Dalibai sun ragargaji malaman su saboda sun hana su satar amsa yayin jarrabawar WAEC - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, May 9, 2018

Dalibai sun ragargaji malaman su saboda sun hana su satar amsa yayin jarrabawar WAEC

Daliban aji na karshe na makarantar
sakandire na Zabzugu Senior High School
da ke yankin Zabzugu na kasar Ghana
sun dauki miyagun makamai da duwatsu
kuma suka kaiwa malaman makarantar
farmaki saboda sun ki barin su suyi satar
amsa a jarabawar WAEC.
Kamar yadda Adomonline ya ruwaito,
fusatattun daliban sun baranat kayayakin
makaranta da dama wanda suka hada da
kofofi, tagogi, talabijin da sauransu.
Daliban sunyi ikirarin cewa an tauye
musu hakkin su na shiga dakin jarabawa
da takardunsu don suyi satar amsa.
Dalibai sun fara ta'adda ga malamai in suka
hana su satar amsa
Wani dalibi da ya nemi a sakaya sunansa
ya ce, duk da cewa ba su yi wata
yarjejeniya da malaman makarantan na
barin su suyi satar amsa ba, suna da
masaniya cewa malaman wasu
makarantun suna barin daliban su suyi
satar amsar.

Wani malamin makarantar da ya tabbatar
da afkuwar lamarin yace laifin su kawai
shine kin amincewa daliban suyi satar
amsa a jarabawar na WAEC. Ya kara da
cewa ya tsira da ransa ne saboda bai tsaya
a gidansa ba domin daliban su tafi gidansa
da duwatsu sunyi kacha-kacha da gidan.
Ya ce, "Daliban suna ikirarin cewa suna da
damar shiga dakin jarabawa da litafan
karatunsu don suyi satar amsa amma ni ban
san wata dokar jarabawa da ta amince da
hakan ba. Saboda kin amincewar da mukayi,
daliban su shiga makaranta dauke da
makamai inda suka rika barna kuma sukayi
ikirarin kashe duk wanda suka samu."
Malaman makarantan sun dauki alwashin
ba zasu sake komawa makarantar ba har
sai gwamnati ta samar da ingantaccen
tsaro.
Shugaban yankin na Zabzugu, Honarabul
Iddi Ahmed ya yi kira ga hukumomin tsaro
su tabbatar cewa sun warware rikicin da
ke faruwa tsakanin daliban da malaman
su.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad