
amma yanzu ba a ganin ku tare, me ya jawo
hakan?
To ai da ma ba a kamfanin Adamu nake ba,
kuma kamfanin Adamu fina-finan da suka yi
mini ba su da yawa. Sai dai su ne suka yi
mini fim din da ya fara daga ni. Don bayan
albam din Mahmud Nagudu babu wani fim da
ya daga ni sai na su Adamu. A gane furodusa
ne yake hada ’yan wasa. Don haka idan suka
ga dama su hada ni da Ali, in suka ga dama
su hada ni da Adamu, ko Sani Danja da
sauransu.
Yanzu a matsayinki na babbar jaruma, burinki
ya cika a harkar fim?
Gaskiya burina ya cika sai godiya ga Allah.
Yanzu burina daya ne kawai Allah Ya ba ni
miji nagari.
Ku ’yan fim kullum ku ne fadar miji nagari
kuke nema, amma ana yi muku kallon masu
ruwan ido, ko me za ki ce kan hakan?
To, ai mu ba ruwan ido muke yi ba, muna
tunanin maza suna ganin mu a fim ne, suna
son su aure mu don wata manufa da suke da
ita. Shi ya sa muke tsoron auren, ba wai muna
tunanin wane mai kudi ba ne, ko marar kudi
ba. Don idan ka auri mai kudi ma zai zaci don
kudinsa ka aure shi. Gara ka auri talaka idan
kudin ya zo kuna tare da shi. To yanzu abin
ne sai ya zama muna tsoron mazan, su ma
suna tsoron mu.
Ba kya ganin ana cewa idan kun yi auren ma
ba kwa zama?
To ai wannan maganar da na yi ita ce ta ba
da amsar wannan tambayarka. Nan za a gane
Allah ne Ya san dalilin rabuwa tsakanin mata
da miji, babu mamaki wancan dalilin zai sa a
zo a yi auren wani bai yi tunanin wannan ba
sai haka ta kasance.
Bayan harkar fim, ko akwai wata harka ta
kasuwanci da kike yi?
E, ina yin kasuwanci. Don yanzu ina da wajen
gyaran gashi a gidanmu. Sannan a
makarantarmu ina yin aiki na wucin gadi,
kuma ina saro kayan mata ina sayarwa.
Akwai wani lokaci da kika shirya na barin
harkar fim?
Gaskiya ban shirya ba, sai lokacin da Allah Ya
kawo mini miji to lokacin zan bar harkar fim.
Me kike alfahari da shi a game da harkar fim?
To abin da nake alfahari da shi na san ko ban
yi komai ba akwai wadanda suka karu da ni a
kan wani fim da na yi na gyara tarbiyya,
sannan na san mutane masu yawa. Hakan
abin alfahari ne, wanda ba kowa Allah Yake yi
wa haka ba.
Sannan na samu abubuwa wadanda suke
hakkokina ne nake ci ba na wasu ba. Sannan
da fim na je Makka, na yi gida, na mallaki
kadarori, na yi karatu, don haka dole na yi
alfahari da harkar fim.
Daga: Aminiya
No comments:
Post a Comment