HANYOYIN 4 NA YADDA ZA’A MAGANCE WARIN BAKI A SAU’KAKE - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Sunday, May 27, 2018

HANYOYIN 4 NA YADDA ZA’A MAGANCE WARIN BAKI A SAU’KAKE

Kiwon Lafiya: Hanyoyi 4 na
kauracewa warin baki
Warin baki cuta da ka iya kama kowa, sai
dai ance babu wata cuta da ba a iya
magance ta,da yawa daga cikin mutane
masu fama da warin baki, shiga cikin abokai
ko ‘yan uwa yana yi musu wahala, sanadiyar
janyo musu barazanar jin kunya ko kuma su
na magana ana toshe hanci.
Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa
warin baki abu da duka wanda ke dauke da
shi, to ko shakka babu shi ya gadarwa
kansa wannan wari na baki, sanadiyar rashin
tsaftace baki ko kuma rashin kula wajen
ciyaye na abinci da ka iya janyo cutar.
Akwai nau’ukan abinci wanda da zarar
mutum ya yi amfani dasu suke sauya launin
baki, baya ga haka akwai lokuta da ba su
dace a ci wasu nau’ukan abincin ba, kamar
irin su shan abin mai zaki kafin kwanciyar
bacci.
Ga jerin tafarki hudu da ka iya taimakawa
wajen kawar da warin baki dake addabar
mutane da dama, ta yadda ba su iya shiga
mutane.

1. Yin amfani da lemun bawo musamman
ma lemun tsami, domin su na tattare da
sunadarai dake hana kwayoyin cututtuka na
cin baki dake janyo warin na baki.
Bincike ya nuna cewa, zuba bari guda na
lemun tsami a cikin kofi daya na ruwa,
sannan a dan gauraya da gishiri wanda bai
wuci rabin cokalin shan shayi ba, kuma a
kurkura a baki kafin kwanciyar bacci, yana
hana warin baki.

2. Garin Khal na itacen tufa Gauraya cokali
daya na garin khal na itacen tare da kofi
daya na ruwa kuma a kwankwade yana hana
warin baki.

3. Garin hodar gashin burodi: Bayan fitar da
hakora da kara musa haske tar-tar, idan aka
kwaba garin hodar gashin burodi da ruwan
dumi aka kurkura a baki koda sau biyu a
rana, tabbas mutum zai yi sallama da warin
baki

4. Ruwan shayi zalla babu madara ko kuma
shayi na koren ganye na daukewa masu sha
warin baki.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad